Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-27 16:44:34    
Ma Yun, wani mahaukaci ne da ke tafiyar da shafin Internet na Alibaba

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu karatu, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na Bunkasuwar kasar Sin. Bayan da sana'ar shafin Internet ta bullo a nan kasar Sin wajen yau da shekaru 10 da suka wuce, a cikin gajeren lokaci ne wannan sana'a ta samu bunkasuwa cikin sauri. Ba zato ba tsammani, wasu mutane sun yi suna kwarai domin sun ci nasarar aiwatar da shafin Internet. A cikin shirinmu da muka gabatar a da, mun taba bayyana muku bayanin Mr. Li Yanhong, wato jami'in farko na shafin bincike Internet na kamfanin Baidu. A cikin shirinmu na yau, za mu kara bayyana muku wani mutum daban Mr. Ma Yun wanda ya fi shahara sosai a nan kasar Sin kuma ake kiransa mahaukaci da ke tafiyar da shafin Internet. Yanzu a cikin hannun Ma Yun, akwai wani sanannen shafin Internet na yin ciniki da aka fi sanin da suna Alibaba kuma ya fi girma a duk fadin duniya. Yau da shekaru 9 da suka wuce, ba a san ko wane ne Ma Yun ba kwata kwata. Amma yanzu ya yi suna kwarai domin ya sayi sashen kasar Sin na shafin Internet na Yahoo.com.

Yau da shekaru 9 da suka wuce, lokacin da Ma Yun ya sayar da shafin Internet nasa, domin yawancin Sinawa ba su san shafin Internet ba, wasu mutane sun dauka cewa shi wani mazambaci ne. Amma bayan shekaru 9 da suka wuce, a watan Agusta na shekara ta 2005, a gun wani taron manema labaru da aka yi a nan birnin Beijing, Mr. Ma Yun ya shelanta cewa kamfaninsa na na Alibaba da ke karkashin jagorancinsa ya ci nasarar sayen dukkkan dukiyoyin sashen kasar Sin na kamfanin Yahoo.com. A sa'i daya, kamfaninsa ya samu jarin da ya kai dalar Amurka biliyan 1 da kamfanin Yahoo.com ya zuba. Game da wannan aikin sayen sashen kasar Sin na kamfanin Yahoo.com, Mr. Ma ya ce, "A ran 26 ga watan Yuli na shekara ta 2005, da na sauka a kasarAmurka, na gaya wa lauyoyi cewa, wannan ne kamfanin Alibaba da ya sayi sashen kasar Sin na Yahoo.com, ban hada kan jarin kamfanonin biyu ba, ba kamfanin Yahoo ne ya sayi kamfanin Alibaba ba. Idan babu wannan magana, to shi ke nan, ba za mu yi shawarwari ba."

Bayan kamfanin Alibaba ya sayi sashen kasar Sin na kamfanin Yahoo.com, ba ma kawai kamfanin Alibaba ya samu jarin da ya kai dalar Amurka biliyan 1 ba, har ma ya samu jerin abubuwa kyauta, kamar su shafin Internet na Yahoo.com na Sinanci da shafin binciken sauran shafuffukan internet na Yahoo da talla kuma da ikon yin amfanin da alamar Yahoo.com a nan kasar Sin har abada. Abin da kamfanin Alibaba ya bayar shi ne takardun hannun jari da suka kai kashi 40 cikin kashi dari kuma da ikon jefa kuri'u da suka kai kashi 35 cikin kashi dari kuma da wani mukamin dake cikin majalisar shugabannin kamfanin.

Kowa ya sani, kamfanin Yahoo.com wani babban kamfani ne da ke tsara shafuffukan Internet. Yanzu ya riga ya sayi kamfanoni 25 a duk fadin duniya, amma a da bai taba sayar da dukiyoyinsa ba. Amma me ya sa kamfanin Yahoo.com ya sayar wa kamfanin Alibaba karamin kamfaninsa da ke nan kasar Sin? Ma Yun ya ce, "Ina da kwakwalwa daya kawai kamar sauran mutane. Kuma ni ramamme ne kwarai. Ba ni da kyaun gani. Amma a ganina, mutum maras kyaun gani yana da hankali kwarai."

A shekarar 1964 ne aka haifi Ma Yun a birnin Hangzhou da ke gabashin kasar Sin. Bai taba shiga jami'a ba, sai ya koyi harshen Turanci kuma ya gama karatu a wata makarantar Polytechnique. Bayan da ya gama karatu, ya fara koyar da harshen Turanci a wata makaranta. Bai san kimiyya da fasaha ba, kuma ba shi da kudade da yawa. Dalilin da ya sa Ma Yun ya iya cin nasara shi ne, a kullum yana cike da imani ga aikinsa.

A shekarar 1996, Ma Yun bai ci nasarar sayar da shafin Internet nasa a nan birnin Beijing ba, babu sauran hanyar da zai iya zaba, sai ya koma garinsa Hangzhou. A shekarar 1999, ya kafa kamfanin Alibaba a birnin Hangzhou, ya ci nasara kadan domin a lokacin can, harkar shafin Internet ta samu ci gaba cikin sauri sosai. Amma a shekara ta 2000, yunkurin raya tattalin arzikin shafin Internet ta ci tura a duk duniya. Harkar shafin Internet ta shiga mawuyacin lokaci. Kamfanonin shafin Internet masu dimbin yawa sun rufe kofa. Mutane wadanda suke aiki a kamfanin Alibaba ma sun gudu daga kamfanin. Amma Ma Yun ne kawai ya tsaya tsayin daka ya ci gaba da aiwatar da kamfaninsa na Alibaba.

Mr. Wang Juntao, shugaban kamfanin 6688 na Beijing yana ganin cewa, "A Hakika dai, wancan lokacin lafawa ne na masu zuba jari. A ganina, idan za a tsawaitar da wannan lokacin lafawar, mai yiyuwa ne wannan abu mai kyau ne ga kamfanin Alibaba domin sauran sana'o'in da yake dogara suna ta samun bunkasuwa. Yawan mutanen da suke kama kan shafin Internet yana ta samun karuwa. Masana'antun da suke yunkurin yin ciniki a kan shafin Internet suna kuma ta samun karuwa cikin sauri. "

A karkashin kokarin kamfanin Alibaba da Ma Yun, a shekara ta 2001, yawan kudin shiga da kamfanin Alibaba ya samu a kowace rana ya kai kudin Renminbi yuan miliyan 1. Amma ya zuwa shekara ta 2004, yawan ribar da kamfanin Alibaba ya samu a kowace rana ya kai kudin Renminbi yuan miliyan 1. Ko da yake mutane suna da ra'ayoyi daban-dabam game da Ma Yun, amma Ma Yun na ci gaba da bin hanyar da ya zaba da kansa.(Sanusi Chen)