Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-02 19:27:41    
Halin da ake ciki a kasar Sin wajen masaku

cri

A shekarar 2005, ko da yake an yi hargitsin ciniki da hauhawar darajar kudin kasar Sin da ake kira Renminbi, amma a galibi dai sana'ar saka ta kasar Sin tana ci gaba da samun karuwa wajen tattalin arziki, yawan kudin da manyan masaku suka samu wajen sayar da kayayyaki cikin shekarar ya kai Renminbi kusan Yuan biliyan 2000, yawan ribar da suka samu ya kai wajen Yuan biliyan 66, jimlar kudin da duk sana'ar ta samu wajen sayar da kayayyaki zuwa kasashen waje ta kai kusan dalar biliyan 116.

Bisa harsashin saurin karuwar tattalin arziki da aka samu daga shekarar 2002 zuwa ta 2004, a shekarar 2005 kuma sana'ar saka ta kasar Sin ta kara samun ci gaba da sauri. Bisa adadin da hukumar yin kididdigar kasar Sin ta bayar an ce, yawan kudin shiga da manyan masakun kasar suka samu daga watan Janairu zuwa watan Oktoba na shekarar 2005 wajen sayar da kayayyaki da karuwar kudin masaku dukansu sun wuce matsayin karuwar kudin da aka samu a duk shekarar 2004.

Sabo da hauhawar farashin man fetur da babakeren da kasashen duniya ke yi wa danyun kayayyakin sana'ar yin zare ta hanyar kimiyya, shi ya sa yawan kudin da wannan sana'ar ta ware domin sayen danyun kayayyaki ya karu, kuma ta gamu da wahaloli wajen sayar da kayayyanta. Ban da sana'ar yin zare ta hanyar kimiyya wadda yawan ribar da ta samu ya ragu da kashi 30 bisa 100, sauran manyan masaku dukkansu sun tabbatar da makasudinsu na ci gaba da samun karuwar riba.

Ko da yake an gamu da tasirin da aka kawo sabo da hargitsin ciniki da aka yi tsakanin Amurka da Turai, da harajin da ake buga wa kayayyakin fici da kuma hauhawar darajar kudin Renminbi, amma duk da haka a shekarar da ta wuce, sana'ar saka ta kasar Sin ta dogara bisa kayayyakin da ta fitar zuwa kasashen waje ta hanyar zamani, musamman ma masaku masu gyara kayayyaki sun kara karfinsu don yin gasa a tsakaninsu, shi ya sa har ila yau suna ci gaba da samun karuwa da sauri.

Sa'an nan kuma, a shekarar da ta wuce da akwai wasu matsalolin da suka jawo hankulan mutane a lokacin da ake tafiyar da harkokin sana'ar saka.

Matsala ta farko ita ce, an sake yin cinikin kayayyakin saka cikin 'yanci a duniya, wannan ba ma kawai yana da amfani ga masakun kasar Sin wajen daga matsayinsu mai rinjaye ba, sa'an nan kuma yawan hargitsin ciniki ya karu sosai.

Ta 2, sakamakon saurin yunkurin da ake yi wajen sana'ar saka domin samun tsarin bai daya a duniya, ban da hargitsin cinikin da ake yi kuma, yawan hadarurrukan da masana'antu ke fuskanta wajen ka'idar sauyin kudi, da yawan ruwan kudi, da danyun kayayyaki da kuma abubuwan siyasa na shiyya-shiyya su ma sun karu.

Ta 3, kara kyautata muhallin kasuwanni tana da muhimmancin gaske ga masakun kasar Sin don kara karfinsu don yin gasa tsakanin kasashen duniya.

Ta 4, cikin sabon halin da ake ciki yanzu, an kara abubuwan kasawa na masakun kasar Sin sai kara bayyanuwa suke wajen sabunta fasaha cikin walwala, da kago lambobin kayayyaki masu shahara, da tsarin sayar da kayayyaki da na tafiyar da harkokin masaku, ta yadda 'yan kasuwa da mutanen da suke mallakar lambobin kayayyaki da tarunan tajirai za su iya cin riba da yawa. (Umaru)