Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-02 19:23:12    
Takaitaccen bayani game da nahiyar Afirka

cri

Nahiyar Afirka tana gabas da tekun India kuma tana yamma da tekun Atlantika, wadda ikwaita ta ratsa ta, a arewa, Bahar Rum da zirin Gibraltar sun hada ta da nahiyar Turai, haka kuma koramar Suez tana arewa maso gabashinta. Duk fadin Afirka ya kai muraba'in kilomita miliyan 30 da dubu 290, wanda ya kai kashi 20.2 daga cikin dari na dukkan nahiyoyin duniya, ta yadda ta zama babbar nahiya ta biyu a bayan Asiya. A halin yanzu dai, ya kasance da kasashe masu zaman kai da yawansu ya kai 53 cikin shiyoyyi biyar wato arewacin Afirka da gabashin Afirka da yammacin Afirka da tsakiyar Afirka da kudancin Afirka.

Tsawon gabar tekun Afirka ya kai kilomita dubu 30 da dari 5, kashi biyu da ke cikin duk fadinta suna zama tsibirai. A yankunanta da ke dab da teku, ya kasance da wasu duwatsu, sabo da haka, tsayinta ya kai mita 750: a arewa maso yamma, sai duwatsun Atlas, a gabashinta, sai dutsen Kenya. Babbar zaizaiyar kasa a gabashin Afrika ta fi tsawo a duk duniya, wadda ta yi arewa da wata bahar da ake kira Dead Sea a bakin Turawa da ke yammacin Asiya, tsawonta ya yi kusan kilomita dubu 6 da dari 7. a cikin wannan babbar zaizaiyar kasa, ya kasance da wasu tabkoki. A nahiyar Afirka, yawancin koguna sun kasance ne ruwa mai tafiya da sauri ko kuma magangarar ruwa. Kogin Nile ya shiga cikin Bahar Rum, kogunan Congo da Niger da Senegal suna shiga cikin tekun Atlantic, kogin Zambia yana shiga cikin tekun India. Kogin Nile ya fi tsawo a duk duniya. Yawancin tabkoki na Afirka suna filaton gabashin Afirka, daga cikinsu tabkin Victoria ya fi girma a duk Afirka.

Afirka nahiya ce mai arzikin ma'adinai, a halin yanzu dai, ma'adinai da aka sani a Afirka kamar man fetur da tagulla da zinariya da daimun da bauxite da phosphate da niobium da kuma cobalt a bakin Turawa sun yi yawa sosai. An fi samun man fetur a arewacin Afirka da kasashen da ke dab da tekun Atlantic, yawan man fetur a wuraren ya kai kashi 12 daga cikin dari na jimlar yawan man fetur na duk duniya. An fi samun tagulla a kasashen Zambia da Kongo(Kinshasa), yawancin zinariya kuma yana kasashen Afirka ta kudu da Ghana da Zimbabuwei da Kongo(Kinshasa), yawancin daimun yana kasashen Kongo(Kinshasa) da Afirka ta kudu da Botswana da Ghana da Zimbabuwei. Ban da wadannan ma'adinai da muka ambata a sama kuma, nahiyar Afirka tana da manganese da antimony da chrome da vanadiumranium da platinum da iron da tin da asbestos a bakin Turawa da dai sauran makamantansu. Sashen da itatuwa suka mamaye a Afirka ya kai kashi 21 da ke cikin dari. Sashen da ciyayi suka mamaye ya kai kashi 27 da ke cikin dari, wanda ya fi yawa a duk nahiyoyi. A cikin ruwan Afirka, ya kasance da kifaye da yawa. Hamada ta kai sulusin dukkan fadin nahiyar Afirka, Sahara, hamada ce da ta fi girma a duk duniya, fadinta ya kai muraba'in kilomita miliyan 9 da dubu 450.

Yawan mutanen Afirka ya kai kimanin miliyan 800, wanda ya kai kashi 13 daga cikin dari na jimlar yawan mutanen duk duniya a bayan Asiya. Yawan hayayyafa da yawan mutane da ke mutuwa da yawan mutane da ke karuwa ya fi na sauran nahiyoyi. An fi samun kabilu da yawa a nahiyar Afirka, yawancin kabilun bakakken fata ne, sauransu fararran fata da kuma rawayan fata. Yawancin mazaunan Afirka suna nuna biyayya ga addinan gargajiya da musulunci, wasu kuma suna bin addinan Catholic da Kirista.(Danladi)