Ran 25 ga wata, kwamitin zabe na kasar Uganda ya sanar da cewa, shugaban kasar na yanzu kuma dan takarar jam'iyyar NRM da ke mulkin kasar Mr. Yoweri Museveni ya ci nasarar babban zaben shugaban kasar da aka yi a ran 23 ga wata, ya sake zama shugaban kasar. Zai kafa sabuwar gwamnatin kasar a watan Mayu na shekarar da muke ciki. Masu nazarin harkokin yau da kullum suna ganin cewa, a lokacin da ba a kwantar da tawaye a arewacin kasar daga duk fannoni ba tukuna, kuma kasashen yamma sun hada da jam'iyyun 'yan hamayya suna matsa lamba, yadda za a shugabanci wata gwamnatin da jam'iyyu daban daban suka kafa da su yi takara da hadin gwiwa da juna wajen farfado da tattalin arzikin kasar, zai zama muhimmin kalubalen da Mr. Museveni zai fuskanta a cikin shekaru 5 masu zuwa.
Mr. Museveni, mai shekaru 63 da haihuwa a yanzu, ya hambarar da gwamnatin soja na kasar a shekara ta 1986, ya zama shugaban kasar. Ya ci nasarar sake zaman shugaban kasar a cikin babban zaben shugaban kasar da aka yi a shekarar 1996 da 2001. A watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, majalisar dokokin kasar ta yi wa tsarin mulkin kasar kwaskwarima, ta soke kayyadewar da aka yi kan wa'adin aikin shugaban kasar, ta yadda Mr. Museveni ya sami damar neman ci gaba da zama shugaban kasar.
A cikin shekaru 20 da Mr. Museveni yake mulkin kasar, kasar Uganda ta fid da kanta daga mawuyacin halin da take ciki wajen siyasa da tattalin arziki, al'ummomin kasar sun hada kansu, a maimakon yin yakin basasa da juna, an shimfida kwanciyar hankali a kasar, tattalin arzikin jama'ar kasar ya karu da kashi 6 bisa dari, wanda ya fi na yawancin kasashen Afirka. Amma a sa'i daya kuma, kasar Uganda ba ta fid da kanta daga jerin kasashe mafiya fama da talauci ba tukuna, gwamnatin kasar ba ta tafiyar da ayyukanta yadda ya kamata ba, manyan ayyukan kasar suna baya, kayayyakin da ta kera ba su da isasshen kwarewa a kasuwar duniya. Bisa halin da kasar Uganda take ciki a gida da waje a yanzu, Mr. Museveni ya dauki babban nauyi a cikin shekaru 5 masu zuwa.
Masa nazarin harkokin yau da kullum sun yi la'akari da cewa, ko da yake bunkasuwar tattalin arzikin kasar Uganda ta karu a shekarun nan da suka wuce, amma tana dogara da taimako da sayan kayayyaki daga kasashen waje sosai. Shi ya sa, kasashen yamma za su ci gaba da bin manufofin da suka bi a da, za su ba da tasiri kan sabuwar gwamnatin kasar daga fannonin tattalin arziki da diplomasiyya da dai sauransu. An zargi shugaban jam'iyyar 'yan hamayya Mr. Kizza Besigye da laifuffukan cin amanar kasa da fyade, majalisar dokokin kasar ta yi kwaskwarima kan tsarin mulkin kasar, ta soke kayyaden wa'adin aikin shugaban kasar, dukan wadannan al'amura sun jawo rashin jin dadi daga wasu kasashen yamma, a sakamakon haka, kasashen Birtaniya da Holland da Norway sun janye taimakon kudi daga kasar Uganda bi da bi. Yanzu yawan taimakon kudin daga waje da ke cikin kasafin kudi ya ragu daga kashi 60 cikin dari na shekarar 2004 zuwa kashi 40 cikin dari na yanzu.
A sa'i daya kuma, saboda babban zaben da aka yi a wannan gami, manyan jam'iyyun 'yan hamayya na kasar sun kara samun fasahohi, da kuma tattara masu goyon bayansu da kudade, sun riga sun zama wani karfin da ba za a iya raina shi ba. Ban da wannan kuma, har zuwa yanzu, sojoji 'yan tawaye da ke arewacin kasar ba su kwance damara sosai ba, sun jawo mugun tasiri kan sabuwar gwamnatin kasar, a matsayin dalilin rashin kwanciyar hankali a kasar, sun kuma ba da tasiri kan zuba jari daga waje da bunkasuwar tattalin arzikin arewacin kasar kai tsaye.
A shekarun baya da suka wuce, wasu 'yan kasar Uganda sun nuna damuwarsu sosai saboda jami'an gwamnatin kasar sun ci hanci da rashawa, kuma yawan mutanen masu rashin aikin yi ya karu, sun rage aniyarsu ga gwamnatin kasar.
Masu nazarin harkokin yau da kullum sun nuna cewa, a karkashin lambar da gida da waje suka matsa mata, wajibi ne sabuwar gwamnatin kasar Uganda ta samu ci gaba a bayyane a fannonin rage masu fama da talauci da aikin ba da ilmi da masana'antu da sauran muhimman ayyuka, in ba haka ba, ba ta tabbatar da matsayinta na mulkin kasar da kuma shimfida kwanciyar hankali a kasar ba.(Tasallah)
|