Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-16 09:38:01    
Hukumar Tsaron Lafiya ta kasar Sin tana mai da muhimmanci kan karfafa ayyukan kananan hukumomi

cri

Assalamu alaikum ! Jama'a masu karantun shafinmu na Internet, ga shirinmu na musamman na "Duniya ina labari" na yau mai lakabin haka : Hukumar Tsaron Lafiya ta kasar Sin tana mai da muhimmanci kan karfafa ayyukan kananan hukumomi .

Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , a cikin 'yan shekarun da suka shige , Hukumar tsaron lafiya ta kasar Sin sun yi ta karfafa da kyautata aikin tsaron lafiyar jama'a . Yanzu jama'a sun ba da martani cewa , a wajen tafiyar da dokokin shari'a an kasance da wasu matsaloli. Sa'an nan kuma wadannan matsalolin sun fito daga kananan hukumomin da suke cudanya kai-tsaye da jama'a . Saboda haka a ran 7 ga watan nan wani jami'in Hukumar tsaron lafiya ta kasar Sin ya bayyana cewa , a wannan shekara , Hukumar Tsaron Lafiya ta kasar Sin za ta mai da muhimmanci kan karfafa ayyukan sassan tsaron lafiyar jama'a da na kananan hukumomi da sassan 'yan sanda masu kula da harkokin wakafi da kurkuku .

A cikin 'yan shekarun da suka shige , hukumomin tsaron lafiyar jama'a na kasar Sin sun kyautata ayyukan 'yan sanda kuma sun dauki matakan ba da taimako ga jama'a . Sa'an nan kuma sun mai da muhummanci kan aikin karfafa ingancin 'yan sanda a wajen siyasa da hakikannun harkoki . Saboda haka hukumomin sun warware matsalolin da jama'a suke gamuwa da su a cikin zaman yau da kullum kuma sun sami maraba daga mutane farar hula .

Wu Heping , mataimakin darekta na Ofishin Ma'aikatar tsaron lafiya ta kasar Sin ya ce , a sassan 'yan sanda ?kananan hukumomin tsaron lafiyar jama'a suna kai naushi ga makiya da kiyaye jama'a da yanke hukunci ga masu laifi dab a da aikin hidima ga jama'a . Saboda haka dole ne a karfafa sassan 'yan sanda da kara ingancin kananan hukumomi da kuma kara ba da amfaninsu a cikin aikin hidima .

Mr. Wu ya ce, yanzu jimlar karfin 'yan sanda na sassa daban daban na duk kasar ta kai rabin dukannin 'yan sanda na kasar . Hukumomin tsaron lafiyar jama'a na matakai daban daban na kasar Sin suna kokarin warware matsalar karancin 'yan sanda a kananan hukumomi . Wannan muhimmin aiki ne don kara karfin sassan 'yan sanda.

Mr. Wu ya jaddada cewa , don tabbatar da aikin karfafa kananan hukumomin 'yan sanda , hukumar tsaron lafiyar jama'a za ta kara karfin bude harkokin 'yan sanda da bude harkokin gwamnatoci . Ban da asirin da dokar shari'a ta kiyaye , kananan hukumomin za su fara bude harkokin 'yan sanda ga jama'a . Ya kamata a bai wa farar hula ikon gane abubuwan da suke shafar su . Kuma dole ne a bayyana ayyukan da 'yan sanda suka yi a fili . Ya karfafa cewa , Idan ana son kwatanta halin da shiyyoyin kauyuka ke ciki da hargitsi tsakanin jama'a , to , Hukumar Tsaron Lafiya ta kasar Sin dole ne ta mai da muhimmanci sosai kan karfafa ayyukan kananan hukumomin 'yan sanda .

To, jama'a masu karatun shafinmu , shirin "Duniya ina labari " da za mu iya kawo muku ke nan a yau . Ado ne ya fasara wannan bayanin . Da haka muke muku sallama tare da fatan alheri .( Ado)