|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2006-03-01 09:41:03
|
|
Kasar Gabon da Equatorial Guinea sun tsaida kudurin warware rikici kan yankunan kasashe ta hanyar yin shawarwari
cri
Wakilinmu ya ruwaito mana labari cewa, ran 27 ga wata a birnin Geneva na kasar Switzerland, Mr. Omar Bongo, shugaban kasar Gabon, da takwaransa na kasar Equatorial Guinea, wato Mr. Teodoro Obiang Nguema sun yi tattaunawa, sabo da Mr. Kofi Annan, babban sakataren M.D.D. ya ba da shawara kan wannan da kuma shiga ayyukan. Bayan da aka yi tattaunawar, an bayar da hadaddiyar sanarwar cewa, shugabannin kasashen nan biyu sun tsaida kudurin warware rikicin yankunan kasa ta hanyar yin shawarwari.
Sanarwar ta ce, shugabanin nan biyu sun tsaida kudurin fara yin shawarwari nan da nan a tsakanin kasashen nan biyu, domin shata iyakarsu ta kasa da ta teku har abada, da kuma warware matsalar samu tsibirori 3 da bangarorin biyu suke gardama a kai. Shugaban kasashen nan biyu sun sake nanata cewa, suna goyon baya ga kokarin yin sulhuntawa da Mr. Kofi Annan ya yi tun daga shekarar 2003. Bayan haka kuma sun tsaida kuduri cewa, ran 15 ga wata a Geneva, kwararrun da abin ya shafa na kasashen nan biyu za su yi taro, domin tsara takardar lokacin yin shawarwari. Kuma ta hanyar yin tattaunawa ne a lokacin da ke dacewa, shugabannin kasashen nan biyu za su yarda da sakamakon da wadannan kwararru za su samu ta hanyar yin shawarwari, na neman warware rikicin da ke tsakanin bangarorin biyu kafin karshen shekarar da muke ciki.
Mr. Annan, babban sakataren M.D.D. ya halarci wannan tattaunawa. A taron maneman labaru da Mr. Annan, da shugabanni biyu suka shirya tare bayan da aka kammala tattaunawar, Mr. Annan ya bayyana cewa, kudurin da shugaba Bongo da shugaba Ngurma suka tsaida ba kamar aka cewar wai habaka shiyyoyin da ke gardama a kai tare ba, har ma ya kasance na warware matsalar da ke kasancewa a tsakanin kasashen nan biyu har abada ta hanyar shata iyakarsu. Mr. Annan yana ganin cewa, shugabannin kasashen biyu suna da "gaskiya da niyya", kuma suna "yin tsare-tsaren kuduri kan zaman lafiya." Bayan haka kuma, ya fayacce cewa, shugabannin kasashen nan biyu za su kara yin tattaunawa a watan Maris a Afrika, shi da kansa kuma zai halarci wannan taron.
Mr. Nguema, shugaban kasar Equatorial Guinea yana jin fari ciki sosai kan ayyukan yin sulhuntawa da babban sakataren M.D.D. ya yi. Ya nuna cewa, shawarwari na matsayin kwararru da za a yi a tsakanin kasashen nan biyu a cikin 'dan lokaci masu zuwa, zai nuna fatan siyasa sosai na shugabannin kasashen nan biyu. Shugaba Bongo ya gaya wa kafofin watsa labaru cewa, shi da shugaba Nguema sun yi tattaunawa cikin lafiya, kuma ya yi niyyar samun sakamako wajen shirin warware rikicin da ke tsakanin kasashen biyu a karshe.
Tun daga farkon shekarar 1970, kasar Equatorial Guinea, da Gabon suka fara yin rikici kan yankunan kasa, da sararin sama. A cikin 'yan shekarun da suka wuce, tare da ganowar albarkatun man fetur da gas a tekun kusa da kasar Equatorial Guinea, matsalar tabbatar da iyakar sararin teku da ke tsakanin kasar Equatorial Guinea, da kasashe masu makwabtaka da ita guda hudu, wato su kasar Gabon, da Nijeria, da Cameron, da Sao Tome and Principe ta kara yin tsanani a kwana a tashi. Rikicin da ke tsakanin kasar Equatorial Guinea, da Gabon ya shafe matsalar samun tsibirori 3 da ke mashigin teku ta Corisco wadda ke da kyakkyawan sakamkon habaka man fetur da gas. A watan Nuvamba na shekarar 1985, kasar Equatorial Guinea, da Gabon sun yi musayen ra'ayoyinsu kan ayyukan shata iyakar kasa, da na hadin kai na bangarorin nan biyu. A watan Yuli na shekarar 1994, kasashen nan biyu sun daddale yarjejeniya dangane da habaka albarkatun da ke mashigin tekun Corisco tare, kuma sun taba amincewa da cewa, za su shirya shawarwarin aiki domin daddale yarjejeniya ta karshe. Amma, ba a sami ci gaba ba kan wannan. A watan Mayu na shekarar 2002, shugaban kasar Guinea ya kai ziyarar aiki kan kasar Gabon. Amma, shawarwarorin da aka fara daga lokacin sau da yawa dangane da matsalar iyakar kasa ba su iya warware rikicin da ke tsakanin kasashen nan biyu ba. A watan Feburairu na shekarar 2003, ministan tsaron kasar Gabon ya yi rangadin aiki ga wani tsibirin da kasashen nan biyu suke gardama a kai, wannan ya gamu da kiyewa daga bangaren Equatorial Guinea. Daga baya Mr. Annan, babban sakataren M.D.D. ya shiga sasanta rikici kan yankunan kasa da ke tsakanin kasar Equatorial Guinea, da Gabon, bisa matsayinsa na mai sulhuntawa, amma shawarwarin da kasashen biyu suka yi a cikin shekaru 3 da suka wuce ba su sami babban ci gaba ba. (Bilkisu)
|
|
|