Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-20 10:37:50    
Hadaddiyar gasar wasan kwallon teburi ta gwanaye ta kasar Sin tana kan hanyar zama wata shahararriyar alama a duk duniya

cri

Kwallon teburi yana kasancewa kwallon kasa a Sin, 'yan wasa Sinawa su kan zama zakaru a duk duniya. A halin yanzu dai, Sinawa suna kokari suna gudanar da hadaddiyar gasar wasan kwallon teburi ta gwanaye ta kasar, suna fata gasar za ta zama wata shahararriyar alama a duk duniya.

A 'yan kwanakin baya, an shirya taron takaitawa a kan hadaddiyar gasar wasan kwallon teburi ta gwanaye ta kasar Sin na shekarar 2005 a birnin Beijing, inda aka kimanta halin da gasar take ciki a shekarar 2005. mahalartan taron sun bayyana cewa, a sakamakon kokarin da ake yi cikin shekaru 7 da suka gabata da aka fara hadaddiyar gasar kwallon teburi ta gwanaye ta kasar Sin, gasar ta riga tana da matsayi da ya fi duk duniya, haka kuma ta sami sakamako mai kyau wajen zama wata shahararriyar alama a duk duniya. Malam Zhang Xiaopeng, mataimakin darektan kwallon teburi na hukumar wasanni ta kasar Sin, ya bayyana cewa,

'Ko a fannin 'yan wasa na gwanaye, ko a fannin takarar gasa, ko kuma a fannin 'yan wasa da suka zo daga kasashen waje, a halin yanzu dai, hadaddiyar gasar kwallon teburi ta gwanaye ta kasar Sin ta fi kyau a duk duniya.'

An fara gudanar da hadaddiyar gasar kwallon teburi ta gwanaye ta kasar Sin ne a shekarar 1999. A shekarar 2005, ya kasance da kulob 12 na maza kuma 12 na mata a gasar. Mutanen da yawa su kan kalli gasar a filayen wasa ko ta telibijin daga gidan telibijin na tsakiyar kasar Sin. Malam Lan Ping, wani mai nishadin kwallon teburi a Beijing, ya ce haka,

'A ko wace ranar Lahadi, na kan kalli hadaddiyar gasar kwallon teburi ta gwanaye ta kasar Sin. A ganina, ingancinta bai kasa da na gasar kwallon teburi da aka yi a wasannin Olympic ko kadan ba.'

A shekarar 2005, yawan 'yan wasa 14 da suka zo daga kasashen waje sun shiga cikin hadaddiyar gasar kasar Sin, ciki har da Timo Boll na kasar Jamus da Michael Maze na kasar Danmark, da Ryu Seung Min da Oh Sang Eun da Joo Se Hyuk na kasar Korea ta kudu da Koji Matsushita da Fujinuma Ai da Konishi An na kasar Japan, dukkansu su yi suna sosai a duk duniya. Game da haka, Malam Zhang Xiaopeng ya ce haka,

'Muna kokari domin mayar da hadaddiyar gasar kwallon teburi ta kasar Sin da ta zama wata shahararriyar alama a duk duniya. Sabo da haka, bai kamata mu Sinawa kawai muka shiga ba. A shekarar 2005, yawan 'yan wasa da suka zo daga kasashen waje ya kai 14, wanda ya fi yawa a tarihi. Hadaddiyar gasar ta riga tana da wasu abubuwan musamman na NBA da hadaddiyar gasar kwallon kafa ta kasar Ingila, wadanda suke kasancewa shahararrun alamu a duk duniya.'

Shahararrun 'yan wasan kwallon teburi na kasashen waje sun shiga hadaddiyar gasar kasar Sin, wannan ba kawai ya bayar da moriyar tattalin arziki da ta al'umma ba, har ma ya bayar da tasiri mai kyau ga bunkasuwar wasan kwallon teburi a duk duniya.

Ko da yake haka ne, amma kwararru suna ganin cewa, idan ake son mayar da gasar kwallon teburi ta kasar Sin da ta zama wata shahararriyar alama ta gaskiya kamar NBA, to, ya kasance da doguwar hanya. Malam Zhang Xiaopeng ya bayyana cewa,

'Ko shakka babu, muna da 'yan wasa na gwanaye, amma ya kamata mu kara kyautata halin da kulob na hadaddiyar gasar suke ciki.'

A halin yanzu dai, ko wane kulob ba shi da tabbataccen filin wasa na kansa ba, sai kulob sun mayar da filayensu a birane daban daban, wandanda ba su yi girma ba. To, a cikin dogon lokaci, wannan zai zama mahani ga aikin horar da kasuwa mai karko ga gasar. Sabo da haka, muhimmin aiki a nan gaba shi ne kara habaka kasuwar kwallon teburi a manyan birane da tabbatar da filin wasa na kulob a wurin daya, wanda ba a canza shi a cikin gajeren lokaci ba. A sa'i daya kuma, a shekarar 2006, a karo na farko za a bayar da dokokin musanyar 'yan wasa a tsakanin kulob daban daban cikin 'yanci. Jami'an kwallon teburi na kasar Sin kamar Malam Zhang Xiaopeng sun yi imani cewa, bayan da aka yi gyare-gyare, hadaddiyar kasar kwallon teburi ta gwanaye ta kasar Sin za ta zama wata shahararriyar alama mai inganci a duk duniya.(Danladi)