Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-27 09:35:53    
Wata gardamar kayayyakin tarihi ta tashi a jami'ar Beijing sabo da ana neman rushe tsofaffin dakunan tarihi na wannan jami'a

cri
kwanan baya, jami'ai na jami'ar Beijing sun tsaida wani kuduri cewa, za a rushe wadansu tsofaffin dakuna da gina sabbin dakuna. Amma, wannan al'amari ya jawo ban kula daga dimbin jama'a har an yi gardamar kayayyakin tarihi tsakanin jami'ai na wannan jami'a da dalibai da malamai da sashen kula da kayayyakin tarihi. Yanzu ga abubuwan da wakilin rediyon kasar Sin ya rubuto mana daga wurin jami'ar nan filla filla:

Ga sashen jami'ai na wannan jami'ar nan sun bayyana cewa, a wurin nan koda yake an kasance da wadansu dakunan tarihi, amma yanzu sun riga sun fara lalace, kuma ga wuraren nan dakunan tarihi a cunkushe haka, ga wadansu mutane sun ba bayana cewa,in mun rushe wadannan tsofaffin dakunan tarihi, za mu gina wasu sabbin gine gine masu benaye da yawa, kila malamai da dalibai ba za su iya nuna yardarsu ba, kuma ga wani mai ra'ayi daban ya ce, wannan al'amari ya gaya mana cewa, kiyaye kayayyakin tarihi yana da wuya sosai.

Wannan al'amari ya jawo mugun sakamakon haka, ga shugabannin jami'ar nan ba su iya kimantawa haka ba. Yanzu Sabo da gardamar kayayyakin tarihi ta tashi, sai gwamnatin birnin Beijing ta riga ta dakatar da nuna yarda ga shirin ayyukan rushewar tsofaffin dakunan tarihi da kuma gina sabbin dakunan. Bugu da kari kuma gwamnatin birnin Beijing ta sake nemi kwararrun tarihi da su ci gaba da bincike dakunan tarihi.

A farkon watan nan da muke ciki, wata jaridar birnin Beijing ta buga wani labari cewa, don gina wani babban gini mai benaye da yawa na cibiyar bincike ilmin matsematics na duniya na Beijing, sai za a yi shirin rushe wadansu tsofaffifn dakunan tarihi don neman samu wurin sabbin gine gine.Bayan da aka barbaza wannan labari, sai bi da bi sassa watsa labaru fiye da goma da suka aike da wakilansu su je jami'ar Beijing don neman labarin nan.

Koda yake wannan lokaci na yanayin hunturu, amma takanas ne mutane da yawa na sassa daban daban sun zo wannan jami'a sun dauki hotuna don za su tunawa da wadannan dakunin tarihi. Daga cikinsu akwai mutane da yawa da suka gama karatu daga wannan jami'a. Ga wani saurayi kuma malami ne na wannan jami'a ya gaya wa wakilin rediyon cewa, bayan da aka barbaza wannan labari, sai malamai da dalibai na jami'armu sun je wurin nan, ya kuma ce, koda yake an kasance da wadansu dakunan tarihi, amma yanzu sun riga sun lalace, kuma a wurin nan an riga an gina sauran dakuna a cunkushe, irin haka yaya za a kiyaye dakunan tarihi, ra'ayina shi ne na nuna goyon baya ga sashen jami'ar don sake gina wani sabon gini mai kyau.

Amma, a tashar internet ta wannan jami'a, an kasance da ra'ayoyi daban daban, wato an yi gardama sosai tsakanin masu nuna goyon baya da masu nuna kiyewa, bayan da aka yi garda a jami'ar a karshe dai wannan al'amari ya jawo gardama daga dukkan jama'a na zaman al'umma.

Shin me yasa wani karamin al'amarin rushe tsofaffin dakuna na jami'a ya jawo hankunan jama'a na duk zaman al'umma ? Domin wannan jami'ar Beijing tana tsawon tarihi sosai da sosai.

Wurin wannan jami'a shi ne wurin sarki na karshe na daular Qin na kasar Sin. Ga shahararren lambun shan iska na Beijing yana kusa da wannan wuri, sabo da haka dukkan dakunan tarihi na sarkin daular Qin sun mamaye wurare da yawa dake yammacin birnin Beijing.

Yanzu, abin farin ciki shi ne sashe mai iko na kasar Sin ya riga ya fara neman ra'ayoyin jama'a, yaya za a yi sai mu zura ido ga karshen sakamakon da za a samu.(Dije)