Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-31 21:41:20    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(26/01-01/02)

cri
A cikin karon karshe na gasar tsakanin mata biyu biyu ta budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta Australia da aka yi a birnin Melbourne a ran 27 ga watan jiya, 'yan wasan kasar Sin Zheng Jie da Yan Zi sun lashe 'yan wasan kasashen Amurka da Australia da ci 2 da 1, sun zama zakaru. Wannan ne karo na farko da 'yan wasan kasar Sin suka zama zakaru a cikin manyan budaddun gasanninn wasan kwallon tennis na duniya. Wannan wani babban ci gaba ne daban da kasar Sin ta samu a fannin wasan kwallon tennis, bayan da 'yan wasan kasar Sin suka zama zakaru cikin gasar tsakanin mata biyu biyu ta gasar wasan kwallon tennis ta wasannin Olympic na Athens a shekarar 2004. Ban da wannan kuma, dan wasan kasar Switzerland Roger Federer ya zama zakara cikin gasar tsakanin namiji da namiji, kuma 'yar kasar Faransa Amelie Mauresmo ta zama zakara cikin gasar tsakanin mace da mace.

Kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya fayyace cewa, zai aika da ma'aikata 10 zuwa wasannin kasashen renon Ingila wato the Common Wealth Games don yin aikin faratis. An kiyasta cewa, 'yan wasa fiye da dubu 4 daga kasashe da yankuna fiye da 70 za su shiga wannan wasannin da za a yi a birnin Melbourne na kasar Australia a ran 15 ga watan Maris. Jami'in da abin ya shafa na kwamitin nan ya bayyana cewa, wannan dama ce mai daraja wajen horo, kwamitin ya sake aika da ma'aikatanta zuwa manyan wasannin duniya bayan wasannin Olympic na Athens da wasannin Olympic na lokacin hunturu na Torino.

Tashar internet ta kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing da kuma manyan tasoshin internet na kasar Sin sun gabatar da muhimman labaru guda 10 game da wasannin Olympic na Beijing a kwanan baya, tabbatar da kirarin wasannin Olympic na shekarar 2008 wato "duniya daya, buri daya ga duk duniya" da sauran labaru 9 sun shiga wannan jeri. Kwamitin nan ya fayyace a ran 29 ga watan jiya cewa, zai ci gaba da gudanar da wannan aiki a shekarar da muka ciki a kan internet, ya yi imanin cewa, aikin nan zai ba da damar sa hannu cikin shirya wasannin Olympic na Beijing ga mutanen kasar.

Ran 29 ga watan jiya shugaban hukumar motsa jiki ta Beijing Mr. Sun Kanglin ya fayyace cewa, Beijing za ta yi budaddiyar gasar Taekwondo ta kasar Sin da gasar fid da gwani ta guje-guje da tsalle-tsalle ta matasa ta duniya da gasar fid da gwani ta wasan kwallo mai laushi ta mata ta duniya da budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta kasar Sin da kuma gasar cin kofin duniya ta gasar tseren mutum daya cikin wasanni 3 a shekarar 2006, don tattaba wasa ga wasannin Olympic na shekarar 2008.

A cikin budaddiyar gasar wasan kwallon tebur da aka rufe a kasar Croatia a ran 29 ga watan jiya, kungiyar kasar Sin ta sami lambobin zinare guda 3. Wadannan zakaru 3 su ne Guo Yue a cikin gasar tsakanin mace da mace, da Chen Qi da Wang Hao a cikin gasar tsakanin maza biyu biyu, da kuma Zhang Yi'ning da Li Nan a cikin gasar tsakanin mata biyu biyu. Dan wasan kasar Belarus Vladimir Samsonov ya zama zakara cikin gasar tsakanin namiji da namiji, saboda ya lashe Chen Qi da cin 4 da 3.(Tasallah)