Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-20 09:57:15    
Birnin Beijing zai yi kokarin kago da kafa sana'ar nuna al'adu iri iri

cri
Jama'a masu kataru yanzu ga shirin al'adu na zamani namu na yau: jama'a masu karatu, ba da dadewa ba, a birnin Beijing za a shirya taron musamman na nuna wasanni iri iri kamar na tsibirin Puji na kasar Thailand. Kwanan baya, wani shugaba na ofishin al'adu na birnin Beijing ya gana da wakilin rediyonmu ya bayyana cewa, a tsibirin Puji na kasar Thailand, an gina wani lambun shan iska mai al'adun musamman, akan nuna wasan opera iri iri a kowace rana a wannan lambun shan iska. A cikin wasan opera, akan bayyana tatsuniyoyin al'adu na gargajiya na kasar Thailand, 'yan wasa fiye da dari sukan shiga wannan wasa, kuma ta hanyar dauke da fasaha ta zamani wajen aza kayayyaki masu ci gaba sosai a kan dakilin nuna wasa da haske iri iri don kara bayyana ma'anar tatsuniyoyin al'adu iri iri.cikin kuma akwai manyan giwaye da sauran dabobbi iri iri don kara halin annashuwa wajen nuna wasanni iri iri. Sai 'yan kallo suna jin dadi sosai kamar suke cikin halin gaskiya ne.

Wannan shugaban ofishin kula da al'adu na birnin Beijing ya bayyana cewa, dalilin da ya sa irin dakalin nuna wasanni iri iri ya jawo sha'awar mutane na duk duniya sosai. Ya ce,sabo da haka ne kafin shekara ta 2007, birnin Beijing zai zabi wata tatsuniyar al'adu na gargajiya da ta shahara a duk kasar Sin, za a bayyana ma'anar wannan tatsuniyar al'adu ta hanyar zamani, kuma za a kara ma'anarta iri iri don hada tarihi da na zamani da kyau.

Wannan shi ne wani kashi dake cikin sana'ar kagowa na al'adu na birnin Beijing, a gun manyan taruruwan da birnin Beijing ya shirya, an gabatar da babbar manufar mai da sana'ar fasaha da nuna wasanni iri iri da su zama abubuwan ingiza bunkasuwar tattalin arziki na birnin Beijing. A gun wani taron da aka shirya, shugaban birnin Beijing ya bayyana cewa, aikin bunkasa sana'ar nuna wasa na birnin Beijing yana da kyakkyawan sharuda sosai, musamman mutane na birnin Beijing suna da yawa sosai, in mutane masu yawa haka sun zama 'yan kallo sai za a iya samu arzikin ci gaban al'adu, ban da haka kuma a birnin Beijing akwai tashoshin internet da yawa da ma'aikatar fitar da sinima da yawa da sauran ayyukan al'adu iri iri, in an yi kokarin neman kago sana'ar al'adu sosai, za a iya samu bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri kuma ba tare da kashe ruwa da yawa da lantarki da yawa da mamaye gonaki da yawa.

Ya kuma ce, shekara ta 2006, shekara ta farko da aka fara tafiyar da shiri na ll na shekaru biyar biyar.Sabo da haka ofishin kula da al'adu na birnin Beijing yana shirin zai neman bayyana fifitaccen al'adu na hedkwatar kasar Sin, za a yi ta kago da shirya aikace aikace nuna wasanni masu fasaha na wake wake da na raye raye da na opera iri iri na zamani don jawo sha'awar mutane na gida da na kasashen duniya, A karshe dai za a kara ba da taimako ga aikin shakatawa da sassan dafa abinci iri iri da sha'anin nuna nishadi da sauran sassan da abin ya shafa. Ya kuma ce, a da, birnin Beijing ya riga ya shirya wasanni iri iri, kamar an shirya wasan opera na birnin Beijing na duniya, da nuna shirye shiryen makada da wasan raye raye da taron nuna wasanni na sabuwar shekara da shagulgula iri iri kuma da bikin al'adu na wasan 0limpic.

Wani mataimakin shugaban birnin Beijing mai suna Sun Anmin ya bayyana cewa, yawan mazauna na birnin Beijing sun kai fiye da miliyan l5, ban da haka kuma sauran mutane dake neman aiki yi da kai ziyara ga 'yan gidansu da sha hutu da sauran sassa sun kai fiye da miliyan 3, Ban da haka kuma a kowace shekara, yawan masu yawon duniya da suka zo birnin Beijing don yin shakatawa sun kai wajen miliyan l00. (Dije)