Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-18 21:37:10    
Sabuwar gwamnatin kasar Liberia ta bayan yaki tana da aiki mai nauyi kuma na dogon lokaci

cri

A ran 16 ga wata a birnin Monrovia, hedkwatar kasar Liberia, madam Ellen Johnson-Sirleaf, shugabar da jama'a suka zaba ta farko bayan yakin kasar ta yi rantsuwar hawa karagar mulki. Madam Johnson-Sirleaf wadda take da shekaru 67 da haihuwa ita ce shubaba mace ta farko da ta hau karagar mulki ta hanyar zaben jama'a a tarihin Afirka.

A gun bikin yin rantsuwar hawa kujerar shugaban kasa da aka yi a wannan rana, madam Johnson-Sirleaf ta bayyana cewa, sabuwar gwamnati da ke karkashin shugabancinta za ta dukufa kan aikin sa kaimi ga shimfida zaman lafiya da zama mai dorewa a kasar Liberia ta bayan yaki, da yin kokarin farfado da zaman rayuwa na bayan yakin, da maido da amincewar jama'a sannu a hankali. Wasu shugabannin kasashe da na gwamnatocin Afirka ciki har da Olusegun Obasanjo, shugaban kawancen Afirka, kuma shugaban kasar Nijeriya, da Li Zhaoxing, manzon musamman na shugaba Hu Jintao na kasar Sin, kuma ministan harkokin waje na kasar da Madam Condoleezza Rice, sakatariyar harkokin waje ta Amurka sun halarci bikin rantsuwar.

A watan Disamba na shekarar 1989 ne, aka barke da yakin basasa a kasar Liberia daga duk fannoni, wanda ya dade har shekaru 14, wanda kuma ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da dubu 200, tarin mutane fararen hula da ba su bi ba ba su sha ba sun rasa gidajensu, kuma tattalin arzikin kasar ya tabarbare.

Manazarta sun bayyana cewa, kafuwar sabuwar gwamnatin Liberia ta bayan yaki ta zama wani muhimmin taki ne wanda yake da ma'anar tarihi wajen yunkurin shinfida zaman lafiya a kasar. Amma a sa'i daya kuma sun bayyana cewa, ba shakka wannan yunkuri zai gamu da jarrabawa masu tsanani da yawa, wato sabuwar gwamnatin kasar Liberia tana da aiki mai nauyi kuma na dogon lokaci.

Da farko, Kiyaye zaman lafiya da zama mai dorewa na bayan yakin kasar Liberia zai zama wani muhimmin batun da ke gaban sabuwar gwamnatin kasar. Tun bayan gama yakin basasa na kasar, kuma bisa taimakon kungiyar musamman ta kiyaye zaman lafiya ta M.D.D. da ke Liberia ne, aka riga aka kwance wa mayakan rukunoni daban-daban da yawansu ya kai kusan dubu 100 damara.

Na 2, Game da yadda za a daidaita matsalar Charles Taylor, tsohon shugaban kasar Liberia wanda ke yin gudun hijira a kasashen waje, kungiyoyin siyasa daban-daban na kasar Liberia ciki har da madam Johnson-Sirleaf kullum suna yin bakinsu alaikum.

Na 3, Ko da yake gardama da aka yi cikin zaben shugaban kasar Liberia ta riga ta kwanta, amma har ila yau hargitsin da ake yi tsakanin rukunoni daban-daban domin neman moriyarsu ba za a iya kyale shi ba. Ana nan ana zuba ido kan yadda sabuwar gwamnatin da ke karkashin shugabancin madam Johnson-Sirleaf za ta kwantar da sabanin da ke tsakanin rukunoni daban-daban ta hanyar sake nada mambobin gwamnatin kasar.

Na 4, Sake raya kasar Liberia ta bayan yaki aiki ne mafi muhimmaci da ke gaban sabuwar gwamnatin kasar. Yakin basasa da aka yi cikin shekaru da yawa ya sa tattalin arziki na kasar ya lalace sosai, ayyukan samar da ruwan fanfo da wutar lantarki da zirga-zarga da sauran muhimman gine-gine sun gurgunce, yawan mutane marasa aikin yi ya kai fiye da kashi 85 bisa 100. Sa'an nan kuma har ila yau M.D.D. ba ta cire takunkumin cinikin lu'u-lu'u da tumba da ta yi wa Liberia ba tukuna. Ban da wannan kuma ana bukatar lokaci ga sabuwar gwamnatin Liberia kan yadda za ta kawar da yin rashawa da yin facaka kwata- kwata domin kago sharuda ga M.D.D. da ta cire takunkumin da take yi mata tun da wuri. (Umaru)