A ran 15 ga wata jami'an gwamnatocin kasar Sin da ta Amurka wadanda ke halartar taron dandalin tattalin arziki da ciniki da ake yi a nan birnin Beijing sun bayyana cewa, matsalar rashin daidait0 wajen ciniki ba zai jawo mugun tasiri ga ci gaban dangantakar tattalin arziki da ciniki tsakanin kasashen 2 ba. Kasar Sin ta bayyana cewa, matsalar rashin daidaitu wajen ciniki tsakanin Sin da Amurka ba ta yi tsanani kamar yadda ake yin furofaganda yanzu cikin kasar Amurka ba, Amurka ita ma ta bayyana cewa, bangarorin 2 wato Amurka da Sin za su yi kokarin rage gibin kudi da aka samu wajen ciniki ta hanyar yin shawarwari. To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku wani bayanin da wakilinmu ya rubuto mana kan wannan labari.
A ranar Alhamis ta makon jiya, ma'aikatar kasuwanci ta Amurka ta sanar da cewa, yawan gibin kudin da aka samu wajen ciniki tsakanin Amurka da Sin ya karu da kashi 24.5 cikin 100 bisa na shekarar bariya, wato ya kai dala biliyan 201.6. Wannan ya jawo hargitsi cikin kasar Amurka, wasu 'yan majalisar dokokin kasar da wasu kungiyoyin da abin ya shafa sun dauki wannan batu bisa dalilin karya don rokon gwamnatin Bush da ta mats wa kasar Sin.
Mr. Yi Xiaozhun, mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin ya mai da martani ga yawan gibin kudin da Amurka ta bayar kan cinikin da ake yi tsakanin kasashen 2. Lokacin da yake halartar taron dandalin tattalin arziki da ciniki tsakanin Sin da Amurka ya ce, gibin kudin da aka samu wajen ciniki tsakanin Amurka da Sin an same shi ne sabo da dalilai daban-daban, kasar Sin tana nan tana kokarin daidaita wannan matsala. Ya ce, "Da farko, sana'o'in kere-kere na kasashen duniya sun kawar da sana'o'insu da yawa cikin kasar Sin, wannan ya jawo babban gibin kudi ga cinikin da ake yi tsakanin Amurka da Sin. Ban da wannan kuma, kaurar da sana'o'in kasashen duniya ita ma ta haifar da sauyin gibin kudin ciniki. Sakamakon jarin da wasu kasahsen gabashin Asiya suka zuba a kasar Sin, rarar kudin ciniki a tsakaninsu da Amurka ita ma ta kaura zuwa kasar Sin".
A gun taron dandalin tattalin arziki da ciniki tsakanin Sin da Amurka, Mr. Rudy Pumintuan, shugaban kwamitin shawarwarin harkokin Amurkawa 'yan asalin Asiya da tekun Pasific na fadar gwamnatin Amurka ya bayyana cewa, ya kamata kasashen 2 wato Sin da Amurka su kara hadin gwiwa tsakaninsu don daidaita matsalar rashin daidaito wajen ciniki. Ya ce, "Kasashen 2 wato Sin da Amurka dukkansu muhimman kasashe ne kan dandalin duniya, yanzu dangantakar kasashen duniya sai kara sauye-sauye ta ke, ba za mu iya samun moriyar da muke bukata tare ba face sai an kara bunkasa dangantakar tattalin arziki da ciniki tsakanin kasashe daban-daban. Yanzu kasar Sin ta riga ta zama babbar kasa ta 4 ga Amurka wajen fitar da kayayyakinta zuwa kasashen waje. Ko da yake ya kasance da babban gibin kudin ciniki a tsakaninmu, amma abin da ya kamata a bayyana shi ne, yawan kudin da kamfanonin kasar Amurka suka samu a shekarar da ta wuce wajen fitar da hajjoji da ayyukan hadima zuwa kasar Sin ya kai fiye da dala biliyan 40, wannan ya zama wani babban ci gaba, wato an rage rashin daidaito wajen ciniki ta hanyar yin kokari tare tsakanin bangarorin 2."
Ana sa ran alheri cewa, jimlar kudin da kasar Sin za ta samu cikin shekaru 5 masu zuwa wajen sayen hajjoji daga kasashen waje za ta wuce dala biliyan 5000, wannan ya samar da wata babbar kasuwa ga kasashen waje. (Umaru)
|