Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-15 18:21:54    
Tarihin wasan kwallon kafa

cri

To, Alhaji Hassan, gaskiya ne an fara yin wasan kwallon kafa ne a nan kasar Sin. Muna iya samun asalin wasan nan a shekaru 2300 da suka gabata a garin Linzi na lardin Shandong na kasar Sin, kuma shugaban kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya Joseph S Blatter ya riga ya tabbatar da wannan labari. Wasan kwallon kafa wani muhimmin wasan motsa jiki ne a duniyar yau, to amma yaushe kuma a ina ne aka fara yin wasan? Bisa nazarin da masanan ilmin tarihi suka yi, a ran 4 ga watan Faburairu na shekara ta 2004, kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya ta shelanta cewa, 'wasan kwallon kafa ya samo asalinsa ne a kasar Sin, wato wasan da ake kira Cuju da aka yi a kasar Sin a da da da can shi ne asalin wasan kwallon kafa.' Bisa nazarin da aka yi, an tarar da cewa, tun bayan da wasan kwallon kafa ya fito a nan kasar Sin a shekaru 2300 da suka wuce, sai ya yi ta bunkasa, har ma ya taba samun karbuwa a tsakanin masarauta. A wasu kayayyakin tarihin kasar Sin da aka samu, ana iya gano zane-zanen da aka yi a kansu dangane da wasan Cuju da Sinawa ke yi a da.

Amma an soma yin wasan kwallon kafa na zamani ne a jami'ar Cambridge ta kasar Birtaniya, amma ba a samu dokokin wasan ba sai dai har zuwa shekarar 1848. A shekarar 1863, an kafa kungiyar wasan kwallon kafa ta Ingila, kuma an daidaita dokokin wasan da su zama bai daya, daga baya kuma an yi ta bunkasa da kyautata dokokin. A shekarar 1872, an yi gasar wasan kwallon kafa a tsakanin kungiyar Ingila da ta Scotland, wannan ya zama gasa ta farko da aka yi a hukunce a tsakanin kungiyoyi a tarihin wasan kwallon kafa. A shekara ta 1904, an kafa kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya, daga nan, wasan kwallon kafa sai kara bunkasuwa yake ta yi, har ma ya samu karbuwa a duk fadin duniya.

Kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya, wato FIFA a takaice, an kafa ta ne a ran 21 ga watan Maris a shekara ta 1904 a birnin Paris na Faransa bisa shawarar da kasashen Belgium da Faransa da Denmark da Spain da Sweden da Holland da Switzerland suka bayar, a halin yanzu dai, akwai mambobi 204 a cikin kungiyar. A karkashinta kuma, akwai kungiyoyi na shiyya shiyya guda shida, wato na Turai da Asiya da Afirka da Amurka ta arewa da tsakiya da kuma Caribbean da Amurka ta kudu da Oceania. Babban aikin kungiyar FIFA shi ne bunkasa wasan kwallon kafa da kara mu'amalar sada zumunta a tsakanin mambobin kungiyar da jami'anta da kuma 'yan wasa ta hanyar yin gasa iri iri. Bayan haka, ita kuma ta dukufa a kan aiwatar da tsarin dokokin MDD da hana nuna bambancin kabilu da na siyasa da kuma addinai.

Gasar cin kofin duniya shi ne muhimmiyar hanyar da kungiyar FIFA ke bi wajen yin talla, kuma tana da masu kallonta da yawa. Kudin tikitoci da kudin da aka biya don nuna gasar ta telebijin da kudin tallafawa da kuma kudin ciniki sun samar wa FIFA babbar riba.

Muhimman gasa na kungiyar FIFA su ne gasar cin kofin duniya wadda a kan yi shekaru hudu hudu tun daga shekara ta 1930, sa'an nan kuma akwai gasar wasan kwallon kafa ta wasannin Olympic da gasar wasan kwallon kafa ta matasan duniya da gasar wasan kwallon kafa ta matan duniya da dai sauransu.

Babbar mujallar kungiyar FIFA ita ce 'labarun FIFA', wadda a kan buga a watanni daya daya.

Don neman tabbatar da ingancin aikin alkalan wasa a gun gasar duniya da ta shiyya shiyya, kungiyar FIFA ta kan kuma aiwatar da shiye-shiryen horar da alkalan wasan.

To, masu sauraro, mun dai yi muku bayani a kan tarihin wasan kwallon kafa da kuma kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya, wato FIFA a takaice, don amsa tambayar da mai sauraronmu daga birnin Zariya Hassan Bashir Abudul ya yi mana. Muna fatan kun ji dadinsa, kuma za ku ci gaba da aiko mana wasiku ko E-mail zuwa nan sashen hausa na rediyon kasar Sin da ke nan birnin Beijing. Da haka ni Lubabatu ke cewa, sai makon gobe war haka, idan Allah ya kai mu, ku kasance lafiya.(Lubabatu Lei)