Cikin wata takardar da kwamitin sa ido kan dukiyoyin gwamnatin kasa na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar kwanan baya an tsai da cewa, za a yarda da manyan masana'antun gwamnatinta da su sauya ikon mallakar hannun jari ga manyan jami'an da ke tafiyar da harkokinsu ta hanyar kara sayar da hannun jari da yawa, wannan ya zama sabon matakin da kasar Sin ta dauka domin kyautata sha'anin sauyawar ikon mallakar hannun jari ga wadannan manyan masana'antun gwamnatin da ke sayar da hannun jari. To me ya sa aka kaddamar da wannan mataki? Jama'a masu sauraro yanzu za mu yi muku bayani don ba da amsa ga wannan tambaya.
A shekarar 2003, kasar Sin ta taba tsai da dokoki kan maganar sauya ikon mallakar hannun jari na manyan masana'antun gwamnatin kasar, tana fatan ta wannan hanya ce za a tabbatar da samun ikon mallakar hannun jari a fannoni da yawa da sa kaimi ga kafa tsarin kayyade wadannan masana'antu wajen sayar da hannun jari, da kuma kara karfin yin gasa a tsakaninsu. Amma a lokacin da ake aiwatar da wadannan dokoki, wasu manyan jami'an masana'antun sun sayar da hannun jarinsu da araha domin kwace dokiyoyin gwamnati, sabo da haka a wata Afirlu na shekarar 2005, kwamitin sa ido kan dukiyoyin gwamnatin kasa na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya sanar da cewa, an hana manyan masana'antun gwamnatin kasar da su sayar da hannun jari ga manyan jami'ansu.
A wannan gami wato bayan lokacin da bai wuce shekara daya baya, kwamitin sa ido na dukiyoyin gwamnatin kasa ya kaddamar da sabbin dokoki wato an yarda da cewar manyan masana'antun gwamnatinta da suna da ikon mallakar hannun jari ta hanyar kara sayar da hannun jari da yawa. Mr. Li Rongrong, direktan kwamitin sa ido na dukiyoyin gwamnatin kasar Sin ya yi bayani a kan wannan cewa, "Mun riga mun kyautata tsarin dokokin da abin ya shafa, kuma mun tsai da dokokin sauyawar ikon mallakar dukiyoyin gwamnati da kara sa ido bisa wannan harsashi."
Bayan da aka kaddamar da wadannan sabbin dokoki, an jawo gardama a tsakanin sana'ar hannun jari da sassan masanan ilmi. Farfesa Zhao Xijun da ke aiki a ofishin binciken sha'anin kudi da hada-hadar kudi na jami'ar jama'ar kasar Sin ya bayyana cewa, "Bisa halin da ake ciki na gwamnatin kasar wadda take tsaye kan muhimmin matsayi wajen mallakar hannun jari, ya kamata a samu dabarar yin jarrabawa ta hannyar kimiyya ga manyan jami'an masana'antun gwamnatin kasar kan yawan nasarorin da suka samu ba domin manufofin kasa ba amma ta hanyar yin kokari su da kansu."
Yanzu kasar Sin tana da manyan masana'antun gwamnati 169, wadanda jimlar kudin da suke mallaka ta kai Renminbi wato kudin Sin fiye da Yuan biliyan dubu 10. Mr. Li Rongrong, direktan kwamitin sa ido na dukiyoyin gwamnatin kasar Sin ya yi bayani a kan wannan cewa, "Wadannan matakan sa kaimi da aka dauka suna da amafni a wani fanni, a wani fanni daban kuma ba su da amfani. Ya kamata a aiwatar da wadannan matakai yadda ya kamata, kasashe daban-daban sun sha bamban wajen tafiyar da irin wadannan matakai. Kuma ya kamata mu yi kokarin hana bullowar abubuwa marsa kyau, sabo da haka da farko ya kamata mu yi gwajin aiki wajen tafiyar da irin wadannan matakai." (Umaru)
|