A wannan mako, za mu amsa tambayar da Babangida mai shanu, wato mai sauraronmu daga jihar Taraba ta tarayyar Nijeriya ya aiko mana, inda ya ce, ina sha'awar fim na kasar Sin sosai, kuma na sami labari daga shafinku na internet cewa, bana shekara ce ta cikon shekaru 100 da aka fara yin fim a kasar Sin, ko za ku yi bayani a kan tarihin fim na kasar Sin. Ban da wannan, ina matukar sha'awar wani mashahurin tauraron fim na kasarku wanda ake kira Bruce Lee, ko za ku ba mu tarihinsa.
To, malam.Babangida mai shanu, a shekaru 100 da suka wuce, wani dan kasar Sin da ake kira Ren Qingtai ya fitar da fim na farko a tarihin kasar Sin. A cikin shekaru 100 daga baya, fina-finai na kasar Sin sun ganam ma idonsu da sauye-sauye a kasar Sin a zamani daban daban, haka kuma ta rike rekodi na game da ci gaban fasahohi da aka samu a wajen yin fim a nan kasar Sin.
A shekaru 100 da suka wuce, kasar Sin ta gano wata hanya mai halin kanta wajen bunkasa aikin yin fim nata. Ko a lokacin tashin hankali ko a zamanin lumana, ko kuma a lokacin da ake yin gyare-gyare a kasar Sin da bude kofa ga kasashen waje da kokarin raya zaman al'umma mai albarka a yau, kullum fina-finai na kasar Sin suna bayyana bukatun jama'a da halin zamani, sun taka rawa mai kyau a wajen karfafa gwiwar jama'a da farfado da al'ummar kasar Sin.
A halin yanzu dai, fina-finan kasar Sin suna bunkasa lami lafiya, kuma kasar Sin tana fuskantar muhimmin zarafi na bunkasa fina-finanta. Amma a sa'i daya kuma, ya kamata mu gane cewa, fina-finan kasar Sin suna fuskantar babban kalubale. In an kwatanta kasar Sin da kasashe masu ci gaba a wajen yin fim, har zuwa yanzu, kasar Sin ba ta sami karfi sosai ba a wannan fanni, shi ya sa kamata ya yi a kara kyautata manyan ayyuka da bunkasa kasuwanni da kuma fasahohi na yin fim da kuma kara kyautata ingancin fina-finan kasar Sin, ana kuma ci gaba da daukar babban nauyi a wajen yin gyare-gyaren aikin fim da bunkasa shi. Sabo da haka, ya kamata a kara kokarin samar da muhalli mai kyau a wajen bunkasa fina-finan kasar Sin lami lafiya.
Bruce Lee ya taba ba da babban taimako a wajen bunkasa wasannin fina-finai da wasan Kung Fu na zamani. Fina-finansa na wasan Kung fu sun shahara a duk duniya, sakamakon haka kuma, wasan Kung fu na kasar Sin shi ma ya yi suna, har ma an fara samun wata sabuwar kalma a kamus na harsuna da dama, wato Kung Fu.
An haifi Bruce Lee ne a birnin San Fransisco na kasar Amurka, kuma ya yi zama a Hongkong a lokacin yarantakarsa. Lokacin da yake yaro ne, ba shi da lafiya sosai, shi ya sa babbansa ya koya masa wasan damben gargajiya na kasar Sin wanda aka fi sani da suna Taiji a lokacin da shekarunsa suka kai 7, don neman inganta lafiyar jikinsa. Lokacin da ya kai shekaru 13 da haihuwa, sai ya bi wani mashahurin malami mai suna Ye Wen don koyon wasan damben gargajiya iri na Yongchun na kasar Sin daga wajensa. Don neman kyautata fasahar wasan dambensa, ban da wasan damben gargajiya na kasar Sin, ya kuma taba yin nazari a kan wasan dambe na kasashen yammacin duniya.
Lokacin da shekarunsa ya kai 18 da haihuwa, Bruce Lee ya bar Hongkong ya je Amurka don karatu. Bayan da ya shiga jami'a, ban da karatu, sai ya mai da hankalinsa duka a kan nazarin wasan Kung Fu. Ya kuma kafa wata kungiyar wasan Kungfu na kasar Sin a jami'ar, wasannin da kungiyar ta nuna sun sami yabo sosai daga wajen malamai da kuma dalibai.
Tun bayan da Bruce Lee ya sha gaban wasu 'yan iska guda hudu ba tare da yin amfani da ko wane makami ba, don neman kubutar da wata yarinyar kasar Sin, sai sunan nan na Bruce Lee ya fara shahara a duk fadin Amurka, gidajen telebijin sun gayyace shi da ya gwada fasahohin wasan Kung Fu, wasan Kung Fu na kasar Sin ya fara jawo hankulan mutanen duniya.
A farkon shekarun 1970, fina-finan wasan Kung Fu na kasar Sin sun fara ritsa da duk duniya gaba daya. A shekara ta 1971, wani kamfanin yin fim na Hongkong da ake kira Jiahe ya gayyaci Bruce Lee da ya taka rawa a cikin wani fim dangane da wasan Kung Fu na kasar Sin, wato sunansa shi ne 'The Big Boss', fim din nan ya sami karbuwa sosai daga wajen masu kallo. Bayan 'The Big Boss', Bruce Lee ya taka rawa a cikin 'Fist of Fury' da 'Return of the Dragon' da 'Game of Death'. Amma a daidai lokacin da Bruce Lee ke kokarin neman kara samun nasara a ayyukansa, a ran 20 ga watan Yuli na shekara ta 1973, Bruce Lee ya riga mu gidan gaskiya ba zato ba tsammani a Hongkong sakamakon wani maganin da jikinsa ya ki karba, ya mutu yana da shekaru 33 da haihuwa ne kawai.(Lubabatu Lei)
|