Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-30 17:21:26    
Kasar Gabon da ke da bishiyoyi da yawa

cri

Kasar Gabon ana kan kiranta da cewa "wuri mai zinariya da ke da bishiyoyi da yawa", lokacin da jiragen sama suke yin zirga-zirga a sararin samaniyar kasar, nan da nan ake iya gane cewa, wata kusurwar yankin ta shiga cikin Zirin tekun Guinea, sai ka ga ko'ina duniyar ta zama koriya shar ba tare da dan kasa a cikin karamin yankinta ba, kuma ana ganin cewa, tamkar yadda wani zanen siliki mai fadi sosai kuma mai launin kore ya shimfidu a kan babban teku. Kai, ta wannan, ana iya tunawa da tutar kasar Gabon da ke da launin Koriya da rawaye da shudi, launin kore yana sama, kuma yana wakilcin kurmin, wanda dukiya ce mai daraja sosai ta kasar Gabon.

Yawan fadin kurmin kasar Gabon ya kai murraba'in kadada miliyan 22 wanda ya kai kashi 85 cikin dari bisa yawan fadin kasar, daga cikinsu, an dasa bishiyoyi iri iri masu yawan gaske, alal misali, katakai da ake kira Okume da za a iya samu ya kai ninkin mita miliyan 130, ya shiga jerin gaba a duniya.

In ana tafiya a titunan birnin Libreville, sai a ga ko'ina birnin ya zama koriya shar. A gefunan biyu na babbar hanyar da ke bakin teku, bishiyoyi iri na kwa kwa da sauran bishiyoyin da ke da ganyaye masu fadi sosai suna layi layi, in an tashi daga cibiyar birnin da dan nesa, sai a iya ganin bishiyoyi da yawan gaske, gidaje suna karkashin inuwar bishiyoyi, duk birnin ya yi kama da lambun shan iska iri na kurmi. A wani lambun shan iska na tsire-tsire da ke mamaye yankin da yawan fadinsa ya kai murraba'in kadada 16 kuma bai yi nesa da unguwoyin birnin ba, da akwai tsire-tsire iri iri da yawansu ya kai 1800 ko fiye.

Allah ya kawo alheri ga kasar sosai da sosai, Ikwaita ta ratsa wurin da ke nesa da birnin Libreville da kilomita 100, rana tana haskaka wurin sosai a duk shekara, ana samun isasshen ruwan sama saboda tekun Atlantic, mutanen wurin sun yi alfahari da cewa, in an jefa wani dutse a wurin da suke zama, to ko shakka babu za a iya samun tsiro a kan dutsen nan. Kasar Gabon tana da wadatattun albarkatan ma'adinai. Yawan man fetur da aka tanada a kasar ya kai ton miliyan dari 4, wanda ya zama jeri na hudu a kasashen Afrika. Yawan manganese da aka tanada ya kai ton miliyan dari biyu, wato ya kai kashi daya cikin kashi hudu bisa yawansu da aka riga aka yi safiyonsu a duk duniya , ita ce kasa ta uku a duniya wajen haka manganese da kuma fitar da su zuwa kasashen waje . Bayan da ta gano man fetur a shekaru 60 na karnin da ya shige, sai an mayar da wannan kasar da ke da mutane miliyan daya da dubu 150 ko fiye don ta zama daya tak da ke cikin kasashen Afrika masu magana da harshen Faransanci bisa matsayin matsakaici wajen samun kudin shiga. Kwatankwacin kudadden da kowane mutum ya samu wajen sarrafe-sarrafe a gidanta ya kai kudin Amurka dolla dubu 4.

Idan an yawo a titunan birnin Lebreville, an gano cewa, ashe, sabbin motoci da yawa ne da suke zirga zirga kai da kawowa . Bisa abubuwan da 'yan kasuwa na sayar da motoci suka bayyana, an ce, a kowace shekara, a birnin Lebreville kawai, ana sayar da sabbin motoci da yawansu ya kai dubu 3, wannan ba dan adadi ba ne ga birnin da ke da yawan mutane dubu 500. Mazauna birnin da 'yan makaranta sun fita waje ne ta hanyar daukar motocin haya wato Taxi. An bayyana cewa, in wasu mutane sun yi hayar wata mota kawai, sai a biya kudin haya da kudin Amurka rabin dalla kawai a cikin unguwoyin birnin.

Shahararriyar lambar Adidas ita ma tana da rassan kantunan musamman nata a birnin Lebreville. Babbar kasuwa mai suna Monpolo ma na da mataki mai girma, kuma kayayyaki da yawa suna makare a kasuwar, yawancinsu da aka shigar da su ne daga kasashen waje, sa'anan kuma suna da tsada sosai, wato farashin Tumatir da ke da nauyin kilo daya ya kai kudin Amurka dolla goma, farashin naman sa da ke da nauyin kilo daya ya kai dolla 36 da dai sauransu, amma masu saye saye da yawa suna saye-saye a ciki. Mutanen kasar Gabon suna sanya tufaffi masu kyau tare da tsabta sosai, tufaffin da mata suka sanya suna da kyaun gani sosai tare da launuka iri iri, kuma an dinke su da kyau da inganci.(Halima)