Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-25 14:53:03    
Abubuwa da yawa suna bayyana bunkasuwar da Afirka ke samu

cri
A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, bunkasuwar da kasashen Afirka suka samu tana canja tunanin mutanen sauran kasashen duniya. Yanzu harkokin siyasa na Afirka sun fara shiga cikin halin karko, kuma suna samun bunkasuwar tattalin arzikinsu. Sannan kuma, domin kasashen Afirka suna da wadatattun albarkatun halitta da babbar kasuwa, suna jawo hankulan kasashen duniya kuma suna zama sabbin wuraren da kasashen waje suke zuba jari. Wadannan abubuwa suna almantar da cewa, kasashen Afirka suna da boyayyen karfin samun cigaban tattalin arziki.

1, Kasashen Afirka suna ta tabbatar da kwanciyar hankalin siyasa kuma da neman bunkasuwa

A cikin shekaru masu dimbin yawa da suka wuce, nahiyar Afirka tana daya daga cikin yankunan da ke shan yake-yake iri iri domin dalilai iri iri. Bisa kididdigar rikon kwarya da aka yi, tun daga shekaru 60 na karnin da ya gabata, yake-yake da rikice-rikice fiye da 30 sun auku a Afirka inda aka yi sanadiyyar mutuwar mutane miliyan 7. Hasarar tattalin arziki ta kai kudin dolar Amurka fiye da biliyan 250. Bayan an shigo karni na 21 da muke ciki, halin zaman karko a Afirka ya fara samun kyautatuwa a hankali a hankali, tattalin arzikin kasashen Afirka yana ta samun ci gaba yadda ya kamata. Sannan kuma, Tarayyar Afirka tana ba da gudummawarta a kai a kai. Yanzu tunanin yin watsi da hargitsin nuna karfin tuwo kuma da neman zaman lafiya ya fara yaduwa a Afirka, musamman a kasashen Angola da Sudan da Somaliya da Liberia wadanda suka sha yake-yake sosai a cikin shekaru da yawa da suka wuce sun fara shiga cikin halin neman zaman lafiya da na karko. Sabo da haka, an ce, yanzu wannan nahiyar da ta fi talauci a duk duniya tana gamuwa da damar neman bunkasuwa a cikin tarihi.

Abin da ya kamata a ambata shi ne, bayan an kafa Tarayyar Afirka yau da shekaru 3 da suka wuce, tana kokarin tsoma baki a cikin rikice-rikicen da suka auku a Afirka. Tarayyar Afirka ta kuma jaddada cewa, ya kamata a dogara kan karfin dukkan kasashen Afirka domin daidaita maganganun da suke kasancewa a gabansu da kansu. Sannan kuma, a kan wasu muhimman maganganun duniya, ciki har da maganar yin kwaskwarima kan M.D.D., Tarayyar Afirka ta bayar da ra'ayoyinta a bayyane, kuma tana kiyaye moriyar Afirka da kanta.

2, Makomar bunkasuwar tattalin arzikin Afirka tana da kyau

Abin da ba za a iya musuntawa ba shi ne, har yanzu, nahiyar Afirka nahiya ce mafi talauci a duk fadin duniya. Amma a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, tattalin arzikin kasashen Afirka ya smu kyawawan sauye-sauye. A kwanan baya, kwamitin kula da tattalin arzikin kasashen Afirka na M.D.D. ya bayar da wani rahoto, inda ya ce, saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka ya haye matsayin bajinta ya kai kashi 5.2 cikin kashi dari a shekara ta 2005. Tun daga shekara ta 1993, tattalin arzikin kasashen Afirka yana ta samun bunkasuwa. A shekarar 1994, saurin bunkasuwar tattalin arziki ya wuce saurin karuwar yawan mutane a Afirka. Manazarta suna ganin cewa, tattalin arzikin kasashen Afirka yana iya samun bunkasuwa da sauri a cikin shekaru da yawa da suka wuce, wannan ya almanta cewa, kasashen Afirka suna samun bunkasuwar tattalin arziki cikin hali mai dorewa.

Ana ganin cewa, dalilan da suka sa tattalin arzikin kasashen Afirka ya samu cigaba cikin sauri su ne, da farko dai, ana kiyaye kuma ana tabbatar da zaman lafiya da na karko a kasashen Afirka, sannan kuma, yawa-yawan kasashen Afirka sun dauki manufofin sa ido kan bunkasuwar tattalin arziki daga duk fannoni, kuma sun yi kwaskwarima kan tsarin tattalin arzikinsu cikin daidai lokaci. Bugu da kari kuma, domin tattalin arzikin duk duniya yana samun bunkasuwa sosai, ana bukatar albarkatun halittu kwarai, farashin man fetur na kasuwannin duniya ya yi ta karuwa. Kasashe Afirka wadanda suke fitar da man fetur sun samu riba kwarai. Ban da wadannan, kasashen yammacin duniya suna ganin cewa, wadatattun albarkatun halittu da manyan boyayyun kasuwanni na kasashen Afirka suna da muhimmanci kwarai, sun fara sake nazarin kan manufofin da suke bi kan Afirka. Sabo da haka, sun fara kara taimako da zuba jari a kasashen Afirka. Kayayyakin kasashen Afirka ma sun samu izinin shiga kasuwannin kasashen yammacin duniya.

Abin da ya fi muhimmanci shi ne, Tarayyar Afirka ta fara aiwatar da sabon shirin abokantaka domin neman bunkasuwar Afirka domin fama da talauci, ta kuma kafa tsarin binciken juna a tsakanin kasashen Afirka domin tabbatar da aiwatar da wannan sabon shiri.

Amma, domin wasu dalilan tarihi da suka kasance a Afirka, har yanzu, kasashen Afirka suna fuskantar kalubale iri iri lokacin da suke yunkurin cimma burin neman bunkasuwa. (Sanusi Chen)