Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-17 16:09:27    
Al'adu masu iri dabam daban na al'ummomin birnin Beijing

cri

Tun bayan gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, bisa karuwar matsayin zaman rayuwa, mutane suna ta kara neman zaman al'adu. Yanzu a nan birnin Beijing, al'ummomi da yawa suna tafiyar da aikace-aikacen al'adu iri dabam daban, domin wadata zaman al'adu mazauna. Yanzu, ga bayanin da na shirya muku game da aikace-aikacen al'adu na al'ummomin mazauna na Beijing.

A ko wace rana da safe, tsofaffi kusan dari su kan taru a filin al'ummar Haite da ke yammacin Birnin Beijing, a wurin suna yin rawa tare da kade-kade, suna nuna kwararrunsu, kuma suna kece raini a cikin rawarsu. Wannan ita ce kungiyar rawa ta al'ummar Haite.



Madam Ye Daoxia ce ta kafa wannan kungiyar rawa, tana son rawa kafin ta yi ritaya, a shekarar 2000, madam Ye ta kira tsofaffin da ke cikin al'ummar domin kafa wannan kungiyar rawa, kuma ta koyar da sauran tsofaffi ba tare da biyan kudi ba. Bisa abubuwan musamma na tsofaffi, da kuma tare da inganta lafiya, madam Ye ta kafa tsarin rawa masu sauki, a ko wace rana da safe, akwai tsofaffi da yawa suna koyon rawa. Yanzu, yawan kungiyar rawa ya riga ya karu zuwa kusa da dari daga fiye da goma na da. Madam Ye ta ce, tsofaffin al'ummar suna son rawa sosai, "Kamar mu tsofaffi da shekarunmu ya kai fiye da 50, muna iya samun ciwo da sauki idan ba mu motsa jiki sosai ba, sabo da haka, muna rawa a nan yana da amfani sosai don lafiyarmu."

Ba kawai kungiyar rawa ta al'ummar Haite ta sa himma domin shiga wasannin kwaikwayon da al'ummar ta shirya ba, kuma kullum tana wakiltar al'ummar don hallartar wasannin kwaikwayo da gasa, kullum ana iya ganinta a cikin wasu manyan ayyukan da birnin Beijing ta shirya.

A al'ummar Xiluoyuan da ke kudancin birnin Beijing, kullum ana iya kallon wasan kwaikwayon da kungiyar rock mai suna "Jidudianzu" ta ke yi. Wannan kungiyar rock tana hade da samari 4 na al'ummar, dukansu suna da ayyuka, sun kafa wannan kungiya ne sabo da suna son kade-kaden rock. Wadannan samari suna mai da hankali sosai kan shiga ayyukan al'ummar. Jiawei, daya ne daga cikinsu ya ce, a lokacin da suka fara shiga aikace-aikacen al'umma, samari suna son wasanninsu sosai, amma tsofaffi ba su iya fahimtar wasanninsu ba, amma yanzu akwai tsofaffi da yawa suna son rock.

Bayan haka kuma, an kafa ajin koyon Turanci ga tsofaffi a al'ummar Xiluoyuan, dukan malaman ajin sun fito ne daga jami'an da ke kusa da al'ummar, su koyar da Turanci ba tare da biyan kudi ba, mazauna sun yi musu maraba sosai. Yanzu, yawan mutanen da ke hallaratr ajin koyon Turanci ya riga ya kai fiye da 600. Madam Xie Shuyan, shekarun haihuwarta ya kai 51, tun bayan da aka kafa ajin koyon Turanci a shekarar 2002, tana ta tsayawa kan koyon Turanci, yanzu, ta riga ta iya yin musanya da mutanen kasashen waje. Madam Xie ta ce, "Dalilin da ya sa na ke koyon Turanci shi ne, a lokacin wasannin Olimpic na shekarar 2008, muna iya ba da taimakonmu ga al'umma, muna iya sa 'yan wasan kasashen waje da su iya ji kamar a gidajensu a ko wane lokaci, kuma dukan jama'ar kasashen duniya za su san kasar Sin kasa ce mai abokantaka."



A al'ummar Qingqing da ke gabashin birnin Beijing, akwai gine-gine guda 27, da kuma mazauna kusan 2000. An kafa cibiyar aikace-aikace, da dakin karatun litattafai, da kuma filin al'adu a cikin al'ummar, sun bayar da wani dandamalin ayyukan al'adu ga mazaunan al'ummar.

A nan birnin Beijing, al'ummomi kamar irin wadannan suna da yawa, dukansu suna tafiyar da aikace-aikacen al'adu iri iri, domin wadata zaman al'adun mazauna. (Bilkisu)