Bisa shiri, za a fara yin taron shugabannin gamayyar Afirka na karo na shida a ran 23 ga wata a birnin Khartum, hedkwatar kasar Sudan. Gaba daya ne kasashe 53 na gamayyar Afirka za su halarci wannan taro, ciki har da shugabannin kasashen Afirka da manyan kusoshin gwamnati sama da 30. Manazarta suna ganin cewa, a gun wannan taron, shugabanni mahalartan taron za su ci gaba da kokarin neman tabbatar da kwanciyar hankali da bunkasuwa a Afirka.
Babban jigon wannan taron shugabannin gamayyar Afirka shi ne 'ilmi da al'adu'. Gamayyar Afirka tana fatan za a ci gaba da dora muhimmanci a kan bunkasa aikin ba da ilmi da horar da kwararru a gun wannan taro, don samar da sharuda masu kyau wajen tabbatar da kwanciyar hankali da albarka da dinkuwar kasa a Afirka. Yawancin shugabannin kasashen Afirka suna tattare da ra'ayin cewar, a yayin da ake aiwatar da 'shirin ba da ilmi a Afirka cikin shekaru goma' na farko tun daga shekarar 1996 har zuwa 2006, kasashe daban daban na Afirka sun sami babban ci gaba a wajen tabbatar da ikon kowa da kowa na samun ilmi cikin daidaici, amma duk da haka, a halin yanzu, yawancin kasashen Afirka suna fuskantar matsalolin kaurar masana zuwa kasashen waje da karancin samun kudin ba da ilmi daga gwamnati, sabo da haka, maganar ba da ilmi a Afirka tana ci gaba da fuskantar babban kalubale. Shi ya sa a wannan taron shugabanni, ana son sa kaimi ga aiwatar da shiri na biyu na ba da ilmi a Afirka cikin shekaru 10, wato daga shekara ta 2006 zuwa 2015, ta yadda za a cimma burin tabbatar da ikon kowa na samun ilmi cikin daidaici a kasashe daban daban na Afirka.
Ban da wannan, a gun wannan taro, shugabannin da za su halarci taron za su yi nazari a kan shawarar da gwamnatin kasar Sudan ta gabatar, wato kafa kungiyar kula da harkokin ba da ilmi da kimiyya da al'adu ta Afirka wadda hade take da kungiyar UNESCO, wato kungiyar kula da harkokin ba da ilmi da kimiyya da al'adu ta duniya, don sa kaimi ga bunkasuwar Afirka a fannonin ba da ilmi da kimiyya da al'adu. Babban daraktan kungiyar UNESCO ma zai halarci wannan taro, kuma zai bayar da jawabi a kan babban jigon wannan taro.
A gun taron, shugabanni mahalartan taron za su kuma yi bincike a kan rahoton da aka gabatar dangane da kafa 'tarayyar kasashen Afirka' don neman ingiza bunkasuwar siyasa da tattalin arziki bai daya a Afirka. shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi ne ya gabatar da ainihin shawarar nan ta kafa gamayyar kasashen Afirka wadda ke da nufin karfafa bunkasuwar Afirka bai daya, wato a kafa wata tarayyar kasashe masu mulkin kansu.
Bayan haka, shugabanni mahalartan taron za su kuma saurari da kuma binciki rahoton da abin ya shafa da kwamitin sulhu na gamayyar Afirka ya gabatar. An ce, rikicin Darfur na Sudan da gardamar da ke tsakanin Sudan da Chadi da tashin hankali a kasar Cote d'Ivoire su ne muhimman batutuwan da mahalartan taron za su tattauna.
Mahalartan taron za su kuma yi nazari a kan batutuwa kamar su gyare-gyaren MDD da kafa kasuwar takardun hada-hadar kudi a Afirka ta kudu ko Masar da kuma kafa asusun ba da agaji don sassauta barnar da hauhawar farashin man fetur ta kawo wa tattalin arzikin kasashe masu talauci na Afirka da yaki da ciwon Sida da dai sauransu.
Manazarta suna ganin cewa, a yayin da ake ta zurfafa bunkasuwar tattalin arzikin duniya bai daya, shugabannin kasashen Afirka sun riga sun gane cewa, ba za a cimma kawar da tashin hankali da talauci daga Afirka ba, sai dai an yi kokarin ingiza bunkasuwar siyasa da tattalin arziki bai daya a Afirka da kuma karfafa hadin kan kasashen Afirka.(Lubabatu Lei)
|