Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-15 14:51:40    
Yawan kasashen Afrika masu fitar da man fetur ya karu sosai

cri

A da, muhimman kasashen da ke iya haka man fetur da gas su ne kasar Algeria, da Libya, da Masar da ke bakin tekun Med, da kuma kasar Nijeria, da Angolan, da Gabon, da Congo Brazzaville, wato sababbin kasashe masu fitar da man fetur da ke mashigin teku na Guinea. Amma, a cikin 'yan shekarun da suka wuce, yawan manyan kasashen Afrika masu fitar da man fetur a kudancin hamadan Sahara ya ribanya sau biyu. Yawan man fetur da aka fitar a kasar Equatorial Guinea, da Chadi, da Sudan, har ma Sao Tome and Principe, da Mauritania yana ta karuwa. A shekarar 2004, yawan man fetur da dukan Afrika ke fitar a ko wace rana ya kai ganguna miliyan 8, ya kusa da kashi 10 cikin dari bisa na dukan duniya. A cikin shekaru 10 masu zuwa, yawan man fetur da Afrika za ta fitar zai karu sosai, watakila yawan man fetur da za a fitar a ko wace rana zai kai ganguna miliyan 13.

Ganowar babban filin man fetur na kasar Nijeria da ke teku mai zurfi, ta sa bangarori masu kula da man fetur sun kara ba da shawarar kan haka filin man fetur na Sao Tome and Principe. Filin man fetur na mashigin teku na Guinea ya zama buri na bangarori dabam daban da suke neman haka man fetur, manyan filayen man fetur da ke tsakiyar Afrika sun zaman muhimman abubuwa na ayyukan haka man fetur na Afrika a yau. Filaye na kasar Chadi da Sudan suna da tsarin man fetur iri daya, wasu manyan kamfanonin man fetur sun riga sun fara ayyukan haka mai. Wannan ba kawai ba zai sa wadannan kasashe 2 su ci gaba da haka sababbin filayen man fetur a kewayen tsofaffin filayen man fetur, kuma zai inganta haka filayen man fetur na kasar Kameron wanda yawan fitar da man fetur dinta ya ragu a cikin 'yan shekarun da suka wuce. A cikin 'yan kwanakin da suka wuce, sakamakon neman man fetur a kasar Libya ya kuma karfafa zuciyar yin ayyukan haka man fetur.



Yawan man fetur da kasar Nijeria da Angola suka fitar yana ci gaba fiye da na sauran kasashen Afrika, a cikin shekaru 10 masu zuwa, watakila zai ribanya sau biyu. Yanzu, ana zuba jarin dollar Amurka ta biliyoyi kan manyan filayen man fetur da yawa na teku mai zurfi na kasar Angola da ke kudancin Afrika. A cikin shekaru 5 zuwa shekaru 7 nan gaba, yawan fitar da man fetur a ko wace rana na kasar Angola zai karu zuwa ganga miliyan 2 daga ganga miliyan 1 na yanzu. A shekarar 2010, watakila yawan fitar da man fetur na filayen teku mai zurfi, da na bakin teku a ko wace rana na kasar Nijeria zai kai ganga miliyan 4.

Ko shakka babu, babban farashin man fetur na yanzu ya inganta zuba jari kan man fetur. Ko da ya ke karuwar farashin man fetur a cikin gajeren lokacin ba zai kawo tasiri ga ayyukan haka da fitar da man fetur ba, amma a cikin shekaru biyu da suka wuce, musamman a karshen rabin shekarar da ta wuce, karuwar farashin man fetur sosai ta inganta ayyukan haka man fetur sosai. Sabo da wasu dalilai a cikin shekaru 30 da suka wuce, ba a haka filayen man fetur da yawa na Afrika ba. Yanzu, 'yan kasuwa sun fara mai da hankulansu kan wadannan filayen man fetur. Idan farashin man fetur zai ci gaba da kai matsayi na dollar Amurka 50 zuwa 60 a ko wace ganga, watakila za a haka wadannan kananan filayin man fetur da na teku mafi zurfi.

Aikace- aikacen haka mai a jere da aka yi a cikin shekaru 5 da wani abu da suka wuce sun nuna cewa, halin haka man fetur da gas na nan gaba a kudu maso gabashin Afrika yana da kyau.

An taba gane cewa, kasuwar gas ita ce karamar kasuwa, muhimman kasashe masu yi amfani da gas su ne kasar Korea ta kudu, da Japan, da kuma sauran kasashen da ke Asia ta gabas. Ko da ya ke nan gaba Asia za ta ci gaba da zama kasuwar yin amfani da gas da ta fi girma a duniya, amma Turai da Amurka ta arewa za su kara bukatunsu kan gas a hankali a hankali. Yawan kudin da za a samu wajen gas yana jawo hankulan manyan kamfanonin man fetur dabam daban da su shiga filin haka gas.

Kasar Nijeria ita ce babbar kasa ta Afrika wajen fitar da man fetur da gas. A da, kasar Nijeria da sauran manyan kasashe masu fitar da man fetur suna neman fitar da man fetur ne kawai, amma ba su mai da hankulansu kan ayyukan haka gas ba. Yanzu, kasar Nijeria ta fara yin amfani da albarkatun gas, kuma ta riga ta zama muhimmiyar kasa wajen ba da gas ga Turai. (Bilkisu)