Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-07 18:25:10    
Har yanzu dai akwai kafar tattaunawa a kan batun nukiliya na Iran

cri
Bayan da kwamitin daraktocin hukumar makamashin nukiliya ta duniya ya zartas da kuduri dangane da mika batun nukiliya na Iran ga kwamitin sulhu na MDD a ran 4 ga wata, kashegari a ran 5 ga wata, hukumomin da abin ya shafa na Iran sun yi shelar daina daukar dukan matakan hadin gwiwa tun daga ran nan, kuma ba za su amince da binciken da hukumar makamashin nukiliya ta duniya ke iya yi wa na'urorinta na nukiliya ba zato ba tsammani ba. Lalle ne, da wuya a tsinkayi makomar maganar nukiliya ta Iran. Amma duk da haka, masana suna ganin cewa, bisa bayanin da bangarori daban daban suka yi da kuma babbar moriyarsu, muna iya gane cewa, akwai kafar ci gaba da yin shawarwari a kan batun.

Ministan harkokin waje na Iran Manouchehr Mottaki ya shelanta a ran 5 ga wata cewa, a ran nan, Iran ta riga ta dakatar da dukan matakan hadin gwiwa da ta shafe shekaru biyu tana dauka bisa son ranta don neman kulla aminci a kan batun nukiliya. A ran nan kuma, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Iran Hamid Reza Assefi ya bayyana cewa, tilas ne gwamnati ta aiwatar da dokokin da abin ya shafa wadanda majalisar dokoki ta zartas a karshen shekarar bara, wato a soke wadannan matakai. Amma a sa'i daya kuma, ya ce, Iran za ta ci gaba da hada gwiwa da hukumar makamashin nukiliya ta duniya bisa tsarin yarjejeniyar hana habaka makaman nukiliya, kuma tana ci gaba da tsayawa tsayin daka a kan daidaita batun nukiliya na Iran ta hanyar shawarwari, 'har zuwa yanzu kofar shawarwari a bude take'. Ya kuma kara da cewa, Iran tana shirin ci gaba da yin shawarwari tare da Rasha a kan shirin da ta gabatar, don ci gaba da neman warware matsalar nukiliya ta Iran ta hanyar shawarwari.

Sakamakon kudurin hukumar makamashin nukiliya ta duniya, Iran tana fuskantar wani zabi mai wuya, wato yaya za ta kiyaye halalen ikonta a yayin da ba ta kai ruwa rana da gamayyar kasa da kasa ba. A hannu daya, matsalolin hauhawar farashin kaya da rashin samun aikin yi babban nauyi ne da ke bisa wuyan Iran, kamfanonin man fetur na kasashen waje da kasuwannin jari na duniya ne suke bayar da makudan kudade ga Iran wajen yin gyare-gyare a kasar, idan kakaba mata takunkumi ya zama gaskiya a wata rana, to, tattalin arzikinta zai kara tabarbarewa.

A hannu dayan kuma, masana sun yi nazari cewa, daga tace sinadarin uranium zuwa sarrafa cikakkun fasahohin nukiliya hanya ce mai tsawo wadda ke kunshe da matakai da dama, a ko wane mataki kuma, ba ma kawai za a warware matsalolin da za a samu a fannin fasaha ba, haka kuma wajibi ne tsara manufar siyasa kamar yadda ya kamata. Idan Iran ba ta janye jiki daga yarjejeniyar hana habaka makaman nukiliya ba, to, hukumar makamashin nukiliya ta duniya za ta ci gaba da sa ido a kan muhimman ayyukanta na nukiliya, a cikin irin wannan hali, da kyar ta iya aiwatar da shirin nukiliya ta wata hanya daban bayan amfanin jama'a. Amma idan Iran ta yi gaban kanta, to, za ta sha hasara sosai daga hadarin siyasa, kuma mai yiwuwa ne ba za ta cimma burinta ba daga karshe.

A ganin kasashen yammacin duniya ma, har ila yau, shawarwari yana ci gaba da zama hanya mafi kyau wajen daidaita batun nukiliya na Iran. Idan an kakaba wa Iran takunkumi, to, dukan bangarorin biyu za su ji jiki tare. Idan Iran ta yi amfani da man fetur dinta, to, ba sai kawai gamayyar Turai za ta sha hasara sosai a moriyarta a Iran ba, har ma abin zai kai babban naushi ga farashin man fetur a kasuwannin duniya. Ban da wannan kuma, mai yiwuwa ne takunkumin zai karfafa niyyar Iran a wajen bunkasa nukiliya, a lokacin, za a rasa abin da za a yi a kan batun nukiliya na Iran, har ma zai shafi halin da gabas ta tsakiya ke ciki baki daya, wannan kuma ya zama abin da tilas ne Amurka da gamayyar Turai su yi la'akari da shi. Sabo da haka ne ma, kasashen yammacin duniya da suka hada da Amurka da Birtaniya su ma sun yi ta bayanin cewa, ko da yake hukumar makamashin nukiliya ta duniya ta tsai da kuduri, amma ba a rufe kofar daidaita batun ta hanyar diplomasiyya ba tukuna.(Lubabatu Lei)