Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-31 17:31:08    
Wani makaho mai suna Gao Zhipeng kuma mai tsara wake-wake da kide-kide

cri
Mr Gao Zhipeng wani makaho ne da ke kwarewa sosai wajen tsara wake-wake da kide-kide da kuma rera wakoki da kada kayyayakin kida. A cikin shekaru da yawa da suka wuce, bisa burin da ya nema na kishin wake-wake da kide-kide sosai da sosai tare da fuskatar zaman rayuwarsa da ke shan wahaloli da yawa, ya girma cikin mawuyacin hali a kan hanyar yin wasannin fasahohi. Yau za mu bayyana wasu abubuwa dangane da wanann makaho mai suna Gao Zhipeng.

An haifi Mr Gao Zhipeng a wani kauyen lardin Shanxi da ke arewacin kasar Sin. Lokacin da ya cika shekaru 6 da haihuwa ne, ya makance bisa sanadiyar cikas da aka samu wajen aikin likitanci. Dayake ba a samu makarantar makafi a wurin da yake zama ba, shi ya sa bai taba samun damar shiga makaranta, lokacin da ya cika shekaru 9 da haihuwa, ya soma koyon kada "Erhu" wato kayan kidan da aka yi da tsirkiyoyi. A wancan lokaci, ya kan zauna a dab da wurin da mahaifinsa yake zama in ya komo gida daga wurin aiki da maraice, da mahaifinsa ya rera wata waka, shi ma ya maimaita abin da ya rera ta hanyar kada kayan kidan da ake kira Erhu, ba da dadewa ba ya iya rera wasu wakokin gargajiya na garinsu, sai ya yi farin ciki sosai da sosai, kuma ya kara sha'awarsa wajen koyon kada kayan kida. Ba da dadewa ba, kwarewarsa ta kada kayan kidan da ake kira Erhu ta fi ta mahaifinsa.

A lokacin da Mr Gao Zhipeng ya cika shekaru 13 da haihuwa, mahaifinsa ya aika shi zuwa wani kos na koyon ilmin buga gangunan gargajiya a wurin da ya ke zama. A cikin shekara daya kawai, ya iya rike da dabarun da ake bi na busa wani kayan busa da ake kira "Horn" da wani daban da ake kira "A reed Pipe wind instrument" da sauran kayayyakin kida da rera wakoki na gargajiyar kasar Sin . A lokacin da ya cika shekaru 16, sai ya kafa kungiyarsa ta kansa ta nuna wasannin buga ganguna don yawon nuna wasannin fasaha a kauye kauye, ana nuna sha'awa sosai ga wasannin da kungiyarsa ta nuna. Kuma ya sami kudadde daga wajen wasannin da ya nuna, saboda haka ya kan ba da taimako ga iyalinsu wajen zaman rayuwa.

Mutane da yawa suna hassada gare shi bisa sanadiyar aikinsa da ke iya samun kudadde. Amma lokacin da ya sami wani labari da cewa, a birnin Taiyuan na lardin Shanxi, an kafa wata makaranta musamman domin makafi, sai bai yi shakku ko kadan ba, ya yi watsi da kungiyarsa, ya shiga makarantar don soma karatunsa. Ya bayyana cewa,

Ina dalilin da ya sa da na shiga makarantar? shi ne saboda tun lokacin da nake karami, ina da wani buri da imani, wato na ji cewar wai zan yi wani babban aiki, ina son in zama wani babban mai nuna fasahar wake-wake da kide-kide amma ba don samun kudadde kawai ba.

A shekarar 1992, lokacin da ya cika shekaru 18 da haihuwa, ya je birnin Taiyuan don neman shiga makaranta, a kowane mako na wancan lokaci, ya kan je rera wakoki a tashoshin jiragen kasa ko a titunan da ke cunkushe da mutane, ya jawo sha'awar masu sauraro ko 'yan kallo sosai , kuma shumagabar makarantarsa tana ta himmantar da shi wajen tsara wake-wake da kide-kide. A shekarar 1994, Mr Gao Zhipeng ya wallafi wasu wakokin da ke bayyana yadda ya ke girma da cigaban da aka samu a zamanin yau. Wakar da ya wallafa mai suna : "taurarin da ke cika sararin samaniya naka ne ba na sauran mutane ba" da " muryar zuciya" da sauran wakokin da ya wallafa sun sami lambobin yabo a gun gasannin da aka shirya.

Mr Gao Zhipeng yana niyyar shiga karatu a Jami'a don cim ma burinsa na kara ilmi. A shekarar 2000, ya ci jarrabawa kuma ya shiga sashen koyon ilmin kide-kide da wake-wake na jami'ar koyar da ilmin wasannin kwaikwayo ta kasar Sin da ke birnin Beijing. Ya bayyana cewa,

ban da koyon ilmin musamman dangane da wake-wake da kide-kide da sauran ilmi a jami'ar, ina da niyyar yin wani babban aiki, na tabbatar da cewa, ba zan yi aikin lami lafiya ba, amma na riga na shirya sosai da sosai.

Bayan da ya kammala karatunsa, yana ci gaba da kasancewa cikin halin rike da imaninsa sosai. Yanzu yana nan yana shirin kafa dakinsa na nuna fasahar wake-wke da kide-kide, yana son ya iya ba da taimako ga zamantakewar al'umma da karamin karfinsa.(Halima)