Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-25 18:49:20    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(19/1-25/1)

cri
Shugaban babbar hukumar motsa jiki ta kasar Sin Mr. Liu Peng ya bayyana a nan birnin Beijing a ran 19 ga wata cewa, kasar Sin ta sami saurin bunkasuwa a fannin sha'anin motsa jiki daga shekarar 2001 zuwa shekarar 2005. Jama'ar kasar Sin sun kara kyautata ra'ayoyinsu na motsa jiki, har zuwa karshen shekarar 2004, ta riga ta zama kan gaba a tsakanin kasashe masu tasowa. Ban da wannan kuma, 'yan wasan kasar Sin sun samu zama zakaru na duniya guda 493 a cikin shekaru 5 da suka wuce, sun karya matsayin bajimta na duniya guda 98. Kasar Sin ta sami lambar zinare ta farko a cikin wasannin Olympic na lokacin hunturu da aka yi a birnin Saltlake na kasar Amurka a shekarar 2002, ta kuma zama na biyu saboda samun lambobin zinare 32 a cikin wasannin Olympic na Athens a shekarar 2004.

Masana masu ilmin tsaron kai daga ma'aikatar kula da tsarin jama' na kasar Greece sun kawo wa Beijing ziyara ta kwanaki 3 daga ran 17 zuwa ran 19 ga wannan wata, bisa gayyatar da kungiyar kula da tsaron kai ta wasannin Olympic na Beijing ta yi musu, a loakcin da suke ziyarar Beijing, wadannan masana 4 da suka sa hannu cikin aikin tsaro kai na wasannin Olympic na Athens sun koyar da takwarorinsu na kasar Sin fasahohin da suka samu daga tsaron kan wasannin Olympic.

Tun daga ran 23 ga wata, tashar Internet ta kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ta bude shafinta na taswira don bauta wa jama'a, inda za a gabatar wa masu yawon shakatawa na gida da waje labarun yawon shakatawa da suka danganci wasannin Olympic na Beijing. A sakamakon taimakon wannan taswira, mutane suna iya samun duk abubuwan da suke shafi wasannin Oympic na Beijing, alal misali filayen wasannin Olympic da dakunansu da katunan sayar da kayayyakin alamun fatan alehri da sauran hajjojin musamman na wasannin da kuma ni'imatattun wuraren yawon shakatawa na birnin Beijing da sauransu. Adireshin wannan tashar Internet shi ne, www. beijing2008.com

Ran 18 ga wata, a nan birnin Beijing, an kafa kungiyar wakilan motsa jiki ta kasar Sin da za ta halarci wasannin Olympic na lokacin hunturu da za a yi a birnin Torino na kasar Italiya daga ran 10 zuwa ran 26 ga watan Faburairu a shekarar da muke ciki. 'Yan wasan kasar Sin 76 za su shiga manyan wasanni guda 3 na wasan kankara da skiing a tsakanin duwastu da kuma Biathlon (wato yin wasan skiing tare da harbe-harbe), za su yi kokarinsu a cikin kananan wasanni 47 a wannan gami.

Ran 22 ga wata, an rufe budaddiyar gasar wasan kwallon badminton ta duk kasar Ingila da aka yi kwanaki 5 ana yinta a birnin Birmingham na kasar Birtaniya. 'Yan wasan kasar Sin sun kwashe lambobin zinare guda 4 daga cikin guda 5. Lin Dan ya zama zakara cikin gasar tsakanin namiji da namiji, Xie Xingfang ta zama zakara cikin gasar tsakanin mace da mace. Sa'an nan kuma 'yan wasan kasar Sin sun zama lambawan cikin gasannin tsakanin mata biyu biyu da kuma gaurayen namiji da mace.

A cikin karon karshe na gasar wasan kwallon kafa ta mata da aka yi tsakanin kasashe 4 bisa gayyata a birnin Guangzhou na kasar Sin a ran 22 ga wata, kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Amurka ta lashe kungiyar kasar Sin da ci 2 ba ko daya, ta zama zakara, kungiyar kasar Sin ta zama ta biyu. Kungiyar kasar Faransa ta zama ta uku, kuma kungiyar kasar Norway ta zama ta hudu a wannan gami.(Tasallah)