Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-15 09:47:33    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(09/02-15/02)

cri
An bude wasannin Olympic na lokacin hunturu na karo na 20 a filin wasa na Olympic da ke birnin Turin na kasar Italiya a ran 10 ga wata. 'Yan wasa fiye da 2500 daga kasashe da yankuna 84 sun shiga manyan gasanni 9 don neman samun lambobin zinare 85. Kasar Sin ta aika da kungiyar wakilan 'yan wasanta mafi girma da ke kunshe da mambobi 151, wadanda suka yi kokarin samun lambobin zinare a cikin gasannin wasan gudun kankara na gajeren zango da wasan gudun kankara da wasan kankara na salo-salo da wasan skiing daga kan duwatsu tare da nuna fasaha da dai sauransu. An yi kwanaki 17 ana yin wannan wasanni, kuma za a rufe a ran 26 ga wata. A cikin gasar wasan gudun kankara na gajeren zango mai tsawon mita 1500 da aka yi tsakanin maza a ran 12 ga wata, dan wasan kasar Sin Li Jiajun ya sami lambar tagulla, wannan ne lamba ta farko da kasar Sin ta samu a wannan gami.

A gun cikakken taro na karo na 118 da kwamitin wasan Olympic na duniya ya rufe a birnin Turin a kwanan baya, a galibi dai kwamitin ya zartas da shirin da kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya bayar game da aikin bai wa juna wutar yula ta wasannin Olympic na shekarar 2008. Bayan da aka zartas da wannan shiri, kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing zai yi daidaitawa ta hanyar tattaunawa da kasashe da yankuna a jere, inda za a tafiyar da aikin bai wa juna wutar yula, kuma zai gabatar da shiri na karshe a shekarar 2007 mai zuwa.

Ban da wannan kuma, akwai wani labari daban da aka bayar daga birnin Turin, an ce, kakakin kwamitin wasannin Olympic na duniya Mr. Giselle Davies ya bayyana a kwanan baya cewa, kwamitin ya tsai da kudurin shirya wani dandalin wasan Olympic da ya shafi motsa jiki da aikin ba da ilmi da kuma al'adu a nan Beijing a watan Oktoba na shekarar da muke ciki. Mr. Davies ya kara da cewa, dandalin nan zai hada da motsa jiki da aikin ba da ilmi gaba daya, a gun taron dandalin, za a kuma yi tattaunawa kan yadda za a sa matasa su shiga cikin wasannin motsa jiki.

An yi karon karshe na gasar cin kofin Afirka ta wasan kwallon kafa ta shekarar 2006 a birnin Alkahira na kasar Masar a ran 10 ga wata, kungiyoyin kasashen Masar da Cote d'Ivoire sun yi kunnen doki, ba kore bin damo a cikin mintoci 120, a cikin gasar fanareti da suka yi, kungiyar kasar Masar ta lashe kungiyar kasar Cote d'Ivoire da ci 4 da 2, wato ta zama zakara na karo na 5. An bude wannan gasa a ran 20 ga watan jiya, inda kungiyoyi 16 suka yi takara da juna.

Wani jami'in wasannin motsa jiki na kasar Afirka ta Kudu ya bayyana a birnin Capetown na kasar a kwanan baya cewa, gwamnatin kasar Afirka ta Kudu da Hadaddiyar Kungiyar Wasan Kwallon Kafa ta Duniya wato FIFA sun riga sun sami ra'ayi daya kan filayen wasan da za a yi amfani da su a cikin gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta shekarar 2010, kasar Afirka ta Kudu za ta bayar da filayen wasa guda 10, a ciki har da sabbi guda 5. A watan Mayu na shekarar 2004 da ta gabata, kungiyar FIFA ta tabbatar da kasar Afirka ta Kudu da ta shirya gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa a shekarar 2010, wannan ne karo na farko da za a yi wannan muhimmin gasa a Afirka.

An kammala gasar wasan kwallon tennis tsakanin mata biyu biyu a birnin Pattaya na kasar Thailand a ran 12 ga wata. 'Yan wasan kasar Sin Li Ting da Sun Tiantian, zakaru na wasannin Olympic na Athens, sun lashe abokansu Zheng Jie da Yanzi da ci 2 da 1, sun zama zakaru.(Tasallah)