Ga wani labarin da wakilin rediyon kasar Sin ya rubuto mana ya bayyana cewa, a ran 2 ga watan nan d muke ciki,bayan rutsewar jirgin ruwa mai dauke da fasinjoji mai lambar "98 na zaman lafiya" na kasar Massar, har zuwa ran 4 ga watan, yawan mutanen da suka sami ceto sun kai fiye da 400. Ban da haka kuma, yawan gawawaki da masu ceto suka gano sun kai fiye da 200. Amma har yanzu dai yawan mutanen da suka bace sun kai kusan 800. Kwararru sun kimanta cewa, yawan mutanen da suka rasu cikin wannan hadari sun kai kusan dubu.
A game da dalilin da ya sa an yi sanadiyar mutuwa da yawa haka da aukuwar rutsewar wannan jirgin ruwa, har yanzu dai sashen hukuma na kasar Massar bai bayyana sakamakon da aka yi bincike ba tukuna.
A ran 4 ga watan nan da muke ciki, Mr.Mubarak shugaban kasar Massar ya je birnin Hurghada hedkwatar lardin Red Sea don nuna jejjeto ga masu ji rauni da saurari rahoton da aka yi bincike kan hadarin nan. Shugaban ofishin kula da zirga zirga na kasar Massar ya bayyana cewa, wani mataimakin matukin jirgin ruwa mai dauke da fasinjoji wanda ya ji rauni cikin wannan hadari ya fadi cewa, bayan da wannan jirgin ruwa mai dauke da fasinjoji ya tashi daga tashar jirgin ruwa ba da dadewa ba sai wani mota mai dauke da kayayyaki da yawa dake kan wannan jirgin ruwa ya ci gobara, da farko an kashe gobara, sai matukin jirgin ruwan nan ya ba da umurni ga ci gaba da tafiyar wannan jirgin ruwa, amma jim kadan, wannan mota ya sake ci gabara sabo da babbar iska ta tashi sai wannan gobara ta harbe wurare da yawa na wannan jirgin ruwa, ba da dadewa ba, wannan jirgin ruwa ya fara rutsewa, a karshe dai wannan jirgin ruwa ya nutsu cikin ruwa.
Ban da haka kuma, wadansu kwararru masu ilmin ruwan teku sun bayyana cewa, wannan jirgin ruwa mai dauke da fasinjoji da aka kera ya kai shekaru 35, ko da yake an riga an yi gyare gyare ga wannan jirgin ruwa, har an sa yawan fasinjojin da wannan jirgin ruwa ya iya daukawa sun karu daga 500 zuwa l400, amma bayan da an yi wannan gyare gyare, sai an kawo tasiri ga lafiyar tafiye tafiye na wannan jirgin ruwa.Kuma a cikin wannan jirgin ruwa an aza motoci da yawa sosai, in ba a zaunar da wandannan motoci da kyau ba, sai an kawo tasiri ga lafiyar jirgin ruwan nan sosai da sosai.
Ban da haka kuma, a lokacin da faruwar wannan hadari, masu aiki na wannan jirgin ruwa ba su bayyana hakikanin hali na wannan hadari ba, sai fasinjoji sun ji tsoro sun yi ta cukunshe sosai. Amma masu aiki na wannan jirgin ruwa ba su kula da lafiyar fasinjoji, wadansu su kansu sun gudu tare da kananan jiragen ruwa masu yin ceto.
Wani dalili daban shi ne sashen watsa labaru na kasar Masar ba su sami labarin nan cikin lokci, domin a lokacin da tashin gobarar nan, sai wuta ta lahanta hanyoyin zirga zirga na wannan jirgin ruwa, har ba a bayar da rokon neman ceto ba.
Ban da haka kuma, wani dalilin daban shi ne wurin aukuwar hadarin nan ya yi nesa da yankin kasar, ba a iya dauki dabara yin ceto ga fasinjoji.(Dije)
|