Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-27 09:14:32    
An rufe wasannin Olympic na yanayin sanyi da aka shirya a karo na 20 a birnin Turin na kasar Italiya

cri

An rufe wasannin Oympic na yanayin sanyi da aka shirya a karo na 20 a birnin Turin na kasar Italiya a ran 26 ga wata (Agogon wurin).

An bude wasannin Oympic na yanayin sanyin nan ne gadan gadan a ran 10 ga wata, kuma an shafe kwanaki 17 ana yinsu. 'Yan wasa sama da 2500 da suka fito daga kasashe da shiyyoyi sama da 80 sun shiga gasanni, yawan lambobin zinariya da suka samu ya kai 84 a manyan fannonin wasanni 15.

Kasar Sin ta aika da 'yan wasanninta da yawansu ya kai 78 don shiga gasanni da aka yi a manyan fannonin wasanni guda 9, kuma sun sami lambobin zinariya 2 da azurfa 5 da kuma tagulla 5, wato ke nan kasar Sin ta zo ta 9 ke nan wajen samun yawan lambobin.

Yawan lambobin zinariya da kasar Jamus ta samu su ne mafi yawa, kasar Amurka ke biya mata, kasar Austria kuma ta zo ta uku.

Za a shirya wasannin Oympic na yanayin sanyi a karo na 21 a birnin Vancouver na kasar Canada a shekarar 2010. (Halilu)