Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-07 10:28:41    
Birnin Beijing yana sa himma a wajen shirya Wasan Olympic na gajiyayyu a shekarar 2008

cri

Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , A shekarar 2008 birnin Beijing ba kawai zai shirya wasan Olympic na yanayin zafi na 29 ba har ma zai shirya wasan Olympic na gajiyayyu. Gwamnatin birnin Beijing da Kwamitin shirya wasan Olympic na Beijing suna mai da muhimmanci sosai kan aikin shirya wasan gajiyayyu . A cikin shekarar da ta shige , an yi wasu aikace-aikace cikin tsanaki kuma za a dauki matakai masu yawa a cikin sabuwar shekara don kai aikin hidima mai kyau ga 'yan wasa gajiyayyu da masu yawon shakatawa . Shekarar 2006 shekarar kare ce ta kalandar gargajiyar Sinawa . A birnin Dalian dake gabar tekun arewacin kasar Sin akwai wani sansanin horad da karnuka masu ba da taimako ga makafi . A lokacin da a nan kasar Sin an shigo da wasu karnuka masu ba da taimako ga makafi amma ba yawa sosai . Tun daga shekarar 2005 , bisa rokon da gwamnatin birnin Beijing ta yi, Cibiyar gwajin dabobbi ta Jami'ar likitanci ta Dalian ta fara aikin horad da karnuka masu ba da taimako ga makafi . An kimanta cewa , bayan da za a yi aiki cikin shekaru 2 , a wannan shekara ko shekara mai zuwa , karnukan za su zama karo na farko masu ba da jagoranci ga 'yan wasa gajiyayyu . Wadannan karnukan za su jagoranci 'yan wasa makafi a bikin bude wasanin Olympic na shekarar 2008 . Madam Song Yanan , mai nazari na sansanin horad da karnuka masu ba da taimako na Dalian Ta gaya wa wakilin rediyonmu cewa , yanzu muna da wannan shirin . Muna fatan zamu iya aikin ba da hidima ga 'yan wasa makafi a wasan Olympic na Beijing a shekarar 2008.

Domin mai da 'yan wasa makafi su iya samun aikin hidima mai kyau a gun Wasanin Olympic na Beijing , gwamnatin birnin Beijing da Kwamitin shirya wasan na Beijing da Hadaddiyar Kungiyar nakasassu ta kasar Sin sun yi ayyukan share fage mai yawa a cikin shekarar da ta wuce . A cikinsu sun gina ayyuka marasa Katanga kuma sun sami yabo sosai daga Babbar Kungiyar nakasassu ta Duniya . Kayayyaki marasa Katanga za su ba da sauki ga gajiyayyu don tabbatar da kwanciyar hankali da zaman lafiyarsu .

Don shirya wasan Olympic na gajiyayyu na Beijing mai kyau , Kwamitin shirya wasan Olympic na Beijing ya kafa ofishin kula da harkokin gajiyayyu a shekarar bara . A karshen rabin shekara , kwamitin ya fara karbar masu son ba da taimako ga Olympic , kuma ya sami martani mai kyau daga jama'a farar hula na Beijing . Kwamitin zai karbi ma'aikata masu ba da rai ga 'yan wasa nakasassu dubu 30 . Su ma za su koyi ilmin musamman kan gajiyayyu kuma za su iya yi maganar hannu .

To, jama'a masu karatun shafinmu , shirin "Duniya ina labari " da za mu iya kawo muku ke nan a yau . Ado ne ya fasara wannan bayanin . Da haka muke muku sallama tare da fatan alheri .(Ado )