A ran 28 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Liu Jianchao, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya bayyana cewa, bangaren kasar Sin yana fatan bangaren Amurka zai dauki hakikanan matakai domin kiyaye yunkurin neman 'yancin kan Taiwan da ake yi, kuma zai hada da bangaren kasar Sin domin tabbatar da dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da halin zaman lafiya da na karko a yankin mashigin tekun Taiwan da ake ciki.
A ran 27 ga wata, bayan da Chen Shui-bian, jagoran hukumar Taiwan ta kasar Sin ya yi shelar daina aikin "kwamitin dinkuwar duk kasa gaba daya" da "ka'idojin dinkuwar duk kasa gaba daya", a gun wani taron manema labaru da aka yi, Mr. Adam Ereli, kakakin majalisar gudanarwa ta kasar Amurka ya jaddada cewa, kasar Amurka ta ki kowane gefe ya sauya halin da ake ciki yanzu a yankin mashigin tekun Taiwan da kansa kawai, kuma ba ta goyi bayan yunkurin neman yancin kan Taiwan ba.
Sabo da haka, Mr. Liu ya yi sharhi cewa, bangaren kasar Sin ya riga ya mai da hankali kan matsayin bin manufar Sin daya tak da kiyaye yunkurin neman 'yancin kan Taiwan da kasar Amurka take bi. A sa'i daya kuma, bangaren kasar Sin ya nemi bangaren Amurka da ya san tsanani da bala'in da ayyukan neman 'yanci kan Taiwan da Chen Shui-bian ke yi za su yi. Dole ne bangaren Amurka ya cika alkawarinsa kan maganar Taiwan da ya yi wa bangaren kasar Sin, kuma ya dauki hakikanan matakai domin kiyaye ayyukan neman 'yancin kan Taiwan. Kada ya ba wa rukunin neman 'yancin kan Taiwan kowace alamar kuskure. (Sanusi Chen)
|