Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-13 16:30:45    
Farin ciki da jin labarin "kauyen Zhenghe" a kasar Afrika ta Kudu

cri
Bisa labarin da wakilin Kamfanin Dillancin Labaru na Xinhua ya samu daga Malam Liu Guijing, jakadan kasar Sin da ke wakilci a kasar Afrika ta Kudu a farkon watan Afrilu na shekarar bara, an ce, akwai wani kauye da ake kira "Zhenghe" a kasar Afrika ta kudu. A watan Febrairu na shekarar bara, wato yayin da jakada Liu Guijing ke halartar bikin bude taron majalisar dokoki ta kasar Afrika ta Kudu, wani Ba'afrike dan majalisar ya yi farin ciki da gaya masa cewa, ya kasance da wani kauye mai suna "Zhenghe" a wani wuri da ke da nisan misalin kilomita 80 daga tashar jiragen ruwa ta Elizabeth ta kasar Afrika ta Kudu. Manoman kauyen nan su bakaken fata ne, amma ba bakake sosai ba, gashinsu dogo ne, wato kamanninsu ya tashi kusan daya da na Sinawa, haka nan kuma an ce, ya zuwa yanzu dai suna zaman rayuwarsu bisa al'adar Sinawa.

Da wannan wakilin Kamfanin Dillancin labaru na Xinhua ya yi farin ciki da jin wannan labari daga wajen bakin jakada Liu Guijing, sai ya dau niyyar kai ziyara a kauyen "Zhenghe" don neman labaru. Don neman sanin inda kauyen nan yake sosai, ya sha kai ziyarar ban girma ga wasu Sinawa tsoffafi da ke zama a kasar Afrika ta Kudu. A kan kasa Sinawa a kasar Afrika ta Kudu zuwa gidaje biyu wato sabbi da tsoffi. Tsoffin Sinawa da ke zaune a kasar Afrika ta Kudu jikokin Sinawa ne da suka fara zuwa kasar Afrika ta Kudu yau sama da shekaru 100 da suka wuce. A hakika dai, bisa abubuwa da aka rubuta a cikin littafin tarihi, an ce, Sinawa na rukuni na farko sun sauka a kasar Afrika ta Kudu ne a shekarar 1685. A wancan zamani, wato lokacin da kamfanin gabashin Indiya ta kasar Netherlands ya kafa sansaninsa a kasar Afrika ta Kudu, ya yi karanicin kwadago, sabo da haka ya yi jigilar masu laifuffuka dubbai daga Indonesiya zuwa kasar Afrika ta Kudu wadanda suka hada da wasu Sinawa. Daga karshe, yawancin wadannan Sinawa ba su sami damar komawa gida ba domin rashin biyan bashi da ake binsu, ta haka sun zama rukunin Sinawa na farko da suka fara zama a kasar Afrika ta Kudu.

Zuwa farkon karni na 19, mutanen Britaniya sun maye gurbin mutanen kasar Netherlands sun mallaki yankin Cape Town. Yawan Sinawa da suka yi zama a kasar Afrika ta Kudu bai wuce 100 ba a wancen zamani. Amma da hukumar mulkin mallaka ta Britaniya take matukar bukatar 'yan kwadago masu rahusa don yin gine-gine, sai ta shigar da 'yan kwadago masu fasaha da yawansu ya kai kamanin 50 daga lardin Guangdong na kasar Sin.

Haka zalika bayan da aka gano lu'ulu'u da ma'adinan zinariya a kasar Afrika ta Kudu a shekarar 1867 da ta 1886, dimbin masu neman arziki ciki har da wasu Sinawa sun runtuma zuwa kasar Afrika ta Kudu daga wurare daban daban na duniya. Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka yi, an ce, yawan Sinawa wadanda suka sauka kasar Afrika ta Kudu ta hanyar kasar Mauritius ya kai misalin 1800 a tsakanin shekarar 1888 zuwa ta 1898. Yanzu, yawancin jikokin wadannan Sinawa suna zaune a birnin Johannesburg mai arzikin zinariya da birnin Pretorina, hedkwatar mulki ta kasar da tsahar jiragen ruwa ta Elizabeth da birnin Eastern London da birnin Cape Town da kuma sauran birane tashoshin jiragen ruwa.

A lokacin da ake gudanar da akidar wariyar launin fata a kasar Afrika ta Kudu, daidai kamar sauran mutanen Asiya da Afrikawa, wadannan Sinawa su ma sun dandana wahalhalu sosai a karkashin mulkin Turawa mai bin akidar wariyar launin fata.

Amma tun bayan kafuwar sabuwar kasar Afrika ta Kudu, musamman bayan da aka kulla huldar diplomasiya a tsakanin Sin da kasar Afrika ta Kudu a shekarar 1998, an yi ta bunkasa dangantakar aminci da ke tsakanin kasashen biyu, yawan Sinawa da ke zaune a kasar nan ma ya karu da sauri, matsayinsu ma ya yi ta daguwa a kasar Afrika ta Kudu.

Bayan bazuwar labarin nan dangane da "kauyen Zhenghe", duk Sinawa da ke zama a kasar Afrika ta Kudu sun ji matukar farin ciki, suna ta namen karin labarin daga wajen tsoffi Sinawa da ke zaune a tashar jiragen ruwa ta Elizabeth da birnin Eastern London.

Daga karin labaru da aka samu dangane da "kauyen Zhenghe", an kimanta cewa, ko da yake ya zuwa yanzu ba a san inda kauyen nan yake ba, amma an amince da cewa, ya kasance da kauyen nan a kasar Afrika ta Kudu. (Halilu)