Assalamu alaikum, jama'a masu karatu, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Duniya ina Labari. A ran 12 ga wata, jaridar "News of the World" ta kasar Britaniya ta buga jerin hotuna a kan jaridar. Wadannan hotuna sun bayyana cewa, wasu sojojin Britaniya da ke kasar Iraki suna ba da kashi tare da wulakanta wasu yaran kasar Iraki. Kafofin watsa labaru na Britaniya bi da bi ne suka yi suka kan lamarin. Sakamakon haka, matsalar Iraki da gwamnatin Tony Blair take yunkurin gujewa ta sake zama batun da ke jawo hankulan mutane sosai.
Jaridar "News of the World" ta kasar Britaniya ta bayyana cewa, an sami wadannan hotuna ne daga wani kaset da aka dauka a shekara ta 2004. A wancan lokaci, mazaunan lardin Basra na kasar Iraki inda ke cikin hannun sojojin Britaniya suna zanga-zanga. A cikin kaset din an ga wasu sojojin Britaniya sun cafke yaran Iraki 4 sun kai su a wani sansanin sojojin Britaniya, kuma an kai su bangon wani gini, sannan kuma suka yi ta ba da kashi wa wadannan yara da sanda a kafafu da naushi. Wani sojan Britaniya ne ya dauki wannan kaset na hotuna.
A wannan rana, sauran kafofin watsa labaru na Britaniya sun kuma nuna wadannan hotuna. Kamfanin BBC ya watsa kaset da ke dauke da wadannan hotuna har sau da yawa. Bayan da aka bayar da wadannan hotuna, ra'ayoyin bainal jama'a sun bayyana mamakinsu kwarai.
Da kakkausar harshe ne bangaren Iraki ya ba da amsa game da wannan matsala cikin sauri. A ran 13 ga wata a cikin shirin "Yau" na BBC, kakakin firayin minista Ibrahim Jaafari na Iraki ya bayyana cewa, gwamnatin rikon kwarya ta Iraki tana mai da hankali sosai kan matsalar. Ya ce, firayin minista Jaafari ya yi kira ga Tony Blair da manyan jami'an ma'aikatar tsaron kasar Britaniya da su dauki hakkin da ke wuyansu nan da nan, kuma su dauki matakan sa ido mafi tsanani domin tabbatar da cewa, ba za a sake haddasa irin wannan matsala ba. Bugu da kari kuma, Mohammed al-Abadi, jami'in koli na lardin Basra ya bayar da jawabi ta gidan rediyo mai hoto inda ya yi tir kan matsalar, kuma ya nemi Tony Blair, firayin ministan Britaniya da ya fara yin bincike kan matsalar.
A ran 13 ga wata, jaridun kasar Britaniya sun ci gaba da bayar da bayanan da abin ya shafa a kan muhimman shafuffukansu. A cikin wani shirin da kamfanin BBC ya bayar a ran 13 ga wata, wani hafsa mai ritaya ya bayyana cewa, mutanen Iraki sun bata ransu kwarai ga sojojin Britaniya domin abubuwa marasa ladabi da suka yi. Ya tabbatar da cewa, manyan hafsoshin Britaniya sun san aukuwar matsalar, amma ba su fadi kome ba kamar ba su san wannan matsala ba. A sa'i daya kuma, jaridar "The Daily Telegraph" da jaridar "The Independent" da sauran muhimman jaridun Britaniya sun damu kan halin da sojojin Britaniya suke ciki yanzu a kasar Iraki. Wasu mutanen rundunar soja ta Britaniya sun bayyana cewa, yanzu sojojin Britaniya suna da wuyar tabbatar da dangantaka a tsakaninsu da mazaunan wurin, wannan matsala za ta kara tsananta dangantakar da ke tsakaninsu.
A gaban ra'ayoyin bainal jama'a, Mr. Tony Blair, wato firayin ministan Britaniya wanda ke yin ziyara a kasar Afirka ta Kudu ya riga ya dauki alkawarin cewa, za a yi bincike kan matsalar. Amma a sa'i daya, ya yi muhawarar cewa, mafi yawancin sojojin Britaniya suna aiwatar da nauyin da aka dora musu a kasar Iraki da kyau domin tabbatar da dimokuradiyya da jama'ar Iraki suke nema. Haka nan kuma, a ran 13 ga wata, ma'aikatar tsaron kasar Britaniya ta shelanta cewa, an riga an cafke wani sojan da ke da dangantaka da matsalar. Wannan takin farko ne da aka yi domin yin bincike kan matsalar.
Bayan aukuwar yakin Iraki a shekara ta 2003, jama'ar Britaniya su kan yi shakkar cewa ko wannan yaki na halal ne tare da adalci? Bayan da aka bayar da matsalar ba da kashi da wulakanta wasu yaran kasar Iraki da sojojin Britaniya suka yi a Iraki, a kan hada taura biyu a baka, wato wannan matsala da batun wulakanta fursunoni da sojojin Amurka suka yi a kurkukun Abu Ghraib. Wannan ya sa Tony Blair cikin mawuyacin hali. Amma game da maganar janye jikin sojoin Britaniya daga Iraki, gwamnatin Blair ta kan bayyana matsayinta ba a kaikaice. (Sanusi Chen)
|