Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-19 15:02:09    
An sami sauye-sauyen ayyukan shimfida zaman lafiya a kasar Kwadivwa

cri
Jama'a masu karatu, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Duniya ina Labari. A ran 17 ga wata, shugaba Pascal Affi N'Guessan na jam'iyyar 'yan gwagwarmaya ta kasar Kwadivwa wadda ke rike da ragamar mulkin kasar ya shelanta cewa, jam'iyyar ta tsai da kudurin janye jikinta daga ayyukan shimfida zaman lafiya a kasar Kwadivwa da ke karkashin jagorancin M.D.D. Manazarta sun bayyana cewa, wannan amsa ce mafi tsanani da jam'iyya mai rike da mulkin kasar Kwadivwa ta bayar bayan da rukunin aiki na M.D.D. da ke sa ido kan ayyukan shimfida zaman lafiya a kasar Kwadivwa ya bayar da shawarar cewa bai kamata a jinkirtar da wa'adin aikin majalisar dokokin jama'ar kasar ba a ran 15 ga wata. Kudurin da jam'iyyar da ke rike da mulkin kasar Kwadivwa ta yi ya sa ayyukan shimfida zaman lafiya a kasar Kwadivwa ya samu sauye-sauye sosai.

A wannan rana, Mr. N'Guessan ya bayyana cewa, domin yanzu kasashen duniya ba su da karfin raya ayyukan shimfida zaman lafiya a kasar Kwadivwa, jam'iyyar 'yan gwagwarmaya ta kasar Kwadivwa ta ki amincewa da shimfida zaman lafiya a kasar a karkashin jagorancin M.D.D. A sa'i daya, ya bai wa shugaba Laurent Gbagbo shawarar cewa ya kamata a nemi M.D.D. da rundunar tabbatar da zaman lafiya ta kasar Faransa da ke kasar da su janye jikinsu daga kasar. Sannan kuma, a janye jikin wakilan jam'iyyar 'yan gwagwarmaya ta kasar daga gwamnatin rikon kwarya. Haka nan kuma a sake kafa wata gwamnati wadda babu wakilan kungiyoyi masu makamai wadanda suke yin adawa da gwamnatin Laurent Gbagbo.

Domin ayyukan shimfida zaman lafiya a kasar Kwadivwa ya kan samun sauye-sauye, a watan Oktoba na shekarar bara, an zartas da wani kuduri a kwamitin sulhu na M.D.D., inda aka goyi bayan shawarar daidaita rikicin siyasa na kasar Kwadivwa da Tarayyar Afirka ta bayar, wato za a kara wa shugaba Laurent Gbagbo wa'adin aiki na shekara 1, sannan kuma a nada wani sabon firayin minista wanda kowane bangare zai amince da shi kuma ba zai halarci babban zaben da za a yi a nan gaba ba. Nauyin da aka dora wa wannan firayin minista shi ne raya ayyukan kwance damara na kungiyoyi daban-dabam. Bugu da kari kuma ya yi gyare-gyare kan harkokin zabe kuma da share fagen babban zaben da za a yi kafin watan Oktoba na shekarar da muke ciki.

Sannan kuma, kwamitin sulhu na M.D.D. ya tsai da kudurin kafuwar wani rukunin aiki na kasashen duniya. Tun daga watan Nuwamba na shekarar bara, wannan rukuni ya kira taro sau 1 a kowane wata a kasar Kwadivwa domin duba ayyukan shimfida zaman lafiya da ake yi a kasar. A ran 15 ga wata, rukunin ya bayar da wata sanarwa, inda ya bayyana cewa, yanzu babu dalilin halal da yake da shi na nuna goyon baya ga yunkurin tsawaita wa'adin aikin majalisar dokokin jama'ar kasar Kwadivwa. Sabo da haka, rukunin ya ba da shawara cewa, ya kamata a yi watsi da wannan majalisa. Amma a da kwamitin harkokin tsarin mulkin kasar da jam'iyyar da ke rike da ragamar mulkin kasar dukkansu sun taba bayyana cewa sun goyi bayan jinkirtar da wa'adin aikin majalisar har zuwa lokacin zaben sabuwar majalisar.

Bayan da aka bayar da sanarwar rukunin aiki na kasashen duniya, nan da nan mutane wadanda suke nuna goyon baya ga shugaba Laurent Gbagbo sai suka soma zanga-zanga a wasu wuraren kasar, inda suka yi wa rukunin aiki na kasashen duniya zargin cewa ya tsolma baki a cikin harkokin cikin gida na kasar Kwadivwa, kuma yana yunkurin korar gwamnatin yanzu ta hanyar halal daga mukaminta.

Manazarta suna ganin cewa, domin jam'iyyar 'yan gwagwarmaya ta kasar Kwadivwa jam'iyyar siyasa ce mafi girma a cikin majalisar dokokin kasar, idan an ruguje wannan majalisar, za a yi tasiri sosai ga matsayinta na rike da ragamar mulkin kasar kwata kwata. A kan aikin yin gyare-gyare kan dokar zabe da aikin share fagen babban zabe kafin watan Okbota na shekarar nan, jam'iyyar da ke rike da ragamar mulkin kasar yanzu ba za ta yi kome ba. Sabo da haka, babu sauran hanyar da za ta iya zaba, sai ta tsai da kudurin janye jikinta daga ayyukan shimfida zaman lafiya da ke karkashin jagorancin M.D.D. Dalilin da ya sa ta dauki wannan mataki shi ne tana son shugabancin halin siyasa da ake ciki da kanta, amma ba a karkashin jagorancin sauran kungiyoyi ba.

Bugu da kari kuma, Bayan kafuwar gwamnatin rikon kwarya da ke kunshe da bangarori daban-dabam a watan Disamba na shekarar bara, an rage ikon shugaba Laurent Gbabgo kwarai wanda ya zo daga jam'iyyar da ke rike da ragamar mulkin kasar. Idan an yi watsi da majalisar dokokin kasar yanzu, jam'iyyar 'yan gwagwarmaya ta kasar Kwadivwa ba za ta iya ba da jagoranci a zo a gani ba a aikin kafa dokoki, sakamakon haka, jam'iyyar ba za ta iya ci gaba da zauna kan matsayin jagorancin harkokin siyasa na kasar ba.

Amma a sa'i daya, mazanarta sun bayyana cewa, shawarar da rukunin aiki na kasashen duniya ya bayar wata shawara ce kawai, amma ba za ta iya sauya gwamnatin kasar Kwadivwa ba. Har yanzu bangarori daban-dabam suna da damar yin shawarwari game da maganar yadda za a ci gaba da shimfida zaman lafiya a kasar Kwadivwa. (Sanusi Chen)