A ran 28 ga wata, Hu Jintao, shugaban kasar Sin kuma shugaban kwamitin tsakiya na soja na kasar Sin ya jaddada a nan birnin Beijing cewa, babban yankin mahaifa na kasar Sin zai ci gaba da yin namijin kokari domin neman dinkuwar duk kasar Sin cikin lumana, amma tabbas ne ba zai yarda da a kebe yankin Taiwan daga mahaifa ta kasar Sin ba.
Hu Jintao ya fadi haka ne lokacin da yake ganawa da Samuel Schmid, ministan tsaron kasar Switzerland wanda yake yin ziyara a nan kasar Sin. A kan maganar Taiwan, Mr. Hu ya kara da cewa, hukumar Taiwan ba ta mai da hankali kan ra'ayoyin adawa da mutanen tsibirin Taiwan da wadanda ba na tsibirin ba suka yi, ta tsaya tsayin daka kan matsayinta ta tsai da kudurin daina aikin "kwamitin dinkuwar duk kasa gaba daya" da "ka'idojin dinkuwar duk kasa gaba daya". Wannan tsokana ne mai tsanani da hukumar Taiwan ta yi wa ka'idar Sin daya tak da yawancin kasashen duniya suke bi da halin zaman lafiya da na karko da ake ciki a yankin mashigin tekun Taiwan. Wannan kuma mataki ne mai hadari da ta dauka a kan hanyar yunkurin neman 'yancin kan Taiwan. Duk mutumin da ya saba wa ka'idar tarihi ba zai gudu daga makomar cin tura ba.
Sannan kuma, Mr. Schmid ya bayyana cewa, gwamnatin Switzerland za ta ci gaba da bin manufar Sin daya tak kamar yadda ta saba yi. Ya kuma yaba wa kokarin da gwamnatin kasar Sin ta yi wajen tabbatar da zaman lafiya da na karko a yankin mashigin tekun Taiwan da cudanyar da aka yi a tsakanin gabobin biyu na mashigin tekun Taiwan. (Sanusi Chen)
|