Bisa labarin da wakilanmu suka aiko mana, an ce, a cikin 'yan kwanakin nan, Sinawan da suke da zama a kasashen Amurka da Canada da Ingila da Jamus da Rasha da Japan da sauran kasashen duniya bi da bi ne suka yi tofin Allah tsine kan kudurin daina aikin "kwamitin dinkuwar duk kasa gaba daya" da kuma "Ka'idojin dinkuwar duk kasa gaba daya" da Chen Shui-bian, jagoran hukumar Taiwan ta kasar Sin ya tsaida. Sinawa a ketare suna ganin cewa, matakin da Chen Shui-bian ya dauka ya saba wa ka'idar tarihi ta neman bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan, kuma ya bata halin zaman karko da ake ciki a yankunan Asiya da ke bakin tekun Pacific.
Kungiyar Washington ta kasar Amurka ta sa kaimi kan neman dinkuwar duk kasar Sin cikin lumana ta bayar da wata sanarwa, inda ta ce, a wannan lokaci, kamar yadda ya saba yi, Chen Shui-bian ya dauki matakan cin amanar jama'ar Taiwan da kafofin kasashen duniya. Sannan kuma, sauran kungiyoyin Sinawa da ke da zama a sauran wuraren kasar Amurka bi da bi ne suka nuna cewa, kudurin daina aikin "kwamitin dinkuwar kasa gaba daya" da Chen Shui-bian ya tsaida wani mataki ne mai hadari da ya dauka a kan hanyar neman 'yanci kan Taiwan. Wannan kudurin da hukumar Taiwan ta dauka ya gurgunta moriyar jama'ar Taiwan da ta al'ummar Sinawa sosai. (Sanusi Chen)
|