Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-19 15:15:10    
Kasashen Sin da Afirka sun sami sakamako da yawa a fannin yin hadin gwiwar al'adu

cri
Kasashen Sin da Afirka sun kyautata yin mu'amalar al'adu a shekarun nan da suka wuce, sun sami sabbin ci gaba a fannoni daban daban, ta yadda sun kara raya sabuwar dangantakar abokanta bisa muhimman tsare-tsare da ke tsakaninsu.

Darektan cibiyar nazarin Afirka ta Jami'ar Beijing Mr. Lu Ting'en ya bayyana cewa, kasashen Sin da Afirka manyan mahaifata ne na duniya wajen al'adu, yin mu'amalar al'adu ba ma kawai ya kara wa jama'ar bangarorin nan 2 fahimtar juna da abokantaka a tsakaninsu ba, har ma ya ba da gudummowa wajen bunkasuwar al'adun duniya iri daban daban.

A cikin 'takardar manufofin kasar Sin domin kasashen Afirka' da gwamnatin kasar Sin ta bayar a kwanan baya, kasar Sin ta tabbatar da kafa da raya amincewar juna a fannin siyasa, da yin hadin gwiwa da neman samun bunkasuwa tare a fannin tattalin arziki, da kuma yin mu'amala da koyi da juna a fannin al'adu da su zama sabban manufofin da za a bi wajen karfafa yin hadin gwiwar abokantaka a tsakaninta da kasashen Afirka a nan gaba.

Sabuwar kasar Sin ta fara yin mu'amala da kasashen Afirka a fannin al'adu a shekarar 1955. Har zuwa karshen shekarar 2005, kasashen Sin da Afirka sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi 65 a tsakaninsu a fannin al'adu, sun kuma aiwatar da shirye-shiryen yin mu'amalar al'adu guda 151.

Kasashen Afirka fiye da 10 sun aika da kungiyoyin wakilan al'adu na gwamnatocinsu fiye da 20 zuwa kasar Sin daya bayan baya a cikin shekaru 5 da suka wuce, kasar Sin kuma ta sa hannu kan shirye-shiryen aiwatarwa guda 22 a fannin al'adu tare da kasashen Afirka 17.

A sakamakon kokarin da bangarorin nan 2 suka yi tare, kungiyoyin fasaha misalin guda 40 na kasashen Afirka sun kawo wa kasar Sin ziyara, inda suka nuna wasannin kide, wanda ya yi kusan daidai da yawan kungiyoyin fasaha da kasar Sin ta aika da su zuwa kasashen Afirka, shi ya sa an canja rashin daidaituwa tsakanin bangarorin nan 2 a fannin aika da kungiyoyin fasaha zuwa juna.

Kasaitattun bukukuwan al'adun da aka yi a wannan lokaci su ma sun jawo hankulan mutane sosai. Ban da wannan kuma, bangarorin kasashen Sin da Afirka sun yi hadin gwiwa mai amfani a fannin albarkatun kwadago na fasaha.

Wani jami'in ma'aikatar al'adu ta kasar Sin ya bayyana cewa, ci nasarar gudanar da harkokin yin mu'amalar al'adu tsakanin kasashen Sin da Afirka a jere ya sa kaimi kan kara yin cudanya tsakanin zukatan al'ummar kasashen Sin da Afirka da kuma inganta da raya abokantaka da hadin gwiwar da ke tsakaninsu.

A zarihi kuma, yin hadin gwiwar al'adu muhimmin abu ne da kasashen Sin da Afirka suka mayar da shi wajen yin hadin gwiwa a cikin sabon karni. A gun taron ministoci na karo na 2 na dandalin yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka da aka yi a watan Disamba na shekarar 2003, an zartas da 'shirin aikatawa na Addis Ababa', wanda ya gabatar da mataikai filla-filla a fannin yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka.

A cikin takardar manufofin kasar Sin domin kasashen Afirka da ta bayar, gwamnatin kasar Sin ta tsara shirye-shirye kan yin hadin gwiwar al'adu a tsakaninsu. An jaddada cewa, a aiwatar da yarjejeniyoyin da kasar Sin da kasashen Afirka suka sa hannu a kai da kuma shirye-shiryen da abin ya shafa, a rika yin mu'amala a tsakanin hukummomin al'adu na bangarorin nan 2, a kyautata yin mu'amala tsakanin ma'aikatan fasaha da al'adu da kuma motsa jiki na bangarorin nan 2.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar Sin Mr. Ma Heli ya yi bayanin cewa, kasashen Sin da Afirka suna da kama masu yawa a fannin al'adu, kuma suna girmama juna. Bangarorin nan 2 za su iya kyautata mu'amalar da ke tsakaninsu a fannin al'adu.(Tasallah)