Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-15 18:16:59    
Kayayyakin ado da ake yi a lokacin bikin yanayin bazara

cri

Ran 29 ga watan Janairu na shekarar da muke ciki, kasaitaccen biki ne na yanayin bazara na gargajiyar kasar Sin, mutanen kasar Sin suna sa ran alheri mai kyau ga shigowar sabuwar shekara da kuma bayyana halin da ake ciki na murnar bikin, kuma suna kan kayatar da gidajensu daga ciki zuwa waje ta hanyar yin amfani da kayayyakin ado da yawan gaske.

A kasar Sin, in ranar bikin yanayin bazara ta zo, to a kan rarrataya manyan fitilu masu launin ja a gidaje da kuma manna takardun da aka rubuta kalmar da ke da ma'anar alheri, wato da yarenmu ana cewa "Fu" a kofofin gidaje da dakuna tare da manna takardun da aka yi hotuna da ke da ma'anar aljannu a kofa, da yarenmu ana cewa "Men Shen" . A kan marikan kyaure, a kan manna takardu masu launin ja kuma masu dauke da kalmomin fatan alheri, a cikin bangunan dakuna, a kan kuma manna zane-zanen da aka yi don murnar bikin yanayin bazara , a wasu kauyuka, ana kuma yanke takardun da ke da hotuna iri iri don mannasu a tagogin gidaje, dukan al'adar gargajiya sun fito ne daga wani tatsuniyar da aka yi.

Ana yada ta da cewa, a tekun gabas, da akwai ni'imtaccen wuri a wani tsauni mai suna Dushuo , wato tsaunin Taodu ke nan. A kan tsaunin, an dasa wata babbar bishiyar peach, rassan bishiyar sun lankwashe a kasa tamkar wata babbar kofa, a tsaunin Dusho, aljannu da dodanni da dai sauran irinsu suna zama a can, in suna son sauka daga tsaunin, to dole ne su ketare babbar kofar, saboda haka an yi wa kofar nan wani lakabi cewa, "kofar dodanni", aljannun sararin samaniya suna tsoron fitinar da dodanni za su yi wa mutane, sai musamman babban aljanni ya aika da alajnnu guda biyu don yin gadi a kofar dodanni , wani da ake kiran shi da suna "Shen Shu", wani daban ana kiran shi "Yu Lu". Saboda haka, mutane sun yi hotunan Shen Shu da Yu Lu ko rubuta sunayensu a kan katakai irin na bishiyar peach, sun rarrataya su a gefunan kofar biyu don korar bala'I da dodanni. Ana kiran wadannan katakan Peach guda biyu da sunan "alamar peach".

Ya zuwa daular Tang a karni na 7, an cire hutunan aljannu Shen Shu da Yu Lu da ke kan katakan peach da kuma yin amfani da hotunan jarumai guda biyu na mutane , wato hotunan Qin Shubao da Wei Chigong. Duk saboda sarkin daular Tang Li Shimin ya kan yin mafarki da cewa, akwai kukan dodanni a wurin da ke waje da fadarsa, bai yi barci sosai babisa sakamakon hakan , shi ya sa ya aika da jarumansa guda biyu wato Qin Shubao da Wei Chigong don yin gadi a kofar fadarsa, sai nan da nan ya shiga barci sosai. Amma daga baya, sarki Li Shimin ya jin tausayi ga jarumansa guda biyu da ke yin gadi a kowane dare , sai ya ba da umurnin yin zanen da ke da hotunan jaruman nan guda biyu da ke da sifofin kwar jini , sa'anan an manna su a gefunan kofar don korar dodanni. An yada labarin nan sosai, sai mutanen farar hula su ma sun manna zanen da ke da hotunan Qin Shubao da Wei Chigong a gefunan kofofinsu, an ce su ne aljannun kofa.

Bayan daular Son ta kasar Sin, an yalwata zanen da ke da hotunan aljannu masu kori dodanni don su zama zane-zanen sabuwar shekara na kawo zaman alheri, ana kan sauya su a kowace shekara, ma'anar zane-zanen nan ita ce nuna fatan alheri da samun mukami da tsawon rai da zaman alheri da sauransu.

Alamomin Peach an riga an yalwata su da su zama takardu masu dauke da kalmomin fatan alheri, an rubuta kalmomin da tawada mai launin baki ko mai launin zinariya, an manna su a gefunan kofofin gida gida don bayyana burin duk mutanen iyali na nuna fatan alheri ga sabuwar shekara.

Yanzu, mutanen birane suna manna zane-zanen sabuwar shekara da takardu masu dauke da kalmomin fatan alheri ba da yawa ba , amma yawancinsu suna bin al'adar manna takardu masu launin ja da ke dauke da kalmomin fatan alheri wato kalmar "Fu", kuma abu mafi kyau shi ne a manna irin wannan takardar a juye, kamar a ce alheri ya zo da dai sauransu.

A kauyuka, a kan yanke takardu don su zama hotuna iri iri da ke da ma'anar neman samun alheri da lafiya da farin ciki da dai sauransu.(Halima)