Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-03 20:09:30    
A kara jin ra'yoyin kasar Sin a bangaren wasannin motsa jiki na kasa da kasa

cri

A shekarar da ta wuce, wani babban jami'in bangaren wasannin motsa jiki na kasar Sin Malam Ma Wenguang ya ci zaben zaman mataimakin shugaban hukumar wasan daga nauyi ta kasa da kasa. Bayan haka ya bayyana cewa, nasarar da ta samu wajen cin zaben nan ta dangaci kasa mahaifarsa mai kasaita da matsayin ci gaban kasar Sin a cikin wasan daga nauyi.

Ko da yake kasar Sin ta sami manyan nasarori a cikin wasan daga nauyi, musamman ma mata 'yan wasa na kasar Sin sun taba kai matsayi na farko a cikin wasan daga nauyi na duniya, amma duk da haka ba ta da ikon bayyana ra'ayinta a bangaren daga nauyi na kasa da kasa. Yanzu, Malam Ma Wenguang ya canja wannan. Cikin wakiltar bangaren wasan daga nauyi na kasar Sin, kuma a karo na farko ne, Malam Ma Wengunag, shugaban cibiyar kula da wasan daga nauyi da na kokawa da judo ta babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ya zama daya daga cikin manyan shugabannin hukumar wasan daga nauyi ta kasa da kasa. A wannan gami, Malam Ma Wenguna da sauran 'yan takara 16 sun yi takara mai zafi don neman cin zaben zaman mataimakin shugaban hukumar wasan daga nauyi ta kasa da kasa da sauran mukamai biyar.

Da Malam Ma Wenguang ya tabo magana a kan aiki da zai yi, sai ya ce, a farkon farko, zai yi kokari sosai wajen daidaita batun shan magani mai kara kuzari. Haka nan kuma zai sa kaimi ga kasar Sin da ta yi musaye-musaye a tsakaninta da kasashen waje a fannin wasan daga nauyi, ta yi koyi da kyakkyawan sakamako da kasashen waje suka samu wajen horar da 'yan wasa da dawo da karfin jiki bayan gasar, a sa'i daya za ta bayyana wa kasashen waje sakamako mai kyau da ta samu wajen bunkasa wasan daga nauyi.

Hukumar wasannin Olympic da hukumomin wasannin motsa jiki iri-iri na kasa da kasa kullum suna son kasar Sin ta kara taka rawa sosai wajen bunkasa kasuwannin wasannin da horar da 'yan wasa da dai sauransu, musammam ma kasashe matasa suna fatan kasar Sin za ta kara kokari wajen shiga cikin wadannan ayyuka don yin watsi da kane-kane da wasu kasashe masu sukuni ke yi wa wasu hukumomin wasannin motsa jiki.

A gun cikakken zaman taron hukumar wasannin Olympic ta duniya da aka shirya a lokacin wasannin Olympic na Athens na shekarar bariya, Malam Yu Zaiqing, wakilin kasar Sin ya ci zaben zaman wakilin kwamitin zartaswa na wannan hukuma, wato ke nan ya zama daya daga cikin manyan shugabannin hukumar. Bayan haka wani mataimakin shugaban hukumar wasannin Olympic ta kasa da kasa ya bayyana wa wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, "muna bukatar wani wakilin Sin da ya shiga cikin kwamitin zartaswa ta hukumar."

A gun wasannin Olympci na Athens, kasar Sin ta zama ta biyu wajen samun yawan lambobin zinariya. Ta haka an kara mayar da kasar Sin bisa matsayinta na babbar kasa a bangaren wasannin motsa jiki na duniya. Daga nan ne, ake ta kara jin ra'ayoyin kasar Sin a bangaren wasannin motsa jiki na kasa da kasa. Wannan yana da matukar muhimmanci ga kara daga kwarjinin kasar Sin a duniya, da kara karfin hadin guiwa a tsakaninta da kasashe daban daban, da kuma bunkasa harkokin kasuwanci da hukumomin wasanni na kasa da kasa ke yi a kasar Sin.

Yanzu, kwararru a fannin wasannin motsa jiki na kasar Sin suna kara taka rawarsu sosai a cikin hukumomin wasanni na kasa da kasa ta hanyar shiga takara da ta shirya gasar wasannin kasa da kasa a kasar Sin da kuma sauransu. (Halilu)