Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-17 18:16:08    
Yin hadin guiwa a fannin albarkatun halittu a tsakanin Sin da Afirka tana ciyar da kasashen Afirka gaba mai dorewa

cri
Jama'a masu karatu, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Duniya ina Labari. Kwanan baya, lokacin da masana suke ganawa da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin, sun bayyana cewa, loakcin da kasar Sin da kasashen Afirka suke yin hadin guiwa a fannin albarkatun halittu, kasar Sin tana mai da hankali sosai kan yadda kasashen Afirka za su yi amfani da albarkatun halittunsu domin yin takara a kasuwannin duniya kuma da raya su cikin hali mai dorewa.

A ran 12 ga wata a nan birnin Beijing, gwamnatin kasar Sin ta bayar da "Takardar Manufofin da take dauka don kasashen Afirka". Wannan ne karo na farko da gwamnatin kasar Sin ta bayar da irin wannan takarda, inda aka bayar da manyan tsare-tsaren da kasar Sin za ta dauka kan yadda za a yi hadin guiwa a fannonin harkokin siyasa da tattalin arziki da kimiyya da fasaha da zaman al'umma da zaman lafiya da na karko a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a nan gaba. Game da maganar yin hadin guiwa a fannin albarkatun halittu, wannan takarda ta bayyana cewa, "Gwamnatin kasar Sin ta sa kaimi da nuna goyon baya ga masana'antun kasar Sin wadanda suke da karfin yin takara da su yi hadin guiwa da kasashen Afirka a fannin raya albarkatun halittu ta hanyoyi iri iri bisa ka'idojin moriyar juna da neman bunkasuwa tare. A sakamakon haka, kasashen Afirka za su iya yin amfani da albarkatun halittunsu domin yin takara a kasuwannin duniya, kuma za su iya samun bunkasuwa mai dorewa."

Madam Wang Yingying, shehun malama da ke yin nazari kan maganar Afirka a jami'ar yin nazari kan harkokin duniya ta kasar Sin ta bayyana cewa, a mayar da matsayi mai rinjaye da kasashen Afirka suke kai wajen albarkatun halittu da ya zama matsayi mai rinjaye wajen yin takara a kasuwannin duniya, wannan zai zama burin da kasar Sin da kasashen Afirka suke nema domin ciyar da kasashen Afirka gaba kuma mai dorewa.

Madam Wang ta ce, ko da yake a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, tattalin arzikin kasashen Afirka ya samu ci gaba cikin sauri, amma har zuwa yanzu ba shi da karfi. Alal misali, kayayyakin da kasashen Afirka suka fitar kayayyaki ne da ba a sarrafa su ba. Sabo da haka, kasar Sin ta horar da mutane da yawa a kasashen Afirka da su zama masu mallakar fasahohi da masu tafiyar da masana'antu. Sannan kuma ta taimaki kasashen Afirka wajen kafa masana'antun sarrafa albarkatun halittu. Sakamakon haka, ba ma kawai za a iya kara darajar kayayyakin kasashen Afirka ba, har ma irin wadannan kayayyakin Afirka suna da karfin yin takara a kasuwannin duniya.

Madam Wang ta kara da cewa, "Hanyar da kasar Sin take bi tana da bambanci da ta kasashen yammancin duniya suke bi. Lokacin da kasar Sin take raya albarkatun halittu a Afirka, ta kan taimake su domin neman bunkasuwa. Kamar misali, bayan kasar Sin ta samu moriya a kasashen Afirka, ta kan zuba jari ta kafa wasu masana'antu ciki har da masana'antun samar da wutar lantarki a kasashen Afirka, inda jama'ar Afirka za su iya samun moriya.

Mr. An Yongyu, shugaban kungiyar kasar Sin da ke yin nazari kan harkokin Afirka yana ganin cewa, lokacin da kasar Sin da kasashen Afirka suke cinikin albarkatun halittun kasashen Afirka, a kullum ne kasasr Sin ta bayar da farashi mai kyau da ke dacewa da farashin kasuwannin duniya.

Mr. An ya kara da cewa, bin manufar neman bunkasuwa cikin hali mai dorewa, wannan ainihin ka'ida ce da kasar Sin take bi. Lokacin da take raya albarkatun halittu a kasashen Afirka, kasar Sin ta mai da hankali sosai wajen kiyaye albarkatun halittun kasashen Afirka. Alal misali, kamfanin kasar Sin yana raya masana'antun gandun daji a kasar Gabon, lokacin da yake sarin itatuwa, ya kan shuka sauran itatuwa domin kiyaye gandun daji na kasar Gabon.

Mr. An ya jaddada cewa, "lokacin da ake yin hadin guiwa a fannin albarkatun halittu a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, kasar Sin ta kan sa ido kan yadda za a ciyar da Afirka gaba cikin hali mai dorewa." (Sanusi Chen)