Robert Zoellick, mataimakin sakataren harkokin waje na din din din na kasar Amurka ya yi ziyarar kwanaki uku a kasar Sin wato tun daga ran 23 zuwa ran 25 ga wannan wata. A lokacin ziyararsa, Wen Jiabao, firayim ministan kasar Sin da Li Zhaoxing, ministan harkokin waje da kuma sauran shugabannin kasar sun yi shawarwari tare da Zoellick daya bayan daya a kan huldar tsakanin Sin da Amurka da manyan matsalolin kasa da kasa da na shiyya shiyya da ke jawo hankulansu duka.
Da shehun malami Jin Canrong, mataimakin shugaban kolejin koyon ilmin huldar kasa da kasa na Jami'ar Jama'ar Sin ya tabo magana a kan ziyarar da Zoellick ya yi a kasar Sin, sai ya bayyana cewa, "a hakika dai, abubuwa biyu da ke jawo hankulan mutane su ne, na daya ziyarar da Hu Jintao, shugaban kasar Sin zai yi a kasar Amurka a watan Afrilu mai zuwa. Ya kamata, a iya cewa, Zoellick ya yi ziyarar aikinsa a wannan gami ne don share fage ga ziyarar Hu Jintao. Na biyu kuma hulda a tsakanin Sin da Japan. Yanzu tabarbarewar hulda a tsakanin Sin da Japan ta riga ta jawo hankulan mutanen kasar Amurka. Sabo da haka ziyarar da Hu Jintao, shugaban kasar Sin zai yi a kasar Amurka, da kuma hulda a tsakanin Sin da Japan su ne manyan abubuwa biyu ga ziyarar da Zoellick ya yi a kasar Sin a wannan gami. "
A cikin sanarwar da ta bayar, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Amurka ta bayyana cewa, ziyarar Zoellick wani mataki ne da kasar Amurka ta dauka don neman kara karfin hadin guiwa a tsakaninta da kasar Sin. Haka nan kuma a lokacin ziyararsa, Zoellick shi ma ya gabatar da shawara cewa, kasar Sin za ta kara taka muhimmiyar rawarta a cikin gamayyar kasa da kasa a nan gaba.
Shehun malami Jin Canrong ya kara da cewa, a lokacin ziyarar Zoellick a kasar Sin, bangarori biyu wato Sin da Amurka sun sami ra'ayi daya a wasu fannoni. Don ta Amurka, tana bukatar kasar Sin ta taimake ta wajen daidaita batun nukiliya na yankin Korea da na kasar Iran.
Dangane da huldar da za a yi nan gaba a tsakanin Sin da Amurka, shehun Malami Jin Canrong ya ce, "ko da yaushe kasar Sin tana dora muhimmanci ga hulda da ke tsakaninta da kasar Amurka. Wen Jiabao, firayim ministan kasar Sin ya gana da Zoellick yayin da yake yin ziyara a kasar Sin. Wannan ma ya shaida cewa, gwamnatin kasar Sin tana dora matukar muhimmanci ga hulda a tsakanin kasashen biyu. Amma huldar nan mai muhimmanci da kuma sarkakiya ce. Ga shi yanzu, gwamnatocin kasashen biyu sun fara bin manufarsu mai yakini dangane da huldar nan. Sabo da haka na hakake cewa, ziyarar da Hu Jintao zai yi a kasar Amurka za ta sami sakamako mai kyau, kuma za ta ciyar da huldar da ke tsakanin Sin da Amurka gaba."
Kafin ziyararsa a kasar Sin, Zoellick ya riga ya yi ziyara a kasar Japan. Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Japan suka bayar, an ce, a lokacin ziyararsa a kasar Japan, Zoellick ya taba gabatar da shawara cewa, ya kamata, masanan ilmi na jama'ar Amurka da Sin da Japan su yi nazarin tarihi cikin hadin guiwarsu don kubutar da huldar da ke tsakanin Sin da Japan daga halin kaka-ni-kayi. Game da shawarar nan, Shehun malami Jin Canrong ya ce, "kasar Amurka tana fatan kasar Japan za ta taka rawa sosai a fannin siyasa da zaman lafiya a yankin gabashin Asiya. Amma a garkuwar Amurka, kasar Japan take neman cim ma makasudinta na mayar da Japan don ta zama wata kasa ta "yau da kullum", sabo da haka kasar Japan ta gamu da kiyewa daga wajen kasashe da ke makwabtaka da ita. A cikin irin wannan hali ne, kasar Japan ba za ta iya taka rawarta a yankin gabashin Asiya kamar yadda Amurka ke so ba. Da ganin haka, mutanen Amruka da yawa sun sha tabo magana a kan matsala a cikin rabin shekarar da ta wuce, bai kamata a bar hulda a tsakanin Sin da Japan ta ci gaba da tabarbarewa ba. " (Halilu)
|