Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-18 09:43:29    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(12/01-17/01)

cri

A ran 11 ga wata, kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya bayar da sanarwar cewa, tun daga ran 11 ga watan Janairu zuwa ran 26 ga watan Maris, zai tattara shirin tsara samfur lambobin yabo na wasan Olympic na shekara ta 2008 ga duk duniya. An yarda da wani mutum shi kadai ko wani sashe masu tsara samfur lambobi da su shiga shirin nan. Haka kuma kwamitin shirya wasan Olympic na Beijing ya bayyana cewa, wannan shi ne karo na farko da aka tattara shirin tsara samfur lambobin yabo daga fararren hula a cikin tarihin wasannin Olympic.

A cikin kwanakin nan, kwamitin wasan Olympic na musamman na kasar Sin ya bayar da sanarwar cewa, za a yi wasan Olympic na musamman na kasar Sin na karo na hudu daga ran 29 ga watan Yuli zuwa ran 5 ga watan Agusta na shekara ta 2006 a birnin Ha'erbin da ke arewacin kasar Sin. Za a yi wasanni iri 10 kamar wasannin tsalle-tsalle da guje-guje da wasan iyo a cikin wannan wasan Olympic na musamman, kuma 'yan wasa fiye da 1900 da za su zo daga kungiyoyin wakilai 35 na duk kasar Sin za su shiga wasan. Wasan Olympic na musamman wani irin wasa ne ga nakasassu. Yanzu akwai nakasassu kusan miliyan 13 a cikin kasar Sin.

A ran 15 ga wata, an yi bikin rufe budaddiyar gasar badminton ta kasar Jamus a birnin Muelheim da ke yammacin kasar Jamus. Kungiyar kasar Sin ta samu dukkan lambobin zinariya da na azurfa a cikin gasa tsakanin namiji da namiji da ta tsakanin mace da mace da ta tsakanin mata biyu biyu da ta tsakanin gaurayawar namiji da mace. Wato Chen Jin ya lashe Chen Hong bisa maki biyu ba ko daya, shi ya sa ya zama zakara a cikin gasa tsakanin namiji da namiji, kuma Zhang Ning ta samu lambar zinariya sabo da ta lashe Lu Lan bisa maki biyu ba ko daya.

Daga ran 6 zuwa ran 13 ga wata, a birnin Prestatyn da ke kasar Birtaniya, an yi zagaye har uku na gasar share fage don zabar wadanda za su shiga gasar fid da gwani ta kwallon billiards ta Snooker ta duniya ta shekara ta 2006, inda dan wasan kasar Sin Ding Junhui wanda shekarunsa ya kai 18 da haihuwa ya lashe Stuart Mann da Brian Morgan da Drew Henry da sauran shahararrun 'yan wasan Birtaniya, shi ya sa ya samu iznin shiga zagaye na hudu na gasar share fage. Kuma za a yi zagaye na hudu na gasar share fage a tsakiyan watan Maris, Ding Junhui zai yi karawa da dan wasan Birtaniya Hawkins wanda ke matsayi na 10 a cikin jerin sunayen nagartattun 'yan wasa na duniya. Idan Ding Junhui ya lashe shi, to a karo na farko ne zai samu iznin shiga gasar zabar wadanda za su shiga gasar fid da gwani ta duniya da za a yi a cikin watan Afril.

A ran 14 ga wata, 'yan wasa mata na kasar Sin da 'yan wasa mata na kasar Amurka sun yi gasar motsa jiki tsakaninsu a birnin Guangzhou da ke kudancin kasar Sin, a karshe dai kungiyar kasar Sin ta ci kungiyar Amurka daya. Daga ran 18 zuwa ran 22 ga wata, za a yi gasar gayyata ta wasan kwallon kafa ta mata ta kasashe hudu a birnin Guangzhou. Kungiyoyin kasashen Faransa da Norway da Amurka da Sin za su shiga gasar.

A cikin karon karshe na gasar wasan kwallon kafa ta matasa da aka yi bisa gayyata a kasar Afirka ta Kudu a ran 15 ga wata, kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin da shekarun 'yan wasa ba su kai 19 ba ta lashe kungiyar kasar Afirka ta Kudu da shekarun 'yan wasa ba su kai 23 ba da ci 3 da 1, ta zama zakara. Kungiyoyi daga kasashe 8 sun shiga wannan gasa, kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyar kasashen Lesotho da Senegal da Mozambique. Dan wasan kasar Sin Mao Biao ya zama nagartaccen dan wasa cikin wannan gasa.(Kande Gao)