Bisa labarin da wakilinmu ya aiko mana, an ce. a ran 28 ga wata, ofishin kula da harkokin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwa ta kasar Sin sun bayar da wata sanarwa kan matakan daina aikin "kwamitin dinkuwar duk kasa gaba daya" da kuma "Ka'idojin dinkuwar duk kasa gaba daya" da Chen Shui-bian, jagoran hukumar Taiwan ya dauka a ran 27 ga wata. A cikin sanarwar, bangaren babban yankin kasar Sin ya zargi Chen Shui-bian da cewa, yana yin amfani da wannan dama domin kara saurin neman 'yanci kan Taiwan da kuma tsananta dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan.
Sannan kuma, sanarwar ta ce, Chen Shui-bian yana tsayawa tsayin daka kan manufar neman 'yanci kan Taiwan, wannan zai jefa zaman al'ummar Taiwan cikin bala'i, kuma zai kara bata zaman lafiya da na karkon yankin da ke bakin mashigin tekun Taiwan da yankunan Asiya da ke bakin tekun Pacific. Sabo da haka, tabbas ne bangaren babban yankin kasar Sin ya kiyaye da hana a dauki irin wadannan matakai.
Haka nan kuma, sanarwar ta jaddada cewa, bangaren babban yankin kasar Sin zai ci gaba da yin namijin kokarinsa cikin sahihanci kwarai domin neman dinkuwar duk kasar Sin gaba daya cikin lumana. Amma a sa'i daya kuma, ko shakka babu bangaren babban yankin kasar Sin ba zai yarda da rukunin neman 'yanci kan Taiwan su ware yankin Taiwan daga kasar Sin a kowane dalili da kowace hanya ba. (Sanusi Chen)
|