 Bisa labarin da wakilanmu suka aiko mana, an ce, a cikin 'yan kwanakin nan, Sinawan da suke da zama a kasashen Amurka da Ingila da Rasha bi da bi ne suka yi tofin Allah tsine kan kudurin daina aikin "kwamitin dinkuwar duk kasa gaba daya" da kuma "Ka'idojin dinkuwar duk kasa gaba daya" da Chen Shui-bian, jagoran hukumar Taiwan ta kasar Sin ya tsaida. Sinawa a ketare sun yi wa kusoshin hukumar Taiwan kashedin cewa, kada su bata halin neman bunkasuwa cikin lumana a tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan da ake ciki yanzu.
A ran 27 ga wata, Mr. Bao Shiguo, sanannen shugaban Sinawan da ke da zama a Washington na kasar Amurka ya nuna cewa, babu wani dalilin da ya sa Chen Shui-bian ya dauki wannan mataki, sai dai kawai don yana wasan siyasa, kuma ba zai samu nasara ba. Sannan kuma, sauran Sinawan da ke da zama a kasar Amurka suna fatan hukumar Taiwan da ke karkashin jagorancin Chen Shui-bian za ta mai da hankali kan babbar moriya, kada ta jefa jama'ar gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan cikin bala'in yaki domin cimma moriyar radin kanta kawai.
Mr. He Zuo-jun, shugaban sada zumunta a tsakanin 'yan asalin birnin Shun De na kasar Sin wadanda suke da zama a kasar Ingila ya gaya wa wakiliyarmu cewa, matakin da Chen Shui-bian ya dauka ya saba wa ka'idar tarihi. Dalilin da ya sa ya tsai da wannan kuduri shi ne ya yi kacici-kacici domin cimma moriyar radin kansa kawai. (Sanusi Chen)
|