Assalamu alaikum, jama'a masu karatu, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Duniya ina Labari. A ran 15 ga wata, ma'aikatar sha'anin kudi ta kasar Sin ta bayar da jerin tsare-tsaren aikin akanta na masana'antu da tsare-tsaren aikin bincike kan akantocin da suka yi rajista. Minista Jin Renqing, ministan sha'anin kudi na kasar Sin ya ce, wannan ya almantar da cewa, kasar Sin ta riga ta kafa tsarin rikon kwarya na aikin akanta da tsarin binciken kudi da ke dacewa da tsare-tsaren aikin akanta da sauran kasashen duniya suke bi.
A farkon shekarun 1990 da suka gabata ne aka kafa tsarin aikin akanta da ka'adojin aikin akanta na masana'antu da kasar Sin take bi bisa halin da masana'antun kasar Sin suke ciki a wancan lokaci. A wancan lokaci, kasar Sin ta fara juya tsarin raya tattalin arziki bisa shirin da aka tsara zuwa tsarin takarar harkokin kasuwanni. Amma, yanzu, tsarin takarar harkokin kasuwanni ya samu bunkasuwa da sauye-sauye sosai a nan kasar Sin, don haka dole ne a yi kwaskwarima kan tsarin aikin akanta da tsarin aikin binciken kudi da aka tsara a da domin biyan bukatun da ake nema.
Mr. Jin Renqing, ministan sha'anin kudi na kasar Sin ya ce, "An tsara wannan sabon tsarin aikin akanta ne bisa ka'idar kyautata ingancin aikin akanta. An tsara ka'idoji da yawa domin tabbatar da ingancin aikin akanta bisa ka'idojin da sauran kasashen duniya suke bi. Sannan kuma an yi koyi da sabon sakamakon da sauran kasashen duniya suka samu wajen tabbatar da ingancin aikin binciken kudi, an tsara tsarin aikin binciken kudi kan akantocin da suka yi rajista."
Jin Renqing ya ce, da farko dai, za a aiwatar da sabon tsarin aikin akanta da tsarin aikin binciken kudi ne a cikin kamfanoni da masana'antun kasar Sin wadanda suke cinikin takardun hannun jari a kasuwannin takardun hannun jari a shekara mai zuwa. Sannan kuma za a aiwatar da su a cikin sauran manya da matsakaitan masana'antu na kasar Sin.
Bayan da aka samu labarin bayar da wadannan sabbin tsare-tsare, masanan tattalin arziki na kasar Sin da na kasashen waje sun nuna yabo sosai a kai.
Mr. Zhou Zaiqun, mataimakin shugaban bankin kasar Sin ya ce, "Sabon tsarin aikin akanta da aka bayar yana kama da na sauran kasashen duniya. Sabo da haka, lokacin da bankinmu yake yunkurin neman izinin shiga kasuwannin takardun hannun jari ta duniya, za mu iya kawar da bambancin da ke kasancewa a tsakanin takardun akanta da za mu tsara bisa tsarin aikin akanta na kasar Sin da takardun akanta da za mu tsara bisa tsarin akanta da ake bi a kasashen waje. Wannan yana da amfani sosai ga yunkurin neman jari da raya harkokinmu a kasashen waje."
Wasu masanan tattalin arziki sun nuna cewa, sabon tsarin aikin akanta da tsarin binciken kudi kan akantocin da suka yi rajista za su ba da gudummawa sosai wajen raya kasuwar takardun hannun jari a nan kasar Sin. Mr. Li Xiaoxue, wani jami'in kwamitin sa ido kan kasuwar takardun hannun jari na kasar Sin ya ce, cikakken tsarin aikin akanta da tsarin binciken kudi kan akantocin da suka yi rajista muhimman ayyuka ne da aka yi domin raya kasuwar takardun hannun jari.
Bugu da kari kuma, Mr. David Teddy, shugaban kwamitin kula da ka'idojin aikin akanta na duniya, wato IASB yana ganin cewa, tsarin aikin akanta da tsarin binciken kudi kan akantocin da suka yi rajista da kasar Sin ta tsara suna kama da na IASB, wannan wani muhimmin taki ne da kasar Sin ta dauka domin kyautata matsayinta a kasuwar takardun hannun jari ta duniya. Wannan yana da amfani wajen jawo jarin waje a kasar Sin. Mr. David ya ce, "A bayyane ne kasar Sin za ta samu moriya domin ta yi kwaskwarima kan tsarin aikin akanta. Kasar Sin ta sa wasu ka'idojin da masu zuba jari na waje suka saba da ssu a cikin sabon tsarinta na aikin akanta. Wannan zai sa masu zuba jari su kara amincewa da kasuwar takardun hannun jari da rahotannin akanta na kasar Sin. Wannan kuma zai kara sa kaimi kan yunkurin zuba jari a kasuwar takardun hannun jari ta kasar Sin da ta waje." (Sanusi Chen)
|