Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-09 16:58:56    
An fara taron bangarorin da suka kulla "Yarjejeniyar ka'idojin kayyade taba sigari"

cri
Jama'a masu karatu, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Duniya ina Labari. Tun daga ran 6 zuwa ran 17 ga wata, ana yin taron bangarorin da suka kulla "Yarjejeniyar ka'idojin kayyade taba sigari" a birnin Geneva. "Yarjejeniyar ka'idojin kayyade taba sigari" yarjejeniyar farko ce game da aikin kiwon lafiya, tana kuma da muhimmanci kwarai a cikin tarihin kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa. Kan yadda za a aiwatar da wannan yarjejeniyar, wani muhimmin batu ne da ke kasancewa a gaban wakilan kasashe 110 wadanda suke halartar taron.

An fara yin shawarwari ne tun daga watan Oktoba na shekarar 1999 game da yarjejeniyar. A ran 21 ga watan Mayu na shekara ta 2003, daga karshe dai, membobi 192 na kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa sun sami ra'ayi daya kan takardar karshe ta yarjejeniyar. Bayan da membobi 40 na kungiyar suka amince da yarjejeniyar, yarjejeniyar ta fara aiki tun daga ran 27 ga watan Fabrairu na shekara ta 2005. Bisa shirin da aka tsara, ya kamata a yi taron bangarorin da suka kulla yarjejeniyar a cikin shekara 1 bayan yarjejeniyar ta fara aiki.

Wakilai wadanda suka hallara a gun taron sun bayyana yadda kasashensu suke daukan matakan kayyade taba sigari a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce. A kasashen Ireland da Spain da kasar Norway, an riga an hana shan taba a rufaffun wurare. A kasar Indiya kuwa, an riga an tsara jerin dokoki domin hana yin tallace-tallacen sayar da taba a kasar.

Mr. Sha Zukang, wakilin kasar Sin wanda yake halartar taron, ya bayyana cewa, an riga an sami hakikanan cigaba wajen kayyade taba a kasar Sin. Bi da bi ne kasar Sin ta bayar da jerin dokoki ciki har da "Dokar musamman ta cinikin taba" da "Dokar Talla" da "Dokar kiyaye yara", wadanda suke kunshe da kashin kayyade taba sigari. Sannan kuma, a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, hukumomin gwamnatin kasar Sin da abin ya shafa sun dauki matakan kara karfin kayyade taba sigari. An kuma fara aikin kafa da kuma amince da wuraren hana shan taba sigari da hukumomin hana shan taba sigari a harabobinsu da biranen babu tallar taba sigari. Haka nan kuma, an yi yaki da haramtaccen yunkuri na yin cinikin taba sosai, kuma ana hana sayar wa yara taba a nan kasar Sin. Bugu da kari kuma, yanzu gwamnatin kasar Sin tana kokari kan yadda za a iya shirya wasannin motsa jiki na Olympic na shekara ta 2008 da za a yi a nan birnin Beijing ba tare da sha taba ba.

Amma mahalarta taron suna ganin cewa, "yarjejeniyar ka'idojin kayyade taba sigari" wata yarjejeniyar da ke bayyana ka'idojin da ya kamata a bi ne kawai. Haifar da ita alamar kaddamar da aikin kayyade taba sigari ke nan, dole ne a kara tsara sharadu filla filla a nan gaba domin kayyade sha da sayar da taba sigari. Alal misali, ba a tsara sharuda filla filla kan yadda za a iya yin yaki da haramtaccen yunkurin yin cinikin taba sigari ba. Ban da wannan kuma, babu sharadan kayyade yin tallar taba sigari a tsakanin kasa da kasa a cikin yarjejeniyar. Sabo da haka, mahalarta suna fatan za a tsara "Takardar yin yaki da haramtaccen yunkurin yin cinikin taba sigari" da "Takarda game da tallar taba sigari da ake yi a tsakanin kasa da kasa". Ofishin sakatariyar kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa ya bayar da labari cewa, an riga an sa aikin tsara wadannan takardu biyu a cikin ajandar kungiyar. Bugu da kari kuma, a gun taron, za a tattauna maganar yadda za a samar wa kasashe masu tasowa taimakon kudi domin nuna musu goyon baya wajen aiwatar da yarjejeniyar. Sannan kuma, kafin watan Fabrairu na shekara ta 2007, bangarorin da suka kulla yarjejeniyar za su gabatar da rahotanninsu, inda za su bayar da matakan da suke dauka wajen aiwatar da yarjejeniyar.

A gun taron, Dr. Lee Jong-wook, babban direktan kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa ya nuna cewa, yanzu mafi yawancin mutane sun riga sun amince da wannan magana, wato shan taba barazanar farko ce ga lafiyar jama'a. Idan za a iya aiwatar da "Yarjejeniyar ka'idojin kayyade taba" da kyau, to, kafin shekara ta 2050, mai yiyuwa ne za a iya ceton mutane miliyan dari 2. Ya zuwa lokacin can, "za a iya canja tarihi", in ji Lee Jong-wook. (Sanusi Chen)