Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-06 15:51:41    
Mu'amala da hadin kai tsakanin Sin da Amurka a fannin ilimi suna samun habaka

cri

Sin kasa ce mafi girma daga cikin kasashe matasa na duniya, Amurka kasa ce mafi girma daga cikin kasashe masu cigaban masana'antu.Kasashen nan biyu suna hada kansu a fannoni da dama.A cikin shirinmu na yau,za mu karanta muku wani bayani kan yadda kasar Sin da Amurka suke hada kansu a fannin ilimi.

Yau shekaru 8 ke nan da jami'ar Qinghua,mashahuriyar jami'a ta kasar Sin ta soma hada kanta da jamo'ar Harvard ta Amurka.suna hadin kai a wajen kaddamar da shirye-shiryen koyar da sinanci a Jami'ar Qinghua,ana koyar da sinanci ga Amurkawa.Mataimakin shugaban cibiyar koyar da sinanci ga baki ta jami'ar nan Mista Ding Xia ya gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa "daliban ajinmu sun zo daga fannoni daban daban na Amurka,wannan yashaida cigaban dangantaka tsakanin kasar Sin da Amurka.A farkon lokacin da aka fara koyar da sinanci,yawancin dalibai 'yan diplomasiya ko masana ilimi ne musamman wadanda suka dukufa wajen nazarin harkokin Sin da na Asiya ta gabas da wasu jami'an diplomasiya.amma a yanzu ban da'yan diplomasiya da masana ilimi,da akwai ma'aikatan manyan kamfanoni da 'yan jaridu.Ga shi yanzu dailbai a zangon karattu daya ya kai 40 ko 50,tsawon lokacin karatu ya sha banban daga watanni uku zuwa rabin shekara."

Hadin kai wajen koyar da harshe wani muhimmin kashi ne na mu'amala da hadin kaitsakanin Sin da Amurka a fannin ilimi.Bisa labarin da aka samo,an ce ban da koyar da sinanci a gida,kasar Sin ta kuma tura malaman koyarwa 20 zuwa 30 zuwa kasar Amurka a shekarun baya.Ma'aikatun uilimi na kasar Sin da Amurka sun kaddamar da shirin koyar da harsuna ta hanyoyin sadarwa domin ba da taimako ga makarantun sakandare da firamare.Littattafan da aka wallafa cikin shirye-shiryen nan ya samu karbabuwa kimanin dalibai dubu 15 daga jihohi 20 na Amurka,haka kuma sun sami maraba sosai.

Tare da karin cigaban mu'amala tsakanin Sin da Amurka a fannin ilimi,manyan makarantu da damana kasar Sin sun kulla huldar cudanya tsakaninsu da jami'o'in Amurka.Hadin kai na samun bunkasuwa daga musayar ilimi zuwa binciken ilimi da kafa makarantu tare cikin hadin kai.He li daliba ce ta aji na hudu na kolejin koyon iliminkudade na jami'ar jama'ar kasar Sin.Ta yi farin ciki da samun damar yin jarrabawa,idan ta ci za ta iya samun damar karatu a jami'ar Columbia ta kasar Amurka bisa shrin da aka kaddamar da shi tsakanin jami'o'in nan biyu dangane da samar da ilimin tattalin arziki da kudade.Yanzu a shirye take tana neman cin jarabawa a fannin nan.Malama Heli ta gaya wa wakilinmu cewa Amurka tana kan matsayin gaba a duniya wajen tattalin arziki,tunaninta da jan ragamar tattalin arziki ma na zamani ne,yanayin nazarin ilimi ya fi kyau.Idan na iya samun dama zan iya samun bayanai a wannan fannin da ni kaina,ya fi kyau da na samu daga sauran hukumomi,haka kuma zan iya shiga cikin ayyukan."

Daliban kasar Sin kamar He Li wadanda suke son karo ilimi zuwa kasar Amurka ba kadan b a ne, Amurka ta zama kasa ce da ta fi jawo hankulan daliban kasar Sin da ke neman karo ilimi.Bisa wani rahoton shekara da kungiyar ilimi ta duniya ta kasar Amurka ta bayar,an ce daliban kasar Sin da ke dalibta a Amurka sun zarce dubu sittin daga shekarar karatu ta 2004 zuwa shekarar karatu ta 2005.

A sa'I daya kuma Amurkawa da dama sun zo kasar Sin domin koyon sinanci da al'adun Sin da ilimin zamantakewa da fasaha.Natasha lane malama ce da ta zo daga wani kolejin koyon ilimin Acupuncture na jihar Mexicota Amurka.Ta ce "wasu ilimimun iya samu daga littattafai,wasu kuwa saimu same su cikin ayyukanmu.Malaman koyarwan kasar Sin sun fi gwanancewa,kuma suna so su ba mu fasahohinsu da jagoranci,lalle muna iya karo ilimi a kasar Sin."

Bisa kididigar da aka yi,an ce ban da wadanda suka shiga ko da horoa kasar Sin da akwai daliban Amurka sama da dubu hudu da suke karatu a kasar Sin a halin yanzu,yawancinsu suna karatun digiri ne.(Ali)