Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-21 16:53:59    
Kogunan dutse masu ban mamaki da ake kira Huashan a kasar Sin

cri

Kogunan Dutse na Huashan na dab da shahararren wurin yawon shakatawa mai suna Huangshan na lardin Anhui da ke a kudu maso gabashin kasar Sin. In an tashi daga Huangshan cikin mota, za a yi tafiyar da ba ta kai sa'o'i biyu ba, sa'an a isa manyan duwatsu wadanda fadinsu ya kai muraba'in kilomita 7, a nan ne kogunan dutse na Huashan suke.

Bisa binciken da aka yi, an gano cewa, yau da shekaru 1,700 ke nan da aka fara huda kogunan dutse na Huashan. Daga cikin kogunan dutsen nan 36, akwai wani kogon dutse mafi girma wanda fadinsa ya kai murabba'in mita 12,000, wato ya tashi daidai da filayen wasan kwallon kwando guda 10. Tun bayan da aka gano wadannan kogunan dutse, ana ta nutsewa cikin kogin tunani a kansu.

Malama Shao Shuangjuan, jagorar yawon shakatawa ta wurin da kogunan dutsen suke ta bayyana wa wakilinmu cewa, an huda kogunan dutsen Huashan da yawa kamar haka, amma an yi mamaki da rashin ganin duwatsu da aka farfasa daga wadannan koguna. Ta ce, "bayan da aka huda kogunan dutse manya da kanana da yawa kamar haka, ana ganin ko shakka babu, za a sami duwatsu masu dimbin yawa daga kogunan nan. Amma har yanzu dai, ba a gano wurin da duwatsun nan da girmarsu ta kai cubic mita miliyoyi suke ba. Wannan abu ne mai matukar ban mamaki gare mu. "

Haka nan kuma wani abin da ke da wuyar fahimta shi ne, makasudin kogunan nan da mutanen zamanin da suka huda. Madam Lu Xiaoping wadda kullum ke sha'awar kogunan dutse masu ban mamaki na Huashan ainun ta bayyana wa wakilin gidan rediyonmu cewa, an nuna ra'ayoyi daban daban a kan makasudin huda wadannan kogunan dutse, amma a hakika dai , ya zuwa yanzu ma ba a iya tabbatar da shi ta hanyar zamani ba. Ta kara da cewa, "idan an ce wai an huda kogunan dutsen nan don samun duwatsu da za a yi amfani da su, to, me ya sa ba a farfasa dutsen kai tsaye ba. Bisa ra'ayi da aka gabatar a kan cewa, wai an huda kogunan dutsen nan domin zaunar da sojoji da tanadin hatsi, amma akwai damshi sosai a kogunan. Haka zalika an gabatar da ra'ayi daban cewa, wai an huda kogunan dutsen nan ne domin samun kabarin sarkin kasa, amma ba a taba tabbatar da shi ba. Sabo da haka da kyar za a iya tabbatar da makasudin nan."

Dazu mun riga mun bayyana muku wasu abubuwa masu ban mamaki na kogunan dutsen Huashan, yanzu kuma za mu yi bayani a kan abubuwa da ke cikin kogunan nan. Alal misali, a cikin kogunan dutsen Huashan mafiya girma wanda fadinsa ya kai muraba'in mita 12,000, zurfinsa kuma ya tashi mita 170, akwai dakunan dutse manya da kanana da yawansu ya kai 36, fadin daki da ya fi ko wane karanta ya kai murabba'in mita 2 kawai, ban da dakunan dutse kuma akwai gadoji da gadaje duk irin na dutse da makamantansu.

Watakila, wadannan abubuwa masu ban mamaki sun jawo hankulan masu sha'awar gano asirin abubuwa da suka fito daga wurare daban daban na duniya da suka ziyarci kogunan nan. Bayan da Mr Tom Chase, dan yawon shakatawa na kasar Amurka ya ziyarci kogunan nan, ya yi hira da wakilin gidan rediyonmu cewa, yana sha'awar wadanna kogunan dutse masu bata hankali sosai. Ya ce, "kogunan dutsen Huashan abubuwa ne masu ban sha'awa ainun. Ban taba ganin irin wadannan kogunan dutse ba a da. Na fahimci cewa, yau da shekaru 1700 da aka huda wadannan kogunan dutse, mai yiwuwa ne, makasudin huda kogunan nan shi ne domin samun duwatsu da aka yi amfani da su, amma ba a san inda wadannan duwatsu suke ba a yanzu. Tun can zamanin da, an huda wadannan kogunan, amma wa ya taba kwana a ciki? Watakila sojoji sun taba kwana a ciki, amma ba a iya tabbatar da duk wadannan abubuwa ba, da ya ke ba a sami abubuwan shaida ba, ana yi ta cincinsu kawai."

A hakika dai, idan wani ya sami damar sa kafa a cikin kogunan dutsen Huashan, to, mai yiwuwa ne, zai gano sabbin abubuwa masu rikitar da hankalin mutane, sa'an nan kuma zai gano amsarsu. (Halilu)