Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-17 15:37:46    
An yi shawon shakatawa a kasar Swaziland da ke kudancin Afirka

cri

Idan ka je kasar Kenya, ya kamata ka ziyarci gidajen ajiye namun daji; idan ka je kasar Zimbabuwei, ya kamata ka zagaya tsofaffin gine-gine; amma idan ka je kasar Swaziland da ke kudancin Afirka, to, bai kamata ka kyale bikin tsaure ba. Bikin tsaure yana kasancewa bikin musamman na kasar Swaziland, wanda a kan shirya a karshen watan Agusta ko a mako na farko na watan Satumba, kuma wannan biki ya jawo hankulan 'yan yawon shakatawa sosai.

Bikin tsaure ya bayyana al'adu da gargajiya na kasar Swaziland dangane da mata. A kasar, an yi rufin daki ne da tsaure, mata kuma suna aikin tattara tsauren, sabo da haka tsaure ya zama tikiti da ke ba da 'yan mata damar shiga cikin bikin tsaure. A yayin da ake bikin, 'yan mata na duk fadin kasar su kan yi ado mai sauki, su taru a wurin da ke dab da fadar sarki, suna rera waka suna raye-raye domin nuna biyayya ga sarauniyarsu.

Swaziland wata karamar kasa ce da ke kudancin nahiyar Afirka, fadinta bai kai muraba'in kilomita dubu 20 ba, yawan mutanenta bai kai miliyan daya ba, kuma ana gudanar da tsarin mulki na sarauta, kashi 67 da ke cikin dari na mutanenta suna cikin talauci mai tsanani.

A gun bikin tsaure, 'yan mata dubbai suna rike da tsaure a hannunsu, suna rera waka suna raye-raye, suna murna sosai. Bisa labarin da muka samu, an ce, a kan shirya bikin tsaure ne domin nuna jikin 'yan mata mai kyau, wadanda ba su yi aure ba tunkuna.

Ana shafe kwanaki 8 ana bikin tsaure. A rana ta farko ta bikin, 'yan mata da suka zo daga wurare daban daban na kasar su kan taru a gidan sarauniyar sarakuna. Bayan haka, sai 'yan matan suna rera waka suna zuwa filayen tsaure daban daban bisa jagorancin masu rakiya. A cikin kwanaki da dama masu zuwa, a ko wace rana ko wace yarinya ta kan yanka tsaure 20 kuma ta kai su zuwa gidan sarauniyar sarakuna. Tabbas ne 'yan matan su fara wannan aiki daga yamma, sai a dare, za su isa gidan sarauniyar, domin nuna cewa wai suna tafiya a kan doguwar hanya.

Ya zuwa rana ta shida, 'yan matan su fara biki na gaskiya. Su tattara tsaure da suka yanka a gaban fadar sarauniyar sarakuna, bayan haka, su fara raye-raye kamar bakaken furanni a cikin fuska.

Rana ta 7 ta fi muhimmanci domin sarkin kasar Swaziland kan je bikin. Sarkin ya kan zabi mata daya daga cikin 'yan matan. Idan wata yarinya ta yi sa'a, to, za ta iya samun zaman jin dadi, za ta iya kece raini. Sabo da haka, a ran nan, 'yan mata sun fi kokari wajen raye-raye.

A rana ta karshe ta bikin, sarkin kasar kan umurci wani da ya yanka shanu da yawansu ya kai 25, sai 'yan matan su ci su more, bayan haka, sai su koma gidajensu, wannan ya kawo karshen bikin tsaure na ko wace shekara ke nan. A hakika dai, a halin yanzu, bikin tsaure ya sha bamban sosai da na zamanin da, mutane da yawa na kasar Swaziland sun fara canza zamansu na gargajiya a sakamakon tasiri da kasashen yamma suka ba su. Amma 'yan mata da yawa suna kaunar bikin tsaure a halin yanzu. A idonsu, a gun bikin, ba suna bayyana kyaun ganinsu kawai ba, har ma suna bayyana al'adun musamman na kasar Swaziland.(Danladi)