Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-10 16:49:59    
Abubuwan fatan alheri na wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing yana kawo mana damar kasuwanci

cri

Jama'a masu karatu, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Bunkasuwar kasar Sin. A watan Nuwamba na shekara ta 2005, an bayar da abun fatan alheri na wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing, wato Fuwa a Sinanci. Ma'anar Fuwa a harshen Sinanci ita ce jariran da ke kawo mana fatan alheri. Yanzu ana sayar da zane-zanen wadannan jariran fatan alheri sosai a manyan biranen kasar Sin. Masana sun yi hasashen cewa, moriyar da abubuwan fatan alheri irin na Fuwa za su kawo kasar Sin za ta kai kudin dalar Amurka wajen miliyan daruruwa.

A wani kantin da ya samu izinin sayar da kayayyakin wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing, wakilinmu ya ga mutane da yawa suna ribibin sayen abubuwan wasa na Fuwa. Mr. Lu Lin yana da sa'a ya saye abubuwan wasa na Fuwa wadanda su ne na karshe da kantin ke sayarwa a wannan rana. Mr. Lu ya ce, "Na riga na sayi abubuwan wasa na Fuwa duka saiti guda. Amma abokai wadanda suke da zama a wani birni daban sun roke mu da mu sayo musu abubuwan wasa na Fuwa wato saiti guda. Sabo da haka, na zo na saya domin zan je birninsu."

Abubuwan wasa na Fuwa suna kunshe da jarirai guda 5, wato Beibei da Jingjing da Huanhuan da Yingying kuma da Nini. Abin wasa na Beibei ya yi kama da wani kifi, abin wasa na Jingjing ya yi kama da wani Panda, Huanhuan ya yi kama da wutar yola ta Olympic, Yingying kuma ya yi kama da barewa irin ta Tibet. Ningning kuma ya yi kama da wani tsuntsu, wato swallow a Turance. Idan an hada sunayensu za a iya karanta su Beijing Huan Ying Ning a harshen Sinanci, wato barka da zuwa Beijing a cikin Hausa.

Yanzu da akwai manyan kantuna 28 tare da kananan kantuna fiye da 160 wadanda suka samu izinin sayar da kayayyakin wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing a duk fadin kasar Sin. A manyan biranen kasar Sin, kamar a Beijing da Shanghai da Qingdao da Nanjing da Chengdu za a iya sayen jerin kayayyakin wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing.

Mr. Lu Dongbing, kwamishinan kwamitin tsara shirin raya tattalin arzikin wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing kuma shehun malamin jami'ar jama'a ta kasar Sin ya yi hasashen cewa, darajar jerin kayayyakin wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing zai ta kai dalar Amurka fiye da miliyan dari 3.

"Yaya aka cimma wannan kididdiga ta dalar Amurka miliyan dari 3? Yawan kudaden da aka samu domin sayar da jerin abubuwan fatan alheri na wasannin motsa jiki na Olympic na Sydney bai kai dalar Amurka miliyan dari 3 ba. Amma a kasuwar kasar Sin, yawan masu yawon shakatawa na ketare ya wuce adadin da muka yi hasashe a da. Idan an hada su da masu yawon shakatawa na Sinawa, kasuwarmu ta fi ta Sydney girma. Sabo da haka, na yi hasashen cewa, yawan kudaden da za a samu domin sayar da jerin abubuwan fatan alheri na Fuwa zai kai fiye da miliyan dari 3."

Mr. Lu ya kuma bayyana cewa, wannan adadi shi ne moriyar da za a samu domin sayar da jerin abubuwan fatan alheri na Fuwa kawai, bai kunshi boyayyen moriyar da za a samu daga sana'ar yin abubuwan fatan alheri na Fuwa ba. Sabo da haka, wakilinmu ya kai ziyarar musamman ga wata masana'antar da ake yin kayayyakin wasa na Fuwa. A cikin wannan masana'antar, kowane layi yana aiki. Amma har yanzu, yawan kayayyakin wasa na Fuwa bai yi yawa ba, ba su iya biyan bukatar da ake nema a kasuwa ba. Wata ma'aikatar wannan masana'anta mai suna Wang Hong ta bayyana wa wakilinmu dalilin da ya sa ba su iya yin kayayyakin wasa na Fuwa da yawa a kowace rana ba. Aikin yin kayan wasa na Fuwa yana sarkakiya sosai. Daga cikin wannan aiki, an fi shan wuyar yin kawunan Fuwa.

"Mun fi shan wuyar yin wutar yola ta Olympic ta kawunan kayan wasa na Huanhuan. A kowace rana, kowanenmu yana iya yin kawunan kayan wasa na Huanhuan guda 18 kawai."

A karshe dai, shugaban wannan masana'anta bai gaya wa wakilinmu yawan kayayyakin wasa na Fuwa da ake yi a kowace rana ba kuma da moriyar da wannan masana'anta ke samu ba. Amma domin wannan masana'anta tana shan aiki sosai, za a iya sanin cewa ba za a iya kyale moriyar da wannan masana'anta ke samu ba.

Wakilinmu ya kuma samu labaru cewa, bayan an bayar da kayan wasa na fatan alheri na Fuwa, kowa yana mai da hankali kan yadda za a samu izinin kerawa kuma da yin jerin kayayyakin wasan fatan alheri na Fuwa. Yanzu, kwamitin shirya wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing ya riga ya dauki matakan shari'a domin kare ikon mallakar fasahar kayan wasa na Fuwa da kara raya kasuwar nazari da kera kuma da sayar da jerin kayan wasa na Fuwa. Hukumomin kare shari'a na kasar Sin suna kuma daukar matakai iri iri domin fama da yunkurin satar fasahar kayan wasa na Fuwa.(Sanusi Chen)