 Bisa kwarya-kwaryar sakamakon da aka samu a ran 26 ga wata, an ce, kungiyar Hamas ta riga ta samu kujeru sama da 70 daga cikin dukan kujeru 132 na kwamitin kafa doka na Palasdinu, wato ta ci nasara a wannan zaben kwamitin kafa doka ke nan. Wannan kuma yana nufin cewa, kungiyar Hamas wadda ta dade tana kan matsayin 'yar kallo' za ta fara taka muhimmiyar rawa a fagen siyasa na Palasdinu. Sabo da haka kuma, sakamakon ya jawo hankulan kasashen duniya sosai, musamman ma bangarori daban daban na shirin shimfida zaman lafiya a gabas ta tsakiya. Sabo da haka, wakilanmu sun ziyarci wani masanin kasar Sin a kan maganar gabas ta tsakiya, Yin Gang, don ya yi muku bayani a kan dalilin da ya sa kungiyar Hamas ta ci zaben da kuma tasirin da abin ya kawo kan halin da ake ciki a gabas ta tsakiya.
A ganin Yin Gang, dalilai da yawa ne suka sa kungiyar Hamas ta cimma nasarar. Ya ce,'Da farko dai, Hamas wata babbar kungiya ce, kuma tana taka muhimmiyar rawa a wajen ba da taimako ga al'ummar Palasdinu, ciki har da kafa gidajen marayu da gidajen ciyar da tsofaffi da kuma makarantu da dai sauransu. Rukunoninta na nuna karfin tuwo kalilan ne, kuma tun bayan watan Afril na bara, Hamas ta riga ta daina daukar matakan nuna karfin tuwo, ta bi yarjejeniyar tsagaita bude wuta, kuma ta yi shelar shiga cikin zabe don neman warware matsaloli ta hanyar siyasa, sabo da haka, ta sami goyon baya sosai daga wajen jama'ar Palasdinu. Na biyu kuma, 'yan kungiyar Hamas sun yi ayyukansu tsakani da Allah kuma cikin inganci, kuma shugabanninta ma mutane ne masu rikon amana, ba su karbar rashawa. Idan an kwatanta su da Fatah wadda ke mulkin Palasdinu a shekaru 10 da suka wuce, Fatah ba ta sami kwarewar aiki ba'

Yin Gang yana ganin cewa, aiki mai wuya ne ga Hamas da ta sauya rawar da take takawa, wato daga kungiyar dakaru zuwa wata jam'iyya ta halal. Ya ce,'ba sai kawai Hamas za ta daidaita manufofinta na da ba, har ma za ta sauya har ta zama wata kungiyar siyasa daban. Da ma a cewar Hamas, ba za ta yi watsi da nuna karfin tuwo ba, kuma ba za ta amince da Isra'ila ba, wannan kuma hali na musamman ne na kungiyar Hamas. Amma yanzu, abin ya zama tilas ga Hamas da ta amince da Isra'ila nan da nan, na biyu kuma, ta yi shelar hada dakarunta da rundunar tsaron Palasdinu nan da nan. Na uku, ta yi shawarwari tare da Isra'ila bisa shirin musanyar kasa da zaman lafiya da kuma yarjejeniyar Oslo. Idan Hamas ba za ta iya daukar wadannan matakai ba, to, gwamnatin da ta kafa ba za ta samu amicewa daga kasashen duniya ba, kuma za ta shiga cikin halin kaka-nika-yi.'
Daga martanin da bangarori daban daban suka mayar a halin yanzu kuma, mun iya gane cewar, nasarar da Hamas ta samu ta yi kamar ta firgita bangarori daban daban na shirin shimfida zaman lafiya a gabas ta tsakiya. Yin Gang ya ce,'tabbas ne wannan zai kawo babban tasiri, har ma zai kai ga kawo tasiri kan babban zaben da za a yi a Isra'ila a watan Maris mai zuwa. Ko Isra'ila ko bangarori hudu kan shimfida zaman lafiya a gabas ta tsakiya, za su gabatar da bukatunsu ga Hamas cikin gajeren lokaci. Wato, da farko, Hamas ta amince da Isra'ila. Na biyu kuma, ta yi watsi da nuna karfin tuwo. Na uku kuma, ta yi shawarwari da Isra'ila. Idan gaskiya ne Hamas ta yi shelar sauya matsayin da ta dauka a da kwata kwata a cikin gajeren lokaci, kuma ta zama wata sabuwar kungiyar siyasa da addini, to, ba yadda Isra'ila za ta yi, sai ta amince da sakamakon, kuma ta fara tuntubar Hamas sannu a hankali. Amma, idan ba za a samu kwanciyar hankali a Palasdinu ba, kuma kungiyar Hamas ta kasa kafa gwamnati ko gwamnatin da ta kafa ba ta sami amincewa daga kasashen duniya ba, lalle ne, Isra'ila za ta kara daukar matakai daga bangare daya kawai.'(Lubabatu Lei)
|