An yi bikin bude taron koli na karo na shida na kawancen kasashen Afrika a birnin Khartoum, hedkwatar kasar Sudan ran 23 ga wannan wata. Wakilan kasashe 53 na kawancen kasashen Afrika ciki har da shugabannin kasashe da na gwamnatoci kimanin 30 za su tattauna zaman lafiyar Afrika da bunkasuwarta da hargitsin shiyya-shiyya da aikin mayar da Afrika bai daya da aikin bunkasa al'adu da ilmi a Afrika da sauran batutuwa.
Olusegun Obasanjo, shugaban kawancen kasashen Afrika kuma shugaban kasar Nijeriya da Omar Al-Bashir, shugaban kasar Sudan mai masaukin taron da Thobo Mbeki, shugaban kasar Afrika ta Kudu da Moamer Kadhafi, shugaban kasar Libya da Robert Mugabe, shugaban kasar Zimbabwe da Mohamed Sahnoun, mashawarcin musamman na babban sakataren majalisar dinkin duniya mai kula da harkokin Afrika, da Amr Moussa, babban sakataren kawancen kasashen Larabawa da sauransu sun halarci bikin bude taron da aka yi a wannan rana.
A cikin jawabai da aka yi a gun taron da aka yi a wannan rana, kara karfin hadin kan kasashen Afrika da kare zaman lafiya da zaman karko a babban yankin Afrika cikin hadin guiwa sun zama batutuwa da suka jawo hankulan shugabannin kasashe mahalartan taron duka da kuma burinsu na yin kokari tare.
Mr Olusegun Obasanjo ya bayyana a gun bikin bude taron cewa, babu yadda za a yi a iya tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma a kasashen Afrika daban daban, sai an yi kokari wajen sassauta hali mai zafi da ake ciki a shiyya-shiyya, a kawo karshen hargitsi da tashin hankali a shiyya-shiyya tun da wurwuri. Ya kara da cewa, bisa kokarin da kasashen kawancen Afrika suka yi tare cikin shekarar da ta wuce, an yi ta kyautata halin da ake ciki a kasr Guinea Bissau da Togo da Burundi da Liberiya da Cote D'ivoire da sauran kasashe dangane da zaman lafiya, kuma an sami ci gaba sosai wajen gudanar da aikin samar da zaman lafiya. Wannan ya shaida sosai cewa, kasashen Afrika sun dau niyyar ba da taimakonsu wajen namen kubutar da nahiyar Afrika daga hargitsi da tashin hankali ta hanyar yin kokari tare da kuma kwarewarsu. Amma a sa'i daya kuma ya nuna cewa, aikin samar da zaman lafiya a kasar Somaliya ya tsaya cik, ba a warware ricikin iyakar kasa tsakanin Habasha da Eritrea ba tukuna, batun Darfur na kasar Sudan ma ya zama alakakai ga jama'a. Duk wadannan kalubale ne mai tsanani da nahiyar Afrika ke fuskanta yayin da take neman tabbatar da zaman lafiya da zaman karko. Sabo da haka ya yi kira ga bangarori daban daban da abin ya shafa da su ba da taimakonsu ga kyautata halin zaman lafiya da ake ciki a Afrika.
Yayin da Omar Al-Bashir, shugaban kasar Sudan ke yin jawabin fatan alheri a gun bikin bude taron, ya bayyana cewa, kasarsa tana son yin kokari tare da kasashe masu makwabtaka da ita da kuma sauran kasashen kawancen Afrika don kare zaman lafiya da zaman karko a Afrika. Bisa matsayinta na kasar da batun Darfur ya shafa, Mr Bashir ya bayyana a fili cewa, yana fatan kawancen Afrika zai ci gaba da aiwatar da aikinsa na kare zaman lafiya a yankin Darfur, sai ta haka dai ne za a tabbatar da cewa, Afrika za ta iya daidaita batutuwanta ita da kanta.
Mr Mohamed Sahnoun ya karanta jawabin Kofi Annan, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya a gun taron cewa, majalisar dinkin duniya za ta ci gaba da hadin guiwa sosai a tsakaninta da kawancen Afrika, ta ba da taimako wajen kyautata halin da ake ciki a yankin Darfur dangane da zaman lafiya don ci gaba da yunkurar da aikin samar da zaman lafiya a kasar Sudan.
Haka zalika kasashen Afrika suna fatan za a tabbatar da manyan shirye-shiryensu na samun bunkasuwa da farfadowa ta hanyar gaggauta bunkasa harkokin ba da ilmi da kimiyya d fasaha da al'adu da kuma ingiza aikin mayar da Afrika bai daya, wannan ma wani butu ne mai muhimmanci da ke jawo hankalin wannan taron koli na kawanen Afrika. (Halilu)
|