Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-17 17:16:04    
Wang Meng ta samu lambar zinari ta farko ta kungiyar 'yan wasan kasar Sin a wasannin Olympics na Turin

cri

A gun gasar wasan gudu a kan kankara ta mata ta gajeren zango na mita 500 da aka yi a Turin a ran 15 ga wata, agogon wurin, 'yar wasan kasar Sin mai suna Wang Meng ta samu lambar yabo ta zinari, wadda kuma ta zama ta farko da kungiyar 'yan wasan kasar Sin ta samu a gun wannan wasannin Olympics na lokacin hunturu na Turin. To, shin yaya Wang Meng ta samu wannan lambar yabo ta zinari, kuma ita wace irin 'yar wasa ce? Yanzu sai ku sha bayanin da wakiliyarmu ta ruwaito mana.

Wannan ne karo na farko ga Wang Meng wadda shekarunta bai kai 21 ba da ta shiga wasannin Olympics. Amma duk da haka, an dora mata babban nauyin neman samun lambar yabo ta zinari a gun gasar wasan gudu a kan kankara ta mata ta gajeren zango na mita 500. A gun wasannin Olympics na lokacin hunturu na shekara ta 2002 wanda aka yi a birnin Salt Lake, daidai ne a wajen wannan gasar, 'yar wasan kasar Sin wadda ake kira Yang Yang ta zama zakara, kuma lambar yabo ta zinari da ta samu ta zama ta farko da kungiyar 'yan wasan kasar Sin ta samu a wasannin Olympics na lokacin hunturu. A shekaru hudu daga baya, kungiyar 'yan wasan kasar Sin ta zarce takwarorinta na sauran kasashe a wannan fanni. Sabo da haka, kungiyar 'yan wasan gudu a kan kankara ta kasar Sin tana ganin cewa samun lambar yabo ta zinari a wannan gasar aiki ne da tilas ne a kammala. Ko da yake ana ganin Wang Meng 'yar wasa ce da ta fi iya cimma nasara a wannan gasar, amma sabo da nauyin da aka dora mata, da wuya ne ta saki jiki.

Sabo da haka kuma, tun daga gasar farko da aka yi a ran 12 ga wata, Wang Meng ba ta samu sakin jiki sosai ba. Amma ya zuwa ran 15 ga wata, bisa cenki-cenkin da aka yi, an hada Wang Meng da manyan takwarorinta biyu, wato Evgenia Radanova ta kasar Bulgaria da Kalyna Roberge ta kasar Canada a cikin kungiya daya a gasar kusan karshe, kuma wadda za ta sha hasara a gasar kusan karshe za ta fita daga gasar. Amma abin farin ciki shi ne a gaban wannan babban kalubale, Wang Meng ba ta kara dari-dari ba, a maimakon haka, sai ta fara saki jiki. A cikin gasar kusan karshe, Wang Meng ta wuce takwarorinta, kuma ta shiga gasar karshe kamar yadda ya kamata, kuma Kalyna Roberge ta fita daga gasar. Yi Min, malamar wasan gudu a kan kankara na gajeren zango tana ganin cewa, nasarar da Wang Meng ta samu a gasar kusan karshe, ba ma kawai ta cire wata babbar takwararta daga gasar ba, har ma ta lashe Evgenia Radanova wadda ke rike da matsayin bajimta na duniya na gasar, kuma ta karfafa imanin kanta.

Abin da muka gani a gasar karshe ya tabbatar da cewa, kyawawan aikin Wang Meng a gasar kusa da na karshe ya shimfida harsashi mai kyau a gasar karshe, har ma ta zama zakara daga karshe.

Lambar yabo ta zinari da Wang Meng ta samu ta kwantar da hankulan Sinawa duka. Bayan gasar, wannan yarinya ta bayyana cewa, tana fatan za ta kara samun lambobin yabo a cikin gasar da za a yi a nan gaba. Ta ce, "Hasali ma dai, ya kamata in fara natsuwa daga nan, sabo da a nan gaba a ran 25 ga wata, muna da karin gasa, zan shiga gasanni uku, musamman ma a gasar yada kanin wani ta mita 3,000, kuma kamata ya yi in mai da hankali a kan gasar da zan shiga a nan gaba, in yi iyakacin kokari don kara wa kungiyarmu lambobin yabo."